Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa Ba



A shekara ta uku kuwa ya sanya wa Ka’aba majaujawa kuma ya rusa ta kuma ya kona ta, sannan ya rusa rukunanta sannan ya yi yaki har cikin masallaci mai alfarma ya zubar da jini har sai da ya kwarara a Ka’aba, kuma mai litttafin "Tarihin Hamis" da "Diyarul Bakari" da "Dabari" da "Ibn Asir" da Mas’udi a "Murujuzzahab" da wasunsu na daga malaman tarihi sun kawo wannan dalla-dalla cikin bayain abubuwan da suka faru a shekarar sittin da daya har zuwa sittin da uku tahijira.

Amma duk da haka sai ka samu wasu da yawa daga malaman Sunna suna nuna kuskuren wanda ya fito domin yakar Yazid kuma suna ganin fitowa domin yakarsa fita ce daga addini, kai har wasu ma suna kai da nuna kuskuren Imam Husain (a.s) shugban samarin aljanna, kamar kai ka ce lokacin da Annabi (s.a.w) yake cewa: "Hasan da Husain (a.s) su ne shugabannin samarin â€کyan aljanna" bai san zai yaki Yazidu ba ne, kuma lokacin da Annabi (s.a.w) yake cewa: "Hakika Husain (a.s) da sahabbansa zasu shiga aljanna ba tare da wani hisabi ba[7]" kai kace bai san cewa zasu yaki Yazidu ba. Kai Allah ka shiryi mutanenmu! kai ka ce Ibn Arabi Almali ya fi Annabi (s.a.w) sanin makomar al’amura ne da yake nuna wa Husain (a.s) makomar al’amura kuma yana umartarsa da ya zartar da hakan!

Wai zuwa ga wane kaskanci da tabewa ne wannan duniya zata kai mutanen!

Sai mu ga Gazali a cikin abin da ya kawo irin wadannan abubuwan alhalin kuwa ga shi a gabansa akwai gomomin littattafai na tarihi da suke da karfafan hanyoyi amintattu kan al’amarin Yazid da ayyukansa. Sai ga shi amma a littafinsa na Ihya’ul ulum yana cewa game da la’antar Yazid:

Idan aka ce: Shin ya halatta a la’anci Yazid domin ya kashe Husain (a.s) ko kuma ya yi umarni da hakan? Sai mu ce: Wannan bai tabbata a bisa asali ba, don haka bai halatta ba a ce shi ne ya kashe shi ko kuma ya yi umarni da hakan matukar hakan bai tabbata ba, balle kuma a la’ance shi, domin bai halatta ba a danganta wa wani musulmi babban laifi ba tare da wani tabbaci ba, har dai yake cewa: Idan aka ce yaya fadin cewa "Allah ya la’anci makashin Husain (a.s), ko kuma wanda ya yi umarni da kashe shi" sai mu ce: Abin da yake daidai shi ne a ce: Wanda ya kashe Husain (a.s) idan ya mutu kafin ya tuba to Allah ya la’ance shi[8].

Don Allah mai karatu shin tunaninka zai iya jore wa jin wani yana fadin irin wadannan kalamai da suke zowa daga irin wannan mutumim!? Shin littattafan tarihi da suke hannun musulmi wadanda suka zo da wadannan al’amura da suka faru da umarnin Yazid kai tsaye dukkansu ba sa iya tabbatar da ayyukan Yazid ko kuma su hukunta shi su soke shi?! A wajensa yana ganin Yazid da ire-irensa makasa annabawa da â€کya’yan annabawa duk suna samun dacewar tuba?! Kuma duk wata hanya ba ta iya tabbatar da sukan Yazid gun Gazali, sai dai kawai abin da yake tabbata gunsa shi ne ya ga Yazidu ya hadu da Allah ya sanya hannunsa a kan hannunsa, kuma ya yi masa magana, kuma ya kwarara masa haskensa, da gafararsa[9].

Mai littafin Miftahussa’adati yana cewa: Abubakar Nassaj ya yi shisshigi kan al’amarin Gazali a kabarinsa ya fito yana mai jirkitaccen launi, sai suka tambaye shi me ya faru. Sai ya ce; Na ga wani hannun ne na dama ya fita ta bangaren alkibla, kuma na ji wani mai shela yana kira cewa dora hannun Muhammad Gazali a kan hannun shugaban manzanni[10]. Sai ga irin wannan ya isa ya tabbatar da hujja a irin wannan, amma dukkan littattafan tarihi dukkansu ba sa iya tabbatar da wata hanya guda daya da zata soki Yazid!..

Kai al’amari ya kai ga jifan alayen Annabi da fita daga kan hanya, balle kuma share fagen zaginsu. Sai ga Ibn khaldon a mukaddimarsa yana cewa: Ahlu-baiti (a.s) sun fita daga hanya da kirkiro wata mazhaba da suka kago ta, suka kuma kadaita da ita a kan sukan wasu daga sahabbai, da kuma fadinsu na ismar imamai da kuma kawar da sabani daga zantuntukansu, kuma dukkan wannan asasi ne maras tushe.

Yana fadin haka alhalin ga hadisan Annabi (s.a.w) a game da Ahlu-baiti (a.s) a gabansa da Ibn hajar ya ruwaito a littafinsa na Sawa’ikul Muhrika[11] cewa: "A cikin kowane zamani akwai masu adalci daga adalai daga Ahlin gidana da suke kore wa wannan addini karkatar batattu da hanyar mabarnata da kuma tawilin jahilai, ku saurara hakika jagororinku su ne masu zuwa ga Allah, sai ku duba wanda zaku zo tare da shi (a matsayin shugaba a ranar lahira".

Haka nan yana ganin abin da Hakim ya ruwaito a littafinsa na Mustadrak mai cewa: "Wanda ya so ya rayu irin rayuta kuma ya mutu irin mutuwata ya shiga aljanna da Ubangijina ya yi mini alkawarinta, ita ce aljannar dawwama to ya jibanci Ali da zuriyarsa bayana, hakika su ba zasu fitar da ku daga shiriya ba, kuma ba zasu shigar da ku kofar bata ba[12].



back 1 2 3 4 5 6 next