Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa Ba



Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa Ba

Daga dukkan abin da aka ambata zai bayyana cewa abin da masu rubuce-rubuce suka saba na jifan Shi'a da rawafidanci da kuma kiran su da wannan suna ya faru ne daga bayan saboda wasu dalilai da zamu kawo wasu a nan:

 Wannan zamani da aka fara kiran Shi'a da rawafidawa a lokacin Umayyawa ne, shi ya sa wasu littattafai suka zo suna siffanta rawafidawa da cewa wasu bangare ne su na Shi'a, ba wai Shi'a ba kamar yadda wasu suke son kawowa a wasu nassosi:

1- Muhamamd Murtada Zubaidi a Tajul Arus ya ce:

Rawafidawa dukkan wata runduna da suka bar jagoransu, kuma ana gaya wa wasu jama’a daga Shi'a Sunan rawafidawa. Asma’i ya ce: An kira su da wannan suna ne saboda sun yi bai’a ga Zaid dan Ali sannan sai suka ce ya barranta daga shaikhaini sai ya ki ya ce: Ba zai yi ba domin sun kasance wazirai ne na kakansa, sai suka bar shi suka ki shi sannan suka waste suka bar shi[1].

2- Isma’il dan Hammad Al’jawahiri ya fada a cikin Sihah:

Gun kalmar nan ta Rafadha, sai ya fadi abin Zubaidi ya fada kamar ya kwafa daga asali ne[2].

3- Al’kali Iyad:

Al’kali Iyad ya bambanta a littafinsa na "Tartibul Madarik fi a’alami mazhabi Malik" tsakanin Shi'a da rawafidhawa, yayin da ya kwatanta mazhabar Maliku da watanta ya ce: Ba mu ga wata mazhaba da tafi rashinsu kamar malikiyya ba, domin a cikin watanta akwai jahamiyya da rawafidhawa da khawarijawa da mur’ji’a da Shi'a, sai dai kawai mazhabar Maliku, domin ba mu ji wani ya cirato irin wadannan bidi’o’i ba a cikinta[3].



1 2 3 4 5 6 next