Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2



 Tare da kula da ma’anar kalmar “Sawwaitahu” kamar yadda zamu yi bayanin a kanta zamu fahimci cewa wannan kalma ta Sharaf a cikin wannan hadisi tana nufin ma’ana ne ta musamman.

 Dangane da kalma ta biyu kuwa muna iya bayani kamar haka: Kalma ta Sawwaitahu da ta zo da ma’anar aiki wato baje wani abu ko dai-daita shi, ana mafani da ita a cikin harshen larabci da ma’anoni guda biyu.

1-Daidaita wani abu da wani abu daban ta hanyar tsawo ko girma ko makamancin haka, saboda haka idan da wannan ma’ana kalmar sawwa ta zo tana da aikau guda biyu (maf’ul) wanda a cikin harshen larabci wannan maf’ul na biyu yana bukatar harafin jarra wanda zai dai-daita wannan abin da waninsa.[15]

2-Ma’ana ta biyu kuwa shi ne baje wani abu ta yadda zai daidaita babu tudu da kwari, saboda haka a nan wannan fi’ili na sawwa yana bukatar maf’uli guda daya, ba shi bukatar na biyu. Saboda haka duk lokacin kafinta ya daidaita wani katako, kawai zai ce na goge katako, (wato sawwaitul kashab). [16]

 Saboda haka bambanci wannan ma’anoni guda biyu a bayyane yake, wato a ma’ana ta farko siffa ce ta abubuwa guda biyu, amma a ma’ana ta biyu kuwa siffa ce ta abu guda (wato daidaita wani abu ba tare da an hada shi da waninsa ba kamar yadda muka gani).

 Saboda haka yanzu mun fahimci ma’anonin wadannan kalmomi guda biyu wato “Sawwaitahu da musharrafan”. Don haka muna iya fahimtar cewa wannan hadisi yana magana ne dangane da yadda wannan kabari yake domin kuwa yana magana ne a kan abu guda, ba wai kabari ba da kasa (wato ba a dai-daita shi da kasa ba wato a dai-daita shi kansa kabarin) Domin da haka ake nufi sai a ce “sawwaitahu bil ard”. Saboda haka abin da Imam yake nufi a cikin wannan hadisi shi ne, duk inda ya ga wani kabari yana da tudu da kwari kamar tozon rakumi ya dai-daita shi ya gyara shi ya zama kamar dakali. Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana yadda za a yi kabarin musulmi ta yadda za a baje samansa ba a yi masa tulluwa ba kamar bayan rakumi ko kifi.

 Domin kuwa wannan zamani a kan yi kaburra ne da tudu kamar yadda bayan rakumi yake, don haka ne Imam ya ba Abu hayyaj umarni da ya daidaita duk kabarin da ya gani a haka. Saboda haka wannan hadisi wace alaka yake da shi wajen rusa shi kansa kabari ko ginin da aka a samansa?!

 Kuma cikin su maruwaitan wannan hadisi da masu sharhinsa sun bayyana ma’anar wannan hadisi kamar yadda muka yi bayani a sama.

 1-Muslim ya ruwaito wannan hadisi karkashin babin “Amr bi taswiyatul Kubur” wato ruwayoyin da suke magana a kan daidaita saman kabari, saboda haka muna iya cewa shi ma Muslim abin da ya fahimta da ma’anar wannan hadisi kenan (wato kasantuwar kaburbura kamar yadda dakali yake ba kamar yadda bayan rakumi yake ba).

 2-Muslim a farkon wannan babi ya ruwaito cewa: Fudhala tare da wasu mutane sun kasance a Rom, Sai wani daga cikin mutanensa ya rasu sai ya rufe shi ya yi kabarinsa kamar yadda ake dakali (Rectangle) sai ya ce haka na ji daga Manzo (s.a.w) ya ce: Ku yi kaburbura kamar haka wato samansu a baje ba tare da tudu ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next