Dalilin Shi'ancin Farisawa



Muhammad Abu Zuhra yana cewa: Kuma wasu daga sashen malamai daga cikinsu akwai Duzi mustashriki ya tabbatar da cewa asalin mazhabar Shi’anci wani tunani ne daga Farisanci yayin da Larabawa suna da tunanin zabe ne, Farisawa kuma suna da tunanin mulki ne da gado, ba su san wani abu da ma’anar gado ba, har ya ce; Shi'a sun tasirantu da tunanin Farisanci game da mulki da gado[2].

 Haka nan Ahmad Amin da wasu mustashrikai suka tafi a kan haka, kuma shi ma ya ambace su cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra’ayi, kuma wannan ma’anar ta zo a littafinsa na Fajarul Islam yana mai karfafa ra’ayinsa da ra’ayoyin mustashrikai[3].

3- Al’amari Na Uku:

Wasu masu kin shi'ancin suna cewa: Shigar Farisawa Shi'anci ya kasance da nufin rusa muslunci ne da boyewa karkashin son Ahlul-baiti (a.s), sannan sai aka shigo da wadannan ra’ayoyin masu rusa musulunci kamar fadin batun Wasiyya, Raja'a, da Mahadi (a.s) da sauransu.

A kan haka ne Ahmad Amin yake cewa: A bisa gaskiya Shi’anci ya kasance mafaka ce da dukkan wanda yake son rusa musulunci yake fakewa da shi don gaba ko mugun kulli, haka nan dukkan wanda yake son shigar da koyarwar iyayensa na yahudanci da kiristanci da zardashtanci da indiyanci, da dukkan wanda yake son â€کyancin kasarsa da fita daga masarautarsa sun labe karkashin son Ahlu-baitii[4] ne.

Ina fatan mu duba irin wadannan maganganu da muryoyi na kiyayya a kan Shi’anci kuma wannan magana ce da masu yawa tun kafinsa da bayansa suka kawo kamar mai littafin Manar[5]. Kuma mun samu wannan tunani da yake ganin Shi’anci a matsayin wani tasiri na Farisanci a fili gun wasu mutanen masu gaba da kiyayya da tafarkin mazhabin Ahlul-baiti kamar Muhibbuddin Al’khadib, da Ahmad Shalbi, da Musdafa Ash’ka’a da sauransu.

Saoba kuma mu dan yi karin haske a kan inganci ko rashin ingancin wannan da’awar da take tabbatar da abin da aka fada Shi’anci dole mu kawo wasu abubuwan da suka kawo a matsayin dalilai da ya sanya Farisawa shiga Shi’anci:

1-           Raddi kan abubuwa uku

2-           Iyakance hakikanin Shi’anci a bisa kabilanci

3-           Iyakance hakikanin Shi’anci a tunani



back 1 2 3 4 5 6 next