Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2



 Abin mamaki a nan shi ne a mahangar ilimin Usul fikh haduwar mutane a kan hukuncin wani abu har zuwa karnoni da dama yana nuna ingancin wannan abin ne. Amma muslmi sun hadu a kan ingancin gine-gine a kan kabarin annabawa da waliyyan Allah tsawon karnoni masu yawa, amma mahangar wasu wannan bai isa ya zama dalili ba, ta yadda kowane lokaci suna kokarin kaucewa a kan yarda da wannan al’amari.

 

Gine-Ginen Tunawa Da Bayin Allah Da Dalilai Masu Sabani A Kan Haka

 Mun yi bincike a kan dalilan da suke nuni da ingancin ziyar da girmama kaburburan bayin Allah daga Kur’ani da Sunna da tarihin magabata, amma yanzu lokaci ya yi da zamu yi bincike a kan dalilan masu inkarin hakan. Wanda sukan yi riko da hadisin Abil Hayyaj Asadi ne a kan hakan, yanzu zamu auna wannan hadisi ta yadda zamu ga kimarsa ta hanyar ma’aunin da ake gane ingancin hadisi.

 Muslim a cikin sahih dinsa yana ruwaitowa daga Abil Hayyaj kamar haka: “Ali bin Abi Dalib ya ce da ni: Ba na aike ba akan abin da Manzo ya aika ni a kansa ba, kada kabar wani hoto sai ka lalata shi, ko wani kabari mai tudu sai ka daidaita (baje) shi”.

 Masu adawa da wannan al’amari suna kafa dalili ne da wannan hadisin a kan haramcin gina haramin wani Imami daga cikin Imamai (a.s) sakamakon haka ne a shekara ta 1344Bh suka rusa makabartar “Bakiyya” a wannan rana ne kuma a cikin jaridar “Ummul kura” aka sanya tambaya da amsa dangane da dalilan da suka sanya aka rusa wannan makabarta, domin mu gane ta yadda a ka kafa hujja da wannan hadisi yana da kyau mu yi bincike a kan ma’ana da kuma dangane wannan hadisi:

 

A-Sanadin Wannan Hadisi

Maruwaitan wannan hadisi su ne kamar haka: 1-Waki 2-Sufyanus sauri 3-Habib Bn Abi sabit 4-Abu wa’il 5-Abu hayyaj Asadi.

 Dangane da maruwaici na farko kuwa abin da Ahmad Bn Hambal wanda malaman hadisi ne yana cewa dangane da shi ya wadatar da mu inda yake cewa: Waki ya yi kuskure a cikin hadisai guda 500[7]. Sannan ya cigaba da cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi da ma’ana (ba tare da kiyaye lafuzzan da aka yi amfani da su ba) Sannan ba shi da cikakkiyar masaniya a harshen larabci. [8]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next