Halayen Imam Sajjad (a.s)



Kamar kuma karantawarka a addu’a ta 39: “Domin kai idan har ka saka mini da gaskiya to zaka halakar da ni, idan kuma ba ka lullube ni da rahamarka ba to zaka halakar da ni, kuma ina rokon ka ka dauke daga zunubina wanda daukar nauyinsa ya gajiyar da ni, ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyarsa, kuma ka yafe wa raina zunubanta da zaluncintaâ€‌.

Na Hudu: Jan mai addu’a zuwa ga dauke sawunsa daga aikata munanan ayyuka, da siffantuwa da munanan siffofi domin wanke ruhinsa da tsarikake zuciyarsa, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 20: “Ya Allah ka cika mini niyyata da ludufinka, kuma ka inganta mini yakinina da abin da yake gare ka, ka gyara min abin da ya baci daga gare ni da kudurarka, Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad ka jiyar da ni dadi daga shiriya ingantacciya da ba zan taba neman musanya daga gareta ba, da kuma hanya ta gaskiya wacce ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya da ba zan taba kokwanto a cikinta ba.

Ya Allah kada ka bar wani hali da yake aibi ne da ake aibata ni da shi sai ka gyara shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi sai ka kyautata shi, ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai ka cika Shiâ€‌.

Na biyar: Sanya wa mai karanta addu’ar dauke sawunsa daga mutane, da rashin kaskantar da kansa gunsu, kuma kada ya kai kukan bukatarsa gun wani ba Allah ba, domin kwadayin abin da yake hannun mutune yana daga cikin mafi munin abin da mutum zai siffantu da shi kamar yadda zaka karanta a addu’a ta 20: “Kuma kada ka fitine ni da neman taimakon waninka idan na matsu, da kuma kaskan da kai don tambayar wani ba kai ba idan na bukatu, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba kai ba idan na tsorata, saboda haka sai in cancanci tabarwarka da haninka da kawar da kankaâ€‌.

Da kuma misalin addu’a ta 28: “Ya Allah ni na tsarkake niyyata da yankewa zuwa gareka, kuma na juyo zuwa gareka baki daya, kuma na kawar da fuskata daga dukkan wanda bai wadata da falalarka ba, na ga cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wauta ce, kuma bacewar hankalinsa ne.â€‌

Da kuma misalin abin da kake karantawa a addu’a ta 13: “Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinka, kuma ya yi kokarin kawar da talauci da taimakonka, hakika ya nemi bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ake zaton samu, kuma ya zo wa bukatarsa ta fuskarta da ta dace. Wanda kuma ya juya da bukatarsa kuwa ga daya daga cikin halittunka, ko kuma ya sanya shi sababin samunta ba kai ba, to hakika ya jawo wa kansa hani, kuma ya cancanci kubucewar kyautatawa daga gare kaâ€‌.

Na Shida: Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka wa sashensu ga sashe, da fifita juna a tsakaninsu domin tabbatar da ma’anar yan’uwantakar Musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 38: “Ya Allah! ni ina mai neman uzuri daga gareka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da wani kyakkyawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba, da duk wani mummunan aiki da aka nemi uzurina ban bayar da uzuri ba, da duk wani mabukaci da ya roke ni ban ba shi ba, da hakkin mai hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika masa ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi baâ€‌.

Hakika irin wannan neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abin da zai fadakar da zuciya zuwa ga abin da aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi’u madaukaka.

 A addu’a ta 39 akwai karin haske a kan hakan, sai ya sanar da kai yadda zaka yafe wa wanda ya munana maka, kuma yana gargadin ka game da yin ramuwar gayya, yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakku: “Ya Allah duk wani bawa da ya yi mini abin da na hana shi a kansa, ya kuma keta mini abin da na kange shi gareshi, da nauyin zaluntata, ko zuciyata ta tuna shi yana rayayye, to ka gafarta masa abin da ya yi mini, ka yafe masa abin da ya riga ya gabatar gareni, kada ka tsayar da shi don tambaya a kan abin da ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abin da ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su, da kuma kyautar da na yi musu na daga sadaka garesu, ya zama mafi tsarkin sadakar masu sadaka, kuma mafi daukakar addu’ar ma’abota kusanci gare ka. Kuma ka musanya mini afuwata gare su da afuwarka, da addu’ata garesu da rahamarka, har kowanne daga cikinmu ya rabauta da falalarkaâ€‌.

Mamaki ya girmama ga wannan fakarar ta karshe! da kuma yawan girman tasirinta a cikin zukatan masu alheri! Domin fadakar da su a kan kyakkyawan nufi ga dukkan mutane, da nema wa kowa sa’ada hatta ga wanda ya zalunce su. Irin wannan yana da yawa a cikin addu’o’in Sahifatus sajjadiyya, a cikinta akwai da yawa daga irin wadannan koyarwa ta Ubangiji don tsarkake rayukan â€کyan Adam wacce da sun yi riko da ita da sun kasance masu shiryuwa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next