Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2



 Ibn jubair[2] (540-614) shahararren mai yawo bude ido ya ziyarci kaburburan annabawa da bayin Allah a kasashen Misra, Makka, Madina, Iraki da Sham, yayin tafiye-tafiyensa kuma ya yi bayani a kan kowane daya daga cikinsu a cikin littafinsa na tafiye-tafiye, ta yadda dukkammu zamu iya samun wannan a cikin wannan littafin nasa. Ta hanyar karanta wannan littafin musulmi suna samun masaniya a kan tarihin gina hasumiyoyi da gine-ginen kaburburan annabawa da waliyyan Allah. Dangane da abin da ya zo a cikin wannan littafin tafiye-tafiye nasa shi ne: Tarihin gina manya-manyan gine-gine a kan kaburburan Imamai da waliyyai da shahidai a tafarkin Allah, wanda yake komawa zuwa ga zamanin sahabbai da tabi’ai. Wanda yake nuna yadda a wancan zamanin da musulmai suke nuna kauna da kulawarsu dangane da shugabanni da manyan addini. Ta yadda suka tashi domin gina wurare masu kawatarwa domin girmamawa gare su. Sannanbabu wani daga cikin sahabbai wanda ya nuna cewa wannan aiki yana komawa ne zuwa ga shirka ko kuma ya saba wa tauhidi da kadaita Ubangiji.

 Kamar yadda Ibn Jubair ya fara tafiyarsa daga gaban duniyar musulunci (Andulus) zuwa yammacinta ta yadda kasar Misra ta kasance wuri mafi kusa gare shi, Sai ya fara da wuraren tarihin da suke a Misra musamman Alkahira. Zamu kawo wasu daga cikin abin da ya rubuta daga cikin wadannan gine-gine na musulunci a wannan kasa:

 

Gini Mai Girma Na Kan Imam Husain A.S A Alkahira

 Wasu sun tafi a kan cewa an rufe kan Imam Husain (a.s) a garin Alkahira, saboda haka suka gina wani wuri da sunan “Ra’asul Husain” inda mutane suke zuwa ziyara daga cikin gida da waje. Masu sabon aure a wannan gari sukan je Masallacin Husain (a.s) wanda yake a wannan wuri sukan yi dawafi[3].

 Ibn Jubair yana cewa: Daya daga cikin wurare masu tsarki a Alkahira shi ne Wurin da aka rufe kan Husain, an kawata wannan wuri da azurfa, wannan gini yana da girma da daukaka ta yadda harshe ba zai iya siffanta shi ba. A kan wannan gini akwai wani dutse na alfarma kai kace madubin Indiya ne, ta yadda yake haske yana dauko hutunan abubuwan da suke a gabansa.

Ya ce: Da idanuna na ga masu ziyarar Husaini (a.s) yadda suke kuka suna sumbatar yadin da aka dora a kan abin da aka rufe kabarinsa da shi suna neman tabarraki suna addu’a, ta yadda kwallarsu kamar ta rufe wannan kabari.

 Ibn Jubair ya ambaci wani wuri da ake kira “Karafa” inda yake cewa yana daga cikin wurare masu ban al’ajabi kamar yadda ya bayyana akwai kaburburan annabawa da iyalan Manzo da sahabbansa da tabi’ai da sauran kaburburan manyan malamai da aka rufe a wannan wuri.

 Dan Annabi Salih (Raubil) dan Annabi Yakub (Ishak) da matar Fir’auna dukkansu an rufe su ne a wannan wuri. Haka nan daga cikin iyalan Manzo akwai dan Imam Ja’afar mai suna kasim da dansa Abdullah Bn Kasim da dansa Yahya Bn Kasim, sannan da kabarin Ali Bn Kasim Bn Abdullah Bn Kasim da dan’uwansa Isa Bn Abdullah.

 Ibn Jubair ya ambaci da yawa daga cikin ‘ya’yan Ali (a.s) wadanda aka rufe su a can. Haka nan akwai kaburburan Sahabbai tabi’ai ba shuganni kamar Imam Shafi’i ta yadda yake magana a kan girma da matsayin haraminsa, kamar yadda yake cewa Salahuddin Al’ayubi shi yake biyan kudin da ake bukata domin gabatar da bukuwa a wannan harami na Imam Shafi’i.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next