Girmama Kaburbura Masu Tsarki



 Dangane da shari’un da suka zo daga sama muna iya daukar shari’ar Annabi Isa (a.s) a matsayin misali. A akidar musulmi Annabi Isa matsayin annabin Allah yake, wanda yake mai albishiri ne ga zuwan Manzo Muhammad (s.a.w) sannan ya zo da littafi mai suna “Injil” wanda yake dauke da haske a cikinsa. Amma muna samun tabbas a hakan ne ta hanyar Kur’ani mai girma.

 Amma sakamakon matashin da yake yammacin duniya ba shi da imani da Kur’ani ta yadda zai kalli Annabi Isa ta wannan fuskar, a yau dangane da zuwan Annabi Isa da littafinsa yana da shakku a kansu. Domin kuwa ba shi da wata alama ta wannan kira a hannunsa ta yadda zata taimaka masa ya samu yakini a kan hakan. Domin kuwa Masih ba shi da kabari ko mahaifiyarsa da sahabbansa da zasu tabbatar da zuwansa. Sannan littafinsa an hakaito shi ta hanyoyi daban-daban ta yadda zai yi wahala mutum ya gane gaskiyar al’amarin.

 A takaice babu wani abu wanda zai tabbatar wa matshin yammacin duniya gaskiyar zuwan Annabi Isa da littafinsa. Saboda haka sabanin magabatansa yana shakku a kan hakikanin wannan al’amari.

 Saboda haka mu musulmi dole mu dauki darasi daga wannan abin da yake faruwa daga kiristanci, ta yadda zamu kiyaye duk wani abu wanda yake ya zo daga Manzo kuma yana matsayin sheda ne ga da’awar da shi Manzo ya zo da ita, (duk yadda ya kasance abu dan karami ne) ta yadda zamu kare duk wani abu wanda zai sanya wadanda zasu zo bayammu su yi shakku a kan gaskiyar addinin musulunci, kamar yadda matashin yammacin duniya yake shakkun gaskiyar Annabi Isa da Injila.

 Muna iya amfana daga ayoyin Kur’ani da suke nuni da cewa: Al’ummun da suka gabata sun kasance suna kiyaye duk wani abin da manzonsu ya zo da shi, ta yadda suke tafiya da shi yayin wani kwami mai zafi da yake a gabansu. ta yadda ta hanyar neman albarkaci da wannan abin daga annabawansu don neman samu cin nasara daga mushrikai abokan gabarsu.

 A matsayin misali Bani Isra’il sun kasance suna tsaron wani akwati wanda duk abin da musa da iyalansa suka bari yana cikinsa, sannan suna neman tabarruki daga gare shi kuma yayin karo da makiya suna daukar shi domin neman cin nasara.[2]

 Kasantuwar albarkar da muhimmancin wannan akwati ya zamana mala’iku suke daukarsa. Idan har ya kasance kiyaye wasu abubuwa na magabata (kamar wannan akwatin) wani abu ne marar kyau, to me ya sa Kur’ani mai girma yake ambaton wannan al’amari da harshe na yabo, kuma me ya sa mala’iku suke daukarsa, sannan me ya sa bayan dauke wannan akwati daga “Amalika” a cikin wannan aya ya zama wata alama ce da take nuna wanda zai jagoranci wannan runduna ta yaki?!

 Yara wadanda ba su balaga ba su ne, suke wasa da kayan da iyayensu suka bar musu, ta yadda cikin sauki suna iya batar da su. Amma magadan da suke da hankali kuma sukan amfani da matsayin wannan abin da iyayensu suka bar musu, suna rike wadan kaya ne iya karfinsu. Al’ummar muslmi ma sakamakon cigaban da suka samu bayan wafatin Manzo (s.a.w) su kiyaye duk wani abu da ya bari, wannan kuwa har da kwarar gashinsa sun kasance sun sanya ta wani wuri na musamman suka ajiye ta.

Matsayin Gidajen Annabawa A Cikin Kur’ani

 Gidajen annabawa da manyan bayin Allah suna da wani matsayi na musamman, wannan kuwa a fili yake matsayin da suke da shi bai shafi wani abu na duniya ba ne, domin idan da haka ne, gidajensu ba su da wani bambanci da sauran gidajen mutane domin an gina su ne da yumbu da tubali kamar na kowa, wadannan gidaje suna da wannan matsayi ne sakamakon mutane masu matsayi da suka zauna a cikinsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next