Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa Ba



Amma duk da haka sai ya kira Ahlu-baiti (a.s) masu fandarewa masu bidi’a a nazarin ra’ayin Ibn khaldon, Allah ya sani, da zan zo da irin wadannan misalai da zan sanya hannu ne kawai a kan mikin da ya halakar da mu yana kunkuna ga zukata shekaru masu yawa. Kuma irin wadannan matakai na sukan juna ba komai suke zurfafawa ba sai sabani, don haka ne ma ambatonsu wani lokaci yake zama ba daidai ba.

Marubutan musulmi suna da nauyi a kansu na tsayawa kan wannan al’amuran da wadanda suka rubuta su suka mutu suka bar abin da yake bala'i a kan musulmi. Kuma wani abin mamaki a nan shi ne; shirun malamai da marubutan musulmi a kan irin wadannan maganganu na Ibn Khaldon da waninsa tare da samun dalilai masu karfi a kan cewa alayen Muhammad (s.a.w) su ne ci gaban wannan sako da ya zo da shi. Hada da cewa dukkan wannan ya zo a cikin sunnoni da aka ruwaito a tafarkin Ahlu-baiti (a.s) da ba a aiki da su alhalin ana aiki da bidi’o’in da istihsan ya zo su a tafarkin wasunsu, ka riki misali mas’alar kiran salla da aka cire wata fakara a cikinsa ta "Hayya ala khairil amal" tare da tabbatarta da cewa ya tabbata cewa ita wani yanki ne na kiran salla ta hanyoyi masu yawa.

Mai littafin Maba’di’ul Fikihu game da hakan yana cewa: Ga yadda ake kiran salla: Allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar, ash’hadu an la’ilaha illal-Lah, ash’hadu an la’ilaha illal-Lah, ash’hadu anna muhammadar rasulul-Lah, ash’hadu anna muhammadar rasulul-Lah, hayya alassalat, hayya alassalat, hayya alal falah, hayya alal falah, allahu akbar, la’aila illal-Lah. wannan shi ne kiran sallar da mutanen Basara da na Kufa suka hadu a kansa, kuma mutanen Sham da Misira suka bi su a kai, kuma shi ne mazhabar mutane Hijaz da Zaidiyya da Malikiyya, sai dai su a wajensu kalmar Allahu akbar sau biyu ce a kiran salla ba sau hudu ba, kuma a kan wannan ne mutanen Madina suke. Amma kalmar "Assalatu khairun minan naum" ba kiran salla ba ce na shari’a tun asali: A cikin littafin â€کTaisirul wusul" ya zo daga Maliku cewa: Labari ya zo mini cewa mai kiran salla ya zo wajen Umar dan Khaddabi, yana yi masa kiran sallar asuba, sai ya samu yana bacci, sai ya ce: Assalatu khairum minan nau. Sai Umar ya umarce shi da ya sanya ta a cikin kiran sallar asuba! Don haka ne ma Abuhanifa ya ce: Wannan jumlar ana dada ta ne bayan kammala kiran salla, domin ita ba ta daga Sunna.

Amma kalmar "Hayya ala khairul amal" a mazhabar Ahlu-baiti (a.s) tana tsakanin "Hayya alal falah" da "Allahu akbar" ne. Dalilinsu kan hakan daga sunnan shi ne: Baihaki ya ruwaito a cikin Sunan dinsa cewa Aliyyu bn Husain -Zainul abidin- (a.s) ya kasance idan ya ce: "Hayya alal falah" to yana cewa kuma "Hayya ala khairul amal", yana cewa haka kiran sallar farko yake.

Kuma ya zo a cikin sharhin Tajrid kamar dai irin wannan ruwaya daga Bin Abi Shaiba sannan sai ya ce: Bai kamata ba a dauka a fadinsa wannan shi ne kiran sallar farko da cewa shi ne kiran sallar Manzon Allah (s.a.w), ya kuma dada kawo wata ruwaya daga Ibn Umar ya ce: Tayiwu ya dada wannan yanki na "Hayya ala khairul amal" a kiran sallarsa ne. kamar yadda Baihaki ma ya kawo wannan ruwaya daga Ibn Umar.

Ibn wazir ya karbo daga Al’muhib Dabar AsShafi'i a littafinsana "Ihkamul Ahkam" kamar haka: Ambaton hai’ala wato; "Hayya ala khairul amal" ya zo daga Sadaka dan Yassar daga Ibn Umama Sahal dan Hanif cewa idan zai yi kiran salla yana karawa da "Hayya ala khairul amal", Sa'id dan Mansur, ya karbo shi, kuma Ibn Hazam ya ruwaito daga littafin al’ijma daga Ibn Umar: Cewa ya kasance yana cewa "Hayya ala khairul amal".

Ala’uddin Mugaldaya Alhanafi ya fada a littafinsa na "Attalwih" sharhin jami’us sahih: Kamar haka: Amma "Hayya ala khairul amal" Ibn Hazam ya ambaci cewa ya inganta daga Abdullah dan Umar da Abi Umama Sahala dan Hanif cewa suna ambaton ta a kiran sallarsu "Hayya ala khairul amal", kuma aliyyun dan Husain yana yin hakan, kuma Sa’aduddin Taftazani ya ambata a hashiyar sharhin "Al’adhudi ala mukhtasaril usul" na Ibn Hajib cewa "Hayya ala khairul amal" ta kasance a lokacin Annabi (s.a.w) kuma Umar shi ne ya takura mutane su daina wannan, jin tsoron kada su yi rauni gabarin jihadi su dogara da yin salla kawai.

Ibn Hami ya fada a littafinsa: Kuma Ruyani ya kawo daga Shafi'i wata magana mash’huriya game da shi da ya fada game da "Hayya ala khairul amal", kuma da yawa daga malaman malikiyya da wasunsu na hanafiyya da Shafi'iyya sun ambaci cewa "Hayya ala khairul amal" tana daga lafuzzan kiran salla.

Zarkashi yana fada a littafin "Baharul Muhid": Daga cikin abin da aka yi sabani a cikinsa kamar sabanin da aka yi ne a cikin waninta, Ibn Umar ya kasance madogarar mutanen Madina yana ganin "Hayya ala khairul amal" daga cikin kiran salla yake[13].

Bayan dukkan abin da muka ambata da kuma abin da ya zo a cikin wannan fasali da aka karfafa da ruwayoyi ingantattu a tafarkin ahlussunna don me ya sa ba a aiki da abin da ya zo daga alayen Muhammad da tafarkinsu na Sunna sahihiya tare da cewa su ne masaukar rahamar Allah kuma gidajensu ne masaukar wahayi, kirazansu kuwa jakar ilimin Annabi (s.a.w), shin wannan ba ya kawo wata dimuwa?



back 1 2 3 4 5 6 next