Farisancin Shi'anci 2



Masu hadafin cimma maslaharsu sakamakon iza wutar wannan al’amari suna da yawa sai dai mun samu mustashrikai sun fi karfafawa kan iza wannan wutar, sannan kuma sai muka ga dalibansu masu daukar tunani daga garesu daga musulmi suna buga irin wannan gangar da su ma mustashrikai suke bugawa, wato; suna hura wannan wutar ta kyamar Shi’anci da kuma raba masa Farisanci domin cimma hadafinsu da manufarsu, kana iya duba ra’ayoyinsu kamar haka:

1- Mustashriki Duzi:

Mustashriki Duzi yana ganin cewa asalin Shi’anci mazhaba ce mai dauke da tunanin Farisanci, wannan kuwa ya kasance sakamakon cewa Larabawa suna rayuwa ne da ‘yanci game da mulki, su kuma Farisawa suna da tunanin mulki da gado, ba su san ma’anar zabe ba, kuma tun da Annabi (s.a.w) ya tafi bai bar mai gado ba, to wanda ya fi kowa cancantar halifanci bayansa shi ne dan amminsa Ali (a.s).

2- Mustashriki Pan Pulotin:

Wannan ma yana ganin irin ra’ayin da ya gabata ne, kamar yadda ya kawo a littafinsa na "Siyadatul Arabiyya" sai dai yana ganin cewa Shi'a sun riki wannan ra’ayi ne daga yahudawa fiye da yadda suka karba daga Farisawa, da dokokinsu na asali.

3- Mustashriki Brawon:

Yana ganin cewa: Ba a riki tunanin cewa jagoranci na Allah ne ba da karfi (tsakanin musulmi) kamar yadda Farisawa suka rike shi, kuma sai ya yi nuni da cewa Shi'a sun samu wannan ne daga garesu.

4- Mustashriki Welhozan:

Wannan mustashriki yana ganin cewa Farisanci ya kunshi wani yanki mai yawa na Shi’anci a cikinsa ta yadda ya ambaci cewa sama da rabin mazauna birnin Kufa na daga wadanda ba Larabawa ba duk Shi'a ne, kuma mafi yawansu Farisawa ne.



back 1 2 3 4 5 6 next