Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa Ba



To al’ummu biyu[4] su shaida ni barawafide ne

Baiti na karshe na wannan baitoti da Zubaid ya fada a littafin tajul'arsu a kalmar rawafidhawa da sauranta a bayanin tarihin Shafi'i ya zo a cikin littattafai masu yawa[5].

Kuma bayanin Imam Shafi'i da yake cewa: Idan dai son alayen Muhammad shi ne rawafidanci yana nuna cewa ana amfani da wannan kalma a kan dukkawan wani dan Shi'a har ma wannan kalma ta rawafidhanci ta shahara garesu kuma an yi amfani da shi don kinsu, kuma a cikin wannan akwai misali masu yawa, kuma daga cikin abin da yake nuna akwai wani kaidi da ake yi wajen amfani da wannan kalma shi ne yadda aka dora wa Shi'a wannan suna kuma har suka shahara da shi, shin an yi amfani ne t a hanya mai kyau ko maras kyau.

3- Tayiwu a ce babu makawa akwai wasu mutane masu zagin sahabbai amma me ya sa suka kasance hakan, yayin da Shi'a su ba su yarda da zagi ba haka ma imamansu ba su yarda da shi ba? Amsa ita ce ba makawa mu koma zuwa ga wasu dalilai da suke tasowa sakamakon wani abu na takurawa da ya haifar da wannan al’amari, kuma daya daga cikinsu shi ne:

 

Dalilan Zagi

a- Korewa da azabtarwa mai ban tsoro ga Shi'a da kuma abin da suka wahala sakamakon kisa ko kawarwa da batarwa bisa zato da tuhuma, mafi kyawun halin da suka samu kansu a kansa shi ne bin su da kuma yakar su da aka yi bisa lamarin tatattalin arziki da hana su baitul mali, da kuma dora musu haraji mai tsanani, da kuma kawar da su a siyasance. Kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga tarihin Umayyawa a Kufa da wasunsu na daga garuruwan Shi'a domin ya san abin da halin ya kai su zuwa gareshi da abin da suka tuke zuwa gareshi a hannun Umayyawa na kekasar zuciya da kuma take hakkin â€کyan’adamtaka da cin mutuncin da hatta da dabbobi suna barranta daga wannan al’amari da ya faru a lokuta biyu; na Umayyawa da Abbasawa[6].

Irin misalin wannan cusgunawa tana bukatar a samu wata hanyar lumfasawa daga wannan matsi mai tsanani kuma wannan lumfasawa domin samun sauki tana iya kasancewa ta hanya mai kyau, wani lokaci kuma tana iya kasancewa ta hanya maras kyau kamar zagi. Sai dai mu ba muna cewa yin zagin daidai ba ne a kowane hali kuwa kamar yadda ya gabata.

b- Kuma wanda ya assasa wannan al’amari su ne Umayyawa su da kansu domin sun zagi Ali (a.s) a kan mimbari suka kuma zagi Ahlu-baiti (a.s) tsawon shekaru tamanin, kuma wannan yanayi ya ci gaba duk da kuwa kokarin da wannan mutum mai kirki Umar dan Abdul’aziz ya yi na ganin ya kawar da wannan zagi amma bai ci nasara ba, kuma maganganun Banu Umayya musamman Mu’awiya sun riga sun karfafa cewa sun assasa wannan zagin ne domin yaro ya girma a kansa kuma babba ya tsufa a kansa, sai aka samu wannan zagi da ake tuhumar Shi'a da shi domin su yi ramuwar gayya. Kuma idan mutum ya zurfafa sosai zai ga cewa an samu karkatar hanyar warware wannan matsala wajen wasu malaman Sunna. Muna iya ganin misalin dan Taimiyya yana wallafa littafin nan na "Takobi zararre a kan kafirta duk wanda ya zagi Annabi (s.a.w) ko daya daga cikin sahabbai", yana kuma kawo dalilai a kan kafirta wannan zage-zage da ake yi sai dai duk da ya san Mu’awiya ne ya assasa wannan zagin da Umayyawa da zagin da suka yi wa Imam Ali da Ahalin gidansa da la'antar su, amma bai kafrita su ba. Aliyyu dan Abi Dalib (a.s) dan’uwan Annabi (s.a.w) ne kuma ya bayar da komai nasa wajen yin hidima ga musulunci da musulmi amma saboda me wanda yake zaginsa ba ya kafirta? A nan ne zaka ji wani jawabi mai ban mamaki ai ya tuba kuma Allah ya gafarta masa shi ke nan wai an warware wannan matsalar!!

Duba wani misalin: Yayin da Yazid dan Mu’awiya ya hau kan hukunci na shekaru uku kawai a shekarar farko ya kashe Imam Husain (a.s) da ahlin gidan Annabi (s.a.w) kuma ya ribace iyalinsu ya kuma yanka â€کya’yansu kuma ya yi musu abin da ko kisra da kaisar ba zasu yi musu ba.

A shekara ta biyu ya kashe musulmi dubu goma da makaranta Kur'ani dari bakwai daga sahabbai, sannan kuma ya halatta Madina kwana uku, ya ba wa rundunar Sham damar su keta mutuncin musulmai, ya yanka iyaye da yaransu, har sai ka ga sojan Sham ya dauki mai shan nono daga hannun uwarsa ya buga kansa a kan bango har sai kwakwalwarsa ta yi tarwatsi a kan bango, sannan kuma ya tilasta mutane yi wa Yazid bai’a a kan cewa su bayinsa ne, kuma ya tsorata Madina ya firgita mutane sannan kuma ya mayar da wannan gari na Annabi mai haske zuwa ga wata fadama da ta lalace da jini kaca-kaca.



back 1 2 3 4 5 6 next