Farisancin Shi'anci 2



5- Mustashriki Brukle Man:

Yana cewa: Shi’anci ya kasance abu ne da ya hada dukkan jama’ar da take gaba da Larabawa, kuma a yau kabarin Husain (a.s) ya kasance wuri mafi tsarki gun Shi'a musamman farisawan da ba su gushe ba suna ganin zuwa wannan wuri da tarewa a wurin shi ne babban burinsu da suke son cimma sa. A takaice dai idan mun koma wa bahasin mustashrikai a wannan al’amari zamu ga mutane masu yawa daga cikinsu sun tafi a kan wannan ra’ayi saboda wasu dalilai da ba boyayyu ba ne (ga mai hankali).

Kuma suka fitar da wata natija da suke so sakamakon damfara Shi’anci da Farisanci, kuma wannan sakamakon shi ne: Wato; tunda mafi yawan Farisawa Shi’a ne, kuma ana kiransu ‘yantattun bayi, kuma tun da Larabawa sun kwace musu daularsu, kuma tun da daular Umayyawa tana da tunanin Larabawa ne, sai su wadannan ‘yantattu suka yi kokairn ganin sun kayar da ita, kuma sun kafa daular Abbasawa wacce ta taimaki Farisawa, wacce tunanin Shi’anci ya shige ta kuma ya karfafa a cikinta sakamakon mulkin Abbasawa, kuma kana iya samun wadannan tunani gun mafi girman littattafan wannan zamani na musulunci musaman marubuta misirawa. Don haka muna iya fitar da natija kamar haka:

1- Sawwala kai harin nan na rundunar da ta zo daga Khurasan domin gamawa da daular Umayyawa da cewa na kabilanci ne, ba don al’umma ko mutuntaka ba ne, kuma wai jama’ar da ta taru mai kabilu masu yawa sun taru ne domin kawar da hankula daga hadafin nan da yake boye karkashin wannan harin.

2- Kuma cewa wuta uwar gami a wannan harin su ne Farisawa, domin su kawo hari na daukar fansa da yake son dawo da kima da martabar Farisawa ne wanda Larabawa suka kawar da shi, don haka ne da wannan sai a shafi babbar rawar nan da Larabawa suka taka wajen samun jagoranci.

3- Kasancewar tunanin Shi’anci yana cikin kwakwalen wadannan makiya da suka ci nasara a lokacin Abbasawa.

Sai dai dukkan wadannan al’amura ne da ba su faru ba, kuma ba za a yarda da su ba, kuma kokarin rufe abin da aka kasa tabbatarwa ne kawai.

 

Dorawa Kan Maganganun Farko



back 1 2 3 4 5 6 next