Farisancin Shi'anci 2



Bayan wannan gabatarwa ina iya koma wa zuwa ga yaran mustashrikai wadanda suka bi sahun malamansu suka bi su ido rufe a wadannan ra’ayoyin na Farisancin Shi’anci, da suka hada da:

1- Dakta Ahmad Amin:

Dakta Ahmad Amin ya tafi a kan cewa ra'ayin tunanin Farisawa ne ya mamaye Shi’anci, (duk da kuwa cewa Shi’anci ya riga Farisawa) domin mafi yawan Farisawa kamar yadda shi Ahmad Amin ya raya cewa tunanin Shi’anci ya mamaye su, kuma haka nan kana iya duba abin da ya fada na fentinsa na Farisanci, duba abin da ya fada:

Abin da nake gani kamar yadda tarihi yake nuna mana cewa Shi’anci ga Ali (a.s) ya fara tun kafin shigar Farisawa cikin musulunci ne, sai dai wannan da ma’anar Shi’anci mai sauki ce, amma Shi’anci da wannan ma’anar sabuwa ya samu kafuwa ne sakamakon wasu tunani da suka shiga cikinsa daga wasu jama’ar ne, kuma tunda mafiyawan wanda ya shiga musulunci su ne Farisawa to suna da rawa babba da suka taka wajen yin tasriri kan al’amarin Shi’anci.

A wani wurin yana cewa: Kallon Shi'a ga Imam Ali da ‘ya’yansa shi ne irin kallon su ga sarakunan sasaniyya, kuma imani da Ubangizai biyu na Farisawa shi ne asasi da rawafidawa suke dogaro da shi a musulunci, sai wannan ya motsa mu’utazilawa domin ture hujjojin rawafidawa.

A nan ina neman mai karatu ya yi la’ari ya lura sosai da wannan mummunan suka mai kaifi da warin sharri da hura wuta yake kunshe a cikinsa don gani da matakin Ahmad Amin da ire-irensa, kuma muna ganin Ahmad Amin ya saba da kawo wannan fikira da dogaro da ita kamar yadda yake a fili a cikin dukkan wallafe-wallafensa. Ba komai ba ne ya cika cikin Ahmad Amin sai gaba da kiyayya da mugun kaidi da mugun kulli kan Shi'a, hada da koyi da mustashrikai da yake yi kan abin da suke fada.

2- Sheikh Abu Zuhura ya tafi a kan irin wannan ra’ayi na Ahmad Amin yana mai karawa kan haka da cewa: Mafi yawan Shi'a na farko Farisawa ne. Duba abin da yake fada a wannan al’amarin yana mai kawo ra’ayoyin mustashrikai yana mai karawa a kan haka da cewa: A bisa gaskiya Shi'a sun tasirantu da tunanin Farisanci ne game da mulki da gado, kuma yana mai karawa da cewa mafi yawan Farisawa har yanzu suna daga cikin ‘yan Shi'a ne, kuma shi’an farko sun kasance daga Farisawa ne!.

Allah ya ji kan Attayyib Mutanabbi yayin da yake fada a wani Baiti nasa da cewa: Zamanin da mutanensa mutane ne kanana, koda kuwa suna da jiki manya manya. To Abu Zuhrata ma wannan Baiti ya hau kansa yayin da yake cewa: Shi'an farko sun kasance daga mutanen Farisa ne.

Don Allah ina nema daga dukkan wani mai kartau ya fitar mini da mutane biyar daga Farisawa a Shi’ar farko, kuma ina karfafa musu tun da can ba zasu iya samun wannan adadi ba. Shin akwai wata kima da ta rage ga irin wadannan maganganu na Abu Zuhra, kuma magana nawa ce kuke tsammanin Abu Zuhra ya yi ta haka nan babu wani dalili.

3- Ahmad Adiyyatul-Lah:

Wannan mutumin yana daga cikin wadanda suka bi sawun mustashrikai a kan Farisancin Shi’anci, yana ganin cewa fikirar Shi'a ta tasirantu daga wani mutum na jabu da aka kirkira a tarihi aka ba shi sunan Abdullah dan Saba wanda aka ce shi ne ya kawo tunanin shi’anci iri-iri, kuma daga cikinsu akwai cewa shi'anci akida ce bafarisiya, yana mai cewa:

Ibn Sauda (kamar yadda suke kirkirar wannan sunan ga kagaggen mutumin nan wai shi Ibn Saba) ya cirata zuwa Madina, ya yada maganganu da suka saba wa musulunci da sun fito daga yahudancinsa ne, da kuma akidun Farisanci da suka yadu a kasar Yaman, kuma ya fito ne a matsayin mai da’awar taimako ga gaskiyar Imam Ali (a.s), yana mai kiran cewa kowane Annabi (a.s) yana da wasiyyi, kuma wasiyyin Muhammad (s.a.w) shi ne Ali (a.s).

Wannan dai wani abu ne daga cikin misalai na maganganun mustashrikai, kuma kana iya samun wannan gun na wannan zamanin da zaka iya samun wannan a littattafai da suke gadar da tunani tun daga na farko har zuwa masu biye musu, sannan sai ka ga ya yi kokarin ganin ya kafa wannan tunani da dukkan abin da yake da shi na kwarewa.

Mu ba zamu fara raddi kan wannan ra’ayi ba tukun sai bayan mun yi bayanin wadannan ra’ayoyi dalla-dalla tukun wadanda suka kawo bayanin dalilin shigar Farisawa cikin Shi'a’nci, wannan zai kasance kamar shi ne kashin bayan bahasinmu. Kuma mafi girman ra’ayoyin da suka kawo na ganinsu na dalilin shigar Farisawa cikin Shi’anci sun kasu gida uku kamar haka ne:

Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id



back 1 2 3 4 5 6