Dalilin Shi'ancin Farisawa



Kuma duk wani mai bincike ya san cewa kowace al’umma tana da wani abu da ta hadu da wata al’ummar a kansa a wani ra’ayi ko wata mas’ala amma duk da haka wannan ba ya sanya a ce musu abu guda. Mu fara da Ahmad Amin kansa mu dora masa ra’ayinsa a kansa zamu ga dalilin da ya dora wa Shi'a shi ma yana hawa kansa; idan mun duba zamu ga yana tafiya a kan ra’ayin Jabar (tilasci) da Zabi:

Mas’alar Jabar da Zabi malaman Falsafa na Yunan sun yi magana kanta kafin musulmi su yi magana game da ita, kuma Saryaniyawa sun samu wannan daga garesu ne, kuma Zardashtiyyun su ma sun yi magana kanta kamar yadda Kiristoci suka yi, sannan sai Musulmi[8].

Don haka bisa dogaro da maganar Ahmad Amin muna iya cewa ke nan musulmi sun zamo Nasara saboda sun yi ittifaki da Nasara a kan wannan ra’ayi na Jabar, idan kuwa ba haka ba, mene ne dalilin Ahmad Amin na ganin Shi'a cewa Farisawa ne saboda kawai sun hadu da su kan maganar Hakkin Allah madaukaki?.

Amma abu na biyu na da’awar cewa dukkan kowanne daga Farisawa da kuma Shi'a suna ganin jagoranci a matsayin gado ne to wannan batacce ne game da Shi'a, domin Shi'a ba sa ganin jagoranci gado ne, suna ganin al’amari ne na nassi daga Allah (s.w.t) ta hannun Annabi (s.a.w) ko Imami (a.s), kuma littattafan Shi'a cike suke da wannan al’amari[9].

Kuma mas’alar nassin kan Imami (a.s) ba wata masl’ala ba ce da take ta jinkirta gunsu domin ita sananniya ce garesu tun farko gun dabaka ta farko ta Shi'a saboda bayyanar nassi gunsu kan mas’alar Imamanci. Kuma muna iya kawo misali kan haka na wata ganawa da ta faru tsakanin halifa na biyu da Abdullahi dan Abbas, kuma halifa na biyu ya kasance yana samun nutsuwa da Ibn Abbas kuma yana karkata zuwa gareshi sosai, sai wata rana ya ce da shi: Ya kai Abdullahi nauyi yana kanka idan ka boye mini wani abu, shin a cikin ran Ali (a.s) akwai wani abu na kaunar halifanci? Sai Ibn Abbas ya ce; sai na ce; haka ne. Sai ya ce; shin yana raya cewa manzon Allah ya yi masa nassi ne? Ibn Abbas ya ce; sai na ce; na’am. Sai Umar ya ce: Hakika manzon Allah ya kasance yana kambama al’amarinsa kwarai da gaske da maganar da babu wata hujja da ta bari kuma babu wani uzuri da ba ta yanke ba, kuma ya kasance yana daukaka sha’aninsa wani lokacin, kuma lallai ya so ya shelanta sunansa a rashin lafiyarsa sai na hana shi saboda tausayawa da kuma kiyaye al’amarin musulunci. Sai Manzo (s.a.w) ya san na gane abin da yake cikin ransa sai ya kyale[10]. Hanin nan da halifa Umar ya yi nuni da shi ne yayin da Annabi (s.a.w) ya nema daga sahabbansa su zo masa da takarda da tawwada a cikin lokacin rayuwarsa na karshe yana mai cewa: A ba ni tawwada da takarda in rubuta muku abin da ba zaku taba bata ba bayana har abada. Sai halifa Umar ya ce: Yana cikin sumbatu ne kuma ciwo ya yi galaba kansa[11].

A dunkule dai wannan muhawara da ire-irenta tana yi mana bayanin matsayin Shi'a kan al’amarin Imamanci, kuma ita nassi ce ba gado ba, don haka a ina ne mustashrikai da dalibansu suka samu wannan magana ta gado idan dai ba rashin sanin mene ne Shi’anci ba ko kuma son neman karkatar da gaskiya da son rai.

 

3- Al’amari na uku:

Shi ne shigar Farisawa musulunci domin son su rusa shi sannan kuma su tabbatar da hadafinsu da shigar da ra’ayin kakanninsu; wannan ra’ayi dai batacce ne, kuma muna iya cewa kamar haka:

Na farko: Littattafansu masu kariya ga musulunci da masallatansu da kuma cibiyoyinsu na addini da jihadinsu a tafarkin Allah duk wannan yana nuna mana karyar wannan da’awar da ake yi.



back 1 2 3 4 5 6 next