Halayen Imam Sajjad (a.s)



Imam zainul-abidin (a.s) ya kasance daga cikin wadanda suka fi kowa yin kuka a duniya, har ma ruwayoyi sun zo kan masu kuka da suka hada da Annabi Adam (a.s) da ya yi kuka kan Habil, da Ya’akub da ya yi kuka kan Yusuf (a.s), da Zahara (a.s) da ta yi kuka kan Muhammad (s.a.w), da kuma shi Imam Zainul-abidin sayyidus sajidin (a.s) da ya yi kuka kan Husain (a.s), kuma shi ne wanda ya fi kowannensu yin kuka, ya yi kuka shekara arba’in gaban dayan rayuwarsa hawaye ce. Ba a zo masa da abin ci, ko abin sha, sai ya cika su da hawaye.

Imam Ali Sajjad (a.s) ya kasance madogara ga mutane malamansu da jahilansu mabiyansu, akwai labaru masu yawa game da nasihohin da ya yi wa Zuhuri kan ya bar son duniya da rabuwa da azzaluman sarakuna wadanda suke amfani da shi wurin halatta musu duk wata barna.

Ya shahara da ilimi a cikin al’umma da ba a samu kamarsa ba, kuma kissarsa da malamai da suka tafi a kan cewa babu wani azumin wajibi sai na Ramadan kawai yayin da ya yi musu bayanin azumi da kashe-kashensa duk sai suka dimauce, suna mamakin iliminsa.

Ya shahara da tarbiyyantar da mutane ta hanyar addu’o’I, wani abin kayatarwa shi ne yadda Imam Ali Sajjad (a.s) ya yi amfani da addu’a wurin ilmantar da mutane, da tarbiyyantar da su, abin da ba a samu wani gabaninsa ba da irin wannan usulubi mai kayatarwa.

Bayan lamarin nan mai daci da zogi na abin da ya faru a Karbala Imam Zainul-abidin ya tafi Sham kuma zuwan nasa ya kunyata Yazid tsenanne, ya tona masa asirin karairayin da suka dade suna yi wa mutanen Sham sama da shekaru arba’in tun lokacin jagorancin amminsa Yazid dan Abusufyan ga Sham har mutuwarsa da maye gurbinsa da dan’uwansa Mu’awiya dan Abusufyan baban shi Yazid la’ananne.

Imam Zainul-abidin yana da littafi da ya shahara da aka san shi da Sakon Hakkoki, wanda a yanzu haka ni mai wannan rubutu na fassara shi zuwa Hausa, da sharhin da na yi masa, littafin an fassara shi da yarirrika daban-daban masu yawa. Littafi ne mai muhimmanci da ya tattaro bayanai kan hakkokin Allah da na bayi kan bayin Allah gaba daya.

Imam Zainul-abidin ya kasance mai karimci da kyauta da â€کyanta bayi, da sadaka, da ciyar da mutane, da kyautar boye. Ya kasance yana rufe kansa yana daukar buhuhuwan gari zuwa gidajen mutane da dare, da ya rasu sai aka ga kafadarsa da tabon shacin daukar buhuhuwa, sannan kuma bayan rasuwarsa sai mutane suka rasa kyautar dare, sai suka gane ashe shi ne yake yin wannan alherin. Ya kasance yana ciyar da sama da iyalai dari gaba dayansu.

Imam Zainul-abidin ya kafa makarantar da horar da daruruwan malamai da suka zama madogara kuma gwaraza a fagagen ilmomi daban-daban. Wannan makaranta ta kasance wuri ne da ya kasance asasin kariya ga addini da raddin soke-soken da ake jifan sa da shi, da kuma nauyin koyar da addini sahihi ga duniyar musulmi, da tarbiyyantar da malamai masu ci gaba da isar da sakon Allah madaukaki.

Addu’o’in Sahifatus Sajjadiyya: Bayan aukuwar al’amarin karbala mai ban takaici, da kuma kame ragamar shugabancin al’ummar musulmi da Banu Umayya suka yi, kuma suka dulmuya a cikin danniya, suka yi dumu-dumu da jinin mutane, sannan suka yi watsi da koyarwar Addini, sai Imam Zainul Abidin kuma Sayyiddus Sajidin ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusantarsa, kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba.

 Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu’a wanda muka ambata na cewa, yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Kur’ani da ladubban musulunci, da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (a.s), kuma hanyar cusa wa mutane ruhin addini da zuhudu, da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi’u.

Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar da mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da suke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu’o’i masu zurfi, kuma an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya da ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (s.a.w). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da annabci, kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi’u ababan yabo, da kuma ladubban musulunci. Kuma ta kunshi maudu’ai daban-daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini, da kyawawan dabi’u, ta hanyar addu’a, ko kuma addu’a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi’u. Ita ce salon bayanin Larabci mafifici, kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u bayan Kur’ani da Littafin Nahjul Balagha.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next