Dalilin Shi'ancin Farisawa



4-            Iyakance hakikanin sunnanci daga wannan al’amarin da dalilai da aka kawo daga littafin Sunna;

Amsa A Kan Dalilan Shigar Farisanci Shi’anci

1- Al’mari Na Farko:

Surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa;

Yana daga cikin abubuwan da kowa ya yarda da su shi ne: Ka’idar nan ta cewa hukuncin abubuwan da suke iri daya kan abin da halatta da abin da bai halatta ba iri daya ne, don haka wannan ka'ida ta hau kan wadannan marubuta game da abin da suka kawo na shi’antar Farisawa saboda surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa. Domin akwai wannan ga Abdullahi dan Umar dan Khaddabi, da kuma Muhammad dan Abubakar. Kuma Zamakhshari ya kawo wannan a cikin littafin Rabi’ul Abrar da waninsa na malaman tarihi cewa yayin da sahabbai suka zo da â€کya’ya uku na Yazdajir daga ribatattun Farisawa a lokacin halifa na biyu sai aka sayar da ribatattun kuma halifa ya umarci da a sayar da su. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: Ba haka ake yi wa â€کya’yan sarakuna ba, su ba a yi musu kamar sauran mutanen. Sai Halifa ya ce masa yaya za a yi ke nan da su, sai ya ce: A yi musu kima, kuma duk yadda kudinsu ya kai sai wanda ya zabe su ya biya, sai aka yi musu kima, sai Ali (a.s) ya dauki daya ya ba wa Abdullah dan Umar, daya kuwa dansa Husain, daya kuma Muhammad dan Abubakar, sai aka haifa wa Abdullahi dan Umar dansa Salim, shi kuma Husain ya haifi Zainul-abidin, Muhammad kuma ya samu dansa Kasim, wadannan uwayensu mata â€کya’yan sarki Yazdajir ne[6].

A nan ne muke tambaya cewa: Idan dai surukuta ita ce dalili to don me ba zamu ga Farisawa sun karkata ga surukansu na Abdullahi dan Umar da Muhammad dan Abubakar ba!? Kuma kowanne daga cikinsu shi Muhammad da Abdullahi â€کya’yan halifofi ne, kamar yadda Husain yake dan halifa ne. Hada da cewa dukkansu kowanne Yazid dan Walid dan Abdulmalik, da babarsa Shafarand â€کyar Fairuz dan Yazdajir, da Marwan dan Muhammad karshen halifofin Banu Umayya wanda babarsa ita baiwa ce daga Kurdawan Iran, don me ba ma ganin irin wannan dalili a kan al’amarinsu[7], kuma a bisa akasin haka don me ya sa Larabawa su ba sa karkata ga Ahlu-baiti (a.s) ai iyayensu Larabawa ne, yayin da muke ganin wasu jama’a daga Larabawa sun zamanto makiya ga Ahlu-baiti (a.s); wannan tambaya ce ga wadannan hankulan da suke rubutu amma ba sa tunani.

2- Al’amari Na Biyu:

Kusancin Ra’ayi Tsakanin Shi'a da Farisawa:

Kowanne daga cikin masu ra’ayin Hakkin Allah suna cewa akwai gado kuma babu batun zabi a jagoranci, wannan kuma ya tababatar da abubuwa biyu da suka sanya dalilin shiga Shi’anci: Wannan al’amari ina ganin duk wanda ba ya girmama hankalinsa shi ne zai kawo shi, domin yaushe ne dai kawai don kun yi tarayya da mutum a wani abu na akidu sai a samu haduwa a akida daya ya jefar da tasa ya yi riko da taka. (Kamar yadda su masu sukan suke kawo cewa Farisawa sun yi wurgi da ta su akida suka shiga shi'anci saboda kawai sun yi tarayya da shi a wani abu! Wannan wace irin wauta ce? Yaushe ne wani mai hankali yake yin hakan?)



back 1 2 3 4 5 6 next