Tattaunawa Ta Hudu



Kai kun ruwaito cewa: manzon rahama (s.a.w) ya riki hannun Hasan da Husain (a.s) sannan sai ya ce: wanda ya so ni, kuma ya so wadannan, da babansu, da babarsu, to ya kasance tare da ni a darajata a ranar kiyama. Masnad Ahmad bn Hambal, j 1, shafi: 77. Tirmizi ya ruwaito shi a j5, shafi:305, ya ambace shi hadisi kyakkyawa. Mai littafin tuhfatul ahwazi bayan ya kawo wannan hadisi yana cewa: kuma ya gabata Manzo (s.a.w) ya ce: Mutum yana tare da wanda yake so. Ka ga ke nan hatta da shi’ar Ahlul Bait (a.s) suna tare da Manzo (s.a.w) a matsayinsa a aljanna. Ina ga wasiyyansa!

Sannan kuma matsayin annabawa (a.s) yanki ne na matsayin Annabi (s.a.w) wanda yake shi ne asali, sannan kuma ka sani ayar mubahala ta tabbatar da cewa Ali (a.s) shi ne nafsi Muhammad. 

Amma maganganun Ali (a.s) na cewa; Ni ne na farko ni ne na karshe…, da ka yi nuni da su a (Rijaal Kashsi, 138. India Print) Ka sani maganganun Ahlul Bait (a.s) suna yi maka nauyi: Imam Ali (a.s) shi ya fadi hakan kuma ya yi bayanin ma’anarta da kansa da take cewa; shi ne farkon wanda ya musulunta, kuma karshen wanda ya hadu da Manzo (s.a.w) domin shi ya binne shi, Kuma shi ne mai ilimin zahiri da badini: Imam Ali (a.s) da sauran imamai (a.s) sun maimata cewa maganarsu tana da nauyi ba mai karba sai mai imani.

Amma batun cewa imamai su ne fuskar Allah a bayan kasa haka take kamar yadda ka kawo shafinta (Usul- e-Kaafi -83.): Wannan lamari haka yake, dukkan imami (a.s) a zamaninsa shi ne; fuskar Allah a bayan kasa: ka sani shi ne shaidar Allah a kan bayinsa, kuma idanunsa, kuma wadannan lamurra sun zo a ruwayoyi mabambanta.

Fuskar Allah ba tana nufin abin da malamanka suke cewa ba ne: Komai zai halaka sai fuskar Allah (S.W.T) wal’iyazu billah. Wani abin mamaki Albani yana ganin duk wanda ya yi tawilin wannan aya ba ma musulmi ba ne, kuma ya rufe idonsa kan tawilin da Buhari ya yi mata. Ka duba "Fatawa Albani" shafi 522, 523. Don haka ya karfafa cewa Allah zai halaka in banda fuskarsa wacce ita ce kawai ba zata halaka ba: wal’iyazu billah!

Ka sani yayin da al’umma ta bar Ahlul Bait (a.s), ba kowa ba ne ya watse ya bar su, domin sun samu masu karba daga garesu. Ka duba ka gani mana wancan bangaren ya ruwaito hadisai 5 374 daga Abuhuraira da ya zauna da Manzo (s.a.w) wata goma sha shida ne kawai a rayuwarsa kafin a aika shi Baharain mai hidima ga gwamnan Manzo na can. Amma Imam Ali (a.s) ya zauna da manzon rahama (s.a.w) shekaru 33, kuma shi ne ya fi kowa ilimi da ittifakin sahabbai da wannan al’ummar gaba daya. Amma sai gashi ba shi da hadisan da suka wuce guda dari biyar 500, â€کya’yansa (a.s) kuwa sai abin da hali ya yi. A yanzu kana tsammanin sun yi shiru ne sun kame bakunansu tsarkaka alhalin suna wasiyyansa ba su ce komai ba!

Hafiz Muhammad

Kammala gyarawa

01 /July/ 2009

 



back 1 2 3 4