Dalilin Shi'ancin Farisawa



Na biyu: Ba makawa a tambayi wadannan masu wannan magana da cewa shin kuna nufin ganin bayan musulunci da rusa shi ya kebanci Farisawa ne kawai da suka zabi musulunci suka kuma zabi sunnanci ko kuma ya shafi dukkan Farisawa wadanda ya hada da Sunna da Shi’ansu. Kuma dole ne amsa ta kasance da E ne. Domin idan son ganin bayan addinin ya kasance saboda kasancewarsu Farisawa ne ba don komai ba, to idan haka ne don me muka ga ana sukan wadanda suke Shi'a ne kawai banda wadanda suka zama Sunna.

Tayiwu wani ya ce: Wannan ya kasance ne ga Farisawa Shi'a, don haka wannan yana shafar akidar Shi'a ne. To mun riga mun kawo cewa madogarar Shi'a ita ce Littafi da Sunna, don haka babu wata hanyar da za a rika sukan su da abin da yake kore littafin da sunnar, wannan kuwa ga mai binciken gaskiya ke nan -alhalin ya fi kowa nesa da ita- ba don irin wadannan mutane suna neman nesantar da al’umma daga alheri ba, da ba su kawo irin wannan tunani ba, da suka rarraba al’umma suka daidaita hadin kanta, kuma da sun ji kunyar irin wadannan maganganu nasu, kuma da sannu zamu kawo maka cewa gwarazan mutane a tarihi da fikihu da akida su ne Farisawa kansu, kuma ba ma ganin wannan wani aibi ne matukar muna riko da masdari daya kuma matukar kur’aninmu dare da rana yana shelanta hadin kai da cewa asalinmu daya ne a fadinsa "Shin ba mu halicce ku ba daga ruwa abin wulakantawa" mursalat: 20.

Na uku: Mas’alolin da mutanen nan suka kawo kuma suke ganin su a matsayin al’amuran da suke rusa addini kuma suke jifan Farisawa Shi'a da su kamar wasiyya da Raja'a da kuma maganar mahadiyyanci duk wannan ma su ma Ahlus Sunna sun yi tarayya da su a ciki amma ba mu samu wani yana sukan su ba da ita ko kuma yana ganin shi abin zagi ne, kamar yadda wannan al’amura ne da suka zo a ruwayoyin Sunna ta hanya amintacciya da zamu kawo wannan nan kusa in Allah ya so.

Wannan ke nan, hada da cewa wadannan ra’ayoyin ba laruri ba ne a musulunci gun Shi'a koda kuwa sun kasance laruri ne na mazhaba (kamar imani da Imam Mahadi (a.s) amma duk da haka me ya zo da wannan duk kace-nace din da ake kagowa, kuma me ya kawo duk wannan karfi da ake kararwa domin kawo baraka tsakanin ma’abota alkibla daya balle ma a yi maganar kyawunsa? Ko me ya kawo duk wannan hamasa da ake kagowa a kan abubuwan da ba su kebanta da Shi'a ba wadanda abubuwa ne da su ma Ahlus Sunna suna da su?.

Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id


[1] Azzandika wasshu’ubiyya, shafi: 56.

[2] Tarihul mazahibil islamiyya, j 1, shafi: 40.



back 1 2 3 4 5 6 next