Farisancin Shi'anci 2



Fasali Na Biyu

Maganganun Masu Ganin Farisancin Shi’anci

magana kan danganta Shi’anci da Farisanci ta kasance ne a zamunan baya-bayan nan ne, kuma saboda wasu dalilai da yanayin siyasa wadanda mafi muhimmcinsu su ne:

Saboda kasancewar Farisawa suna da bakin jini gun Larabawa saboda wasu dalilai daban-daban, kuma saboda Shi'a sun kasance jama’a ce wacce take mai gaba da hukumar lokacin da ya gabata na farkon musulunci a lokacin Umayyawa da Abbasawa.

Kuma ta wata fuska wannan ya faru ne domin ganin an taskace Shi’anci da wanda ake ganin yana da bakin jini gun Larabawa, musamman ma domin ganin Larabawa ba su karbi wannan mazhabi ba, kuma wannan da’awa da ake yi ta taskace Shi’anci da Farisanci daya ce daga cikin kokarin da ake yi na ganin yin zagon kasa ga Shi’anci. Amma dalilan da su masu wannan kage kan Shi’anci suka kawo a matsayin dalilan da suka kai ga kyamar juna tsakanin Larabawa da Farisawa su ne kamar haka:

1- Farisawa ba su kasance suna banbancewa ba tsakanin musulunci da Larabci, kuma tun da musulunci ya kawar da daularsu kuma ya gama da su, to sai suka kasance bayan sun musulunta suna son dawo da martabarsu, kuma suka dauki hanyoyi biyu mai kyau da maras kyau, sai mulkin Umayyawa ya zo ya nemi taimakonsu wajen tafiyar da hukuma domin tsara al’amuran daularsu sakamakon ci gaban da suke da shi na zamani, wani lokaci kuma a kan nemi taimakonsu domin fuskantar abokan gaba yayin sabani, kuma wasu daga cikinsu sun kama manyan mukamai a wadannan lokauta biyu abin da ya sanya su suka samu damar kutsawa cikin daula, kuma wannan ya sanya gaba tsakanin larabawan kansu da kuma Farisawa a daya bangaren, domin Larabawa suna ganin su ne suka dauki sakon musulunci zuwa ga al’umma, kuma su ne wadanda musulunci ya doru ya kafu bisa kafadunsu da wahalarsu domin su shiryar da al’ummu, to don me za a shugabantar da wani a kansu? a gabatar da shi a kansu tauraruwarsa ta yi sama ta filfila a kan tasu? Su sami matsayi mai girma da ba su da shi?

Sai Farisawa suka ga cewa su ne suke da ci gaba mai dadewa kuma sun fi sanin al’amarin siyasar tafiyar da mulki fiye da Larabawa, da tafiyar da al’amarin hukunci da daula, to don me za a gabatar da wanda ba shi da wannan siffofi na cancanta a kansu?. Sai wannan ya kai ga jayayya da gaba tsakanin al’umma, kuma wannan ya bar kufai mai muni a zukata na gaba da juna da kiyayya da mugun kulli tsakanin wadannan al’ummu biyu kamar yadda ya kai ga yin zagon kasa ga juna.

2- Bude wannan fage da samun wannan kafa da sabani da tsagewar bango da Farisawa suka shigo ta cikinsa, ya kai ga shigar wasu mutane da ba Larabawa ba kamar turkawa da wasunsu cikin mukaman daula, kuma wannan ya haifar da mummunan sakamako mai muni kwarai da gaske, kuma sai Sunan Farisawa ya fi baci kan wannan al’amari domin da su ne aka fara wannan asakala, domin su ne farkon wanda ya bude wannan kofa abin da ya kai ga lalacewar halifanci daga baya.

3- ‘Yan mulkin kama karya sun iza wutar wannan matuka da gaske wacce suka azuzuta ta, domin tabbatar da maslaharsu ta hanyar bude wannan kofa da fadada ta da kuma kawo kage da karairayi domin karfafa wanan sabanin tsakanin wadannan jama’u biyu da suka dade suna asakala da rashin jutuwa da juna, kuma suka yi amfani da mustashrikai (Turawa masana gabas musamman kasashen musulmi da addinin musulunci) a kan wannan, sai ga shi an samu jama’ar musulmi da suka rayu a kan teburin nan na koyarwar mustashrikai da suke da karancin tunani da hankali sun kama sun fi mai kora shafi, suna tabbatar da wannan da’awowin karyar su. Sai suka sanya irin wadannan musulmi kamar wata wuka ce da ake dukan duk bangarorin musulmi da su domin rusa akidunsa da kawo tashin hankali da fadada sabani tsakanin mabiyansa, har wannan ya bar kufai mai muni mai girma da yake neman ganin bayan duk kokarin da aka yi, a yau ana bukatar wani kokari mai girma domin kawar da wannan asakala.

Dalilan gaba sun kasance suna daga cikin dalilan da ake riko da su domin ganin an kawo kiyayyar Shi'a da kuma kyamarsu. Don haka ne ma ba za ka ga irin wannan tuhuma ga Shi'a a gun yan Sunna na farko ba sakamakon cewa babu irin wadannan dalilai a can baya a wancan zamani. Kuma wani abin mamaki shi ne; harsunan da suka fi kowa zagin Shi'a a wancan zamani -kafin su kansu Farisawa su zama Shi’a- zaka samu harsuna ne na Farisawa kamar yadda zamu kawo maka nan gaba kadan.



1 2 3 4 5 6 next