Halayen Imam Sajjad (a.s)



Haka nan sauran imamai (a.s) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri, da kuma azabtar da su da dukkan nau’i na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su yayin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba, sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu, suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyyawa da wasunsu, bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa son haka su kansu.

Imam Ali Zainul-abidin shi ne ne Sajjad, Sayyidul abidin (a.s) dan Husain, babarsa ita ce Shahar banu 'yar sarki Yazdajir, kuma ana cewa da shi dan masu alheri biyu, saboda fadin Manzo (s.a.w) cewa: Allah yana da masu alheri zababbu biyu daga bayinsa, zababbunsu daga larabawa kuraishawa, daga ajamawa kuwa farisawa, a kan haka ne ma abul aswad ya yi waka yana mai cewa:

Wani saurayi ne tsakanin Kisira da Hashim

Mafi girman wanda aka alakanta masa kamala

 An haife shi a Madina mai haske ranar alhamis biyar ga watan sha'aban mai girma a shekara ta talatin da takwas daga hijira, kuma ya yi shahada ta hanyar shan guba ranar asabar ishirin da biyar ga watan Muharram shekara ta casa'in da biyar hijira yana da shekaru hamsin da bakwai kuma dansa Imam Muhammad Bakir (a.s) ne ya shirya janajarsa, kuma ya binne shi gun kabarin amminsa Mujtaba (a.s) a Madina mai haske a Bakiyya.

Ya kasance ba shi da kama a ilimi da ibada da fifiko da tsantseni da taimakon masu rfashi, kuma malamai sun rawaito addu'a da wa'azozi da karamomi da yawa daga gareshi.

Ya kasance yana fita da duhun dare sai ya dauki gari a bayansa kuma da jakunkuna na dinare da dirhami kuma yakan dauki abinci a bayansa ko itace har sai ya zo kofa kofa yana kwankwasawa sannna sai ya ba wa wanda ya fito, ya kasance yana rufe fuskarsa domin kada talaka ya gane shi, yayin da ya mutu sai mutanen Madina suka gane shi suka san cewa shi ne mai raba gari.

Hada da abubuwa da yawa da ayke yi na ba wa maraya da miskinai da raunanan abinci da kuma ci tare da su.

Yana daga kyawawan halayensa (a.s) ya kasance yana kiran masu yi masa hidima kowace shekara sai ya ce: Wanda yake son aure daga cikinku zan aurar da ita, idan tana son a sayar da ita zan sayar da ita, idan tana son 'yanci zan 'yanta ta.

Ya kasance idan mai bara ya zo masa yakan ce: maraba da wanda zai dauki guzuri na zuwa lahira.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next