Halayen Imam Sajjad (a.s)



 

Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da bayanin halayen Imam Ali as-Sajjad (a.s) da rayuwarsa.

Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da yake kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Imam Ali Sajjad da aka fi sani da Imam Zainul-abidin, ko Sayyidul-abidin, da sauran lakabobi da duniyar musulmi ta san shi da shi ya kasance shi kadai ne ya rage a matsayin burin musulmi da suka dogara da shi wurin sanin addini bayan bala’o’in da suka farwa al’ummar musulmi na musibar kashe Imam Husain (a.s) da zuriyar Annabi (s.a.w).

Ya kasance ya samu kansa a cikin al’ummar da ta farka amma ba ta san makama ba, domin ta rasa wanda zai jagorance ta domin samun kaiwa ga tudun tsira, sannan kuma tsananin toshe gaskiya da aka yi ya sanya mai neman gaskiya ba ya iya samun ta domin ta bace, don haka sai Imam Sajjad (a.s) ya yi kokarin dawo da sanin addini cikin mutane ta hanyar addu’o’insa wadanda suka shahara da wadansu sun zo a cikin littafin nan mai suna Sahifa Sajjadiyya.

Girmansa da darajarsa da kwarjininsa ne suka sanya hatta da makiyansa kuma makiyan Allah da addininsa na gaskiya suka fadi darajarsa da babu kamarta. Sarakunan Banu Umayya sun yi furuci da wannan yayin da zamu ga Abdulmalik dan Marwan yana cewa: An ba shi ilimin da addini da tsentseni wanda ba a ba wa wani kamarsa ba. Kuma Umar dan Abdul’azizi yana kiran sa da cewa shi ne fitilar duniya kuma adon musulunci.

Yana da ruwayoyi masu yawa da yake siffanta Allah da kadaita shi a cikin zatinsa da siffofinsa, da ayyukansa, da bayanai masu girgiza zukata kan mahalicci makadaici. Akwai ruwayoyi masu yawa da aka ruwaito daga gareshi game da sahabban Imam Mahadi (a.s) da falalar sauraronsa da ayyukan masu sauraronsa.

Sannan munazarorinsa da masu saba wa ahlul-baiti (a.s) na daga musulmi da wadanda ba musulmi ba suna da yawa da aka ruwaito su musamman wasu sun zo a littafin “Ihtijajâ€‌ na Dabrsi. Sannan mutanen Makka sun yi tawassuli da shi don a samu ruwa, kuma ya yi musu addu’a aka samu bayan idanuwan al’umma ya zazzaro, fari ya kai su ga shiga wani hali mai tsanani.

Imam Ali Sajjad (a.s) ya shagaltu da Kur’ani matuka fiye da komai, duk da kuwa ya samu shahara a addu’o’I, sai dai ya kasance mai yawan karatun Kur’ani, har ma mutane suna tsayawa kusa da katangar gidansa domin su ji muryarsa yana karanta Kur’ani.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 next