Tattaunawa Ta Hudu



Halifa na uku: harhada dukkan kur’anan garuruwa da hada kira’o’insu bisa dogaro da mas’hafi daya, shi ya sama ake kiran Kur’ani da mus’hafin Usman; Maganganun suna da yawa amma mun takaita su.

Amma batun cewa imamai suna da karamomi irin na annabawa da ka yi nuni da shi a (Al- Kulaini. AL- KAAFI, p.231): Wannan haka yake ya inganta a wasu ruwayoyi, a matsayinsu na masu gadon dukkan abin da Annabi (s.a.w) ya bari.

Amma batun tsayuwar daular imamai a hannun Imam Mahadi (a.s) kamar yadda ka yi nuni da shi a (Al- Kulaini, AL- KAAFI, p.397) da batun cewa zasu yi mulki irin na alayen Dawud: Wannan ya inganta cewa Annabi (s.a.w) ya bayar da labarin yadda hukumar Imam Mahadi (a.s) zata kasance, domin kada ta zo mutane su sha mamaki. Ka sani babu abin da Annabi (s.a.w) ya boye wa wannan al’ummar domin kada ta sami rudewa. Ya rage wa al’ummar ta karba ko ta ki karba.

Ka sani Dawud da Sulaiman (a.s) sun yi hukunci da iliminsu ne, kuma Allah ya ba wa Imam Mahadi (a.s) wannan ikon kamar yadda Annabi (s.a.w) ya isar mana. Ka nemin littafinmu na “Shi’anci da Duniyar Gobeâ€‌ domin karin bayani kan gwamnatin Imam Mahadi (a.s).

Amma batun cewa abin da imamai suke da shi, shi ne kawai yake gaskiya kamar yadda ka yi nuni da shi a (Al- Kulaini, AL- KAAFI, p.399): Wannan ya gabata kan bahasin jama’ar da take kan abin da Annabi (s.a.w) ya bari da take kunshe cikin wadanda suka yi riko da wasiyyarsa ta bin Kur’ani da Ahlul Bait (a.s).

Sannan kuma kai ma mai saba wa mazhabar Ahlul Baiti (a.s) kana ganin duk wata mazhaba ba ta ka ba to barna ce kuma bata ce, ko kuma ba ta cika ba, wannan ya faru a tarihin kashe-kashe da haramta aure tsakanin Mu’utazila da Ahlul hadis, da kuma Ash’ariyya, haka nan ma tsakanin shafi’iyya da hanafiyya, da sauransu.

Sannan kuma mai son zuwa ga ilimi dole ne ya zo ta kofarsa, idan kuwa ya ki ba a la’akari da shi, kamar jami’a ce da kake da iliminta amma ba ka yi karatu a can ba, babu yadda za a ba ka sakamakon yin jami’a.

Sannan batun da kake yi na cewa duniya ta Imami (a.s) ce da ka yi nuni da shi a (Al- Kulaini. AL- KAAFI, p.407): Shin kana mamakin Allah ya ba wa imamai (a.s) wannan duniyar! Wannan abin mamaki ne daga gareka, domin kuwa mumini a aljannarsa zai iya gayyatar duk â€کyan aljanna walima, kuma aljannarsa ta ninninka wannan duniyar, don haka wannan kadan ne ma ga imamai (a.s) idan ka girmama abin.

Amma batun kore rashin imani da ubangijin da ya sanya halifa na farko a matsayin wasiyyin manzon Allah (s.a.w) da ka yi nuni da shi a (Anwar-ul-nomania, page #278): Wannan ma kamar maganar dazu ce da muka ce tana nufin Allah bai yi haka ba: kuma dukkan musulmi Sunna da Shi’a sun yi ittifaki a kan cewa Annabi (s.a.w) bai yi nadi ga Abubakar ba. Amma Imam Ali shi ne wanda al’umma ta tafi a kan halifancinsa da yi masa wasiyya, sai dai a zamunan baya an samu wasu suna neman tawilin wasiyyar dogaro da abin da ya faru a tarihi domin wanke wasu mutane ko kuma kariya ga mazhabarsu, sai suka shiga yi wa wannan wasiyoyyi tawilin da wata ma’ana daban saboda maslahar kansu ko ta mazhaba da sauransu, wasu suna cewa an yi wasiyya ga jagorancinsa bayan Annabi (s.a.w) bisa dogaro da ayoyi da ruwayoyin da mun yi bahasi kan wasu daga ciki abaya, kuma wannan shi ne abin da muka tabbatar a bahasosin baya, don haka wannan maganar ba tana nufin ba mu yi imani da Allah ba!

Amma mamakin da kake yi na zuwan annabawa (a.s) a bakin kofar Ali (a.s) da ka yi nuni da shi a (khalkat-e-norania, page #201, Talib Husain karpalwi): Ka sani Imam Ali (a.s) sakataren Annabi (s.a.w) ne kuma kofar birnin iliminsa, don haka ba mamaki domin sun taru suna masu nema a kofarsa domin dukkaninsu masu nema ne wajen Annabi (s.a.w). Hada da abin da ya tabbata na matsayin wasiyyan Annabi (s.a.w) kamar yadda ya gabata a bahasin malaman al’umma matsu matsayin annabawa Banu Isra’ila.



back 1 2 3 4 next