Tattaunawa Ta Hudu



Maganar da ka kawo ta cewa; Shi'a sun ce Allah yana karay to wannan kage ne ka yi musu domin a shafin da ka yi nuni na (USOOL-E-KAAFI, shafi #328, Yakoob kulaini, bol 1): Babu wannan maganar. Shi'a ba su ce Allah yana karya ko kurakurai ba, idan kana ganin cewa ba ka fahimta ba ne, ko kuma wadanda suka ba ka wannan ba su gane ba ne, to a shafi na 327 an yi maganar da aka murguda ta kamar haka: (duk da kai ka yi nuni da ita ne a 328):

Daga Ali dan Muhammad… ...haka ne Ya Aba Hashim, Allah ya yi bada’i game da (al’amarin) abu Muhammad bayan abu ja’afar da abin da ba a san shi ba dacan gareshi, kamar yadda ya yi bada’i game da al’amarin Musa (a.s) bayan mutuwar Isma’il na abin da aka bayyanar da al’amarinsa da shi…

Sannan a kasan wannan ruwaya an yi mata sharhi da cewa: Al’bada'u da fataha da madda shi ne bayyanar abu bayan boyuwa kuma wannan bai halatta ba ga Allah madaukaki, abin da ake nufi da shi a nan shi ne; zartarwa da hukuntawa, kuma… abin da yake nufi shi ne: Allah madaukaki ya zartar da al’amarinsa kan al’amarin abu Muhammad (a.s) bayan mutuwar abu ja’afar (a.s) da abin da dacan bai kasance sananne ba gun jama’a game da abu Muhammad (a.s) wato; Imamanci da halifanci (gareshi) …

Idan aka duba zaka ga ya yi hannun riga da abin da aka fassara aka kaga kan Shi'a.

Ina ganin ba ka da bakin magana game da tsarkake Allah gun Shi'a domin sun yi fintinkau kan sauran mazhabobi wajen siffanta Allah madaukaki da siffofin kamala, alhalin jagoranku Harrani yana ganin Allah yana sauka daga sama ya koma kamar yadda yake hawa kan mimbari yana saukowa, kuma kuka siffanta Ubangijinku da wani saurayi ne mai dunkulallen gashi. Mai sanye da takalma biyu na zinare, mai hawa karaga har tana kara saboda nauyinsa, kuma mala’iku suna dauke da ita masu siffofin daban-daban har da ta dabba. Mai sanya kafarsa a wuta, wanda zai halaka ta yadda babu wani abu nasa da zai tsira daga halaka sai fuska. Mai kama da Annabi Adam (a.s), Mai bude kwaurinsa ana gani. Da sauran akidojin da suka shigo daga Ahlul Kitabi ko ta hanyar rashin mayar da muhkama zuwa ga mutashabiha, kuma kuka dauka kuna masu riko da su riko mai tsanani. Ina ganin masu irin wannan miki da ba zai warku ba, ba su da wani baki da ya rage da zasu bude domin kage ga masu akida sahihiya game da Allah (S.W.T).

Amma abin da ka yi nuni da shi a (Usul Kafi- Babul bad'a - Al- Kafi Bol- 1 -P283 India Ed.): Ma’anar bada' ta rigaya a sama ka duba, Wannan shi ne Shi'a suke nufi.

Amma abin da ka yi nuni da shi na littafin (Kashful Asraar - 107 - Khomeni..) Ban samu duba Kashful Asrar ba, amma idan ka samu irin wannan maganar; ka sani tana komawa ne ga tarihi da darussansa, kuma ba komai take nufi ba sai cewa; Ubangiji ba ya umarni da mummuna, domin ya barranta daga aikata munanan ayyuka kamar kashe bayi na gari, da kebance dukiyar al’umma ga wasu jama’a banda saura, da makamancin hakan. Wato: Allah ba ya bayar da umarnin kashe salihan bayinsa kamar yadda a wadancan lokuta aka kashe jikokin Annabi (a.s) da sahabban manzon Allah masu daraja. Idan ka ga magana mai kama da hakan, to Imam Khomaini ba yana nufin ba ma bauta wa Ubangiji ba ne, ka gane!

Amma batun da ka yi nuni da shi na cewa; imamai sun san ilimin komai kamar yadda ka yi nuni da shi a (Al- Kulaini. AL- KAAFI, p.255): Wannan tsohuwar shubuha ce da Imam Bakir (a.s) ya ba wa wani amsa akai da cewa: Shin Allah zai iya ba wa sauro wannan ilimin, mutumin ya ce haka ne, sai Imam (a.s) ya nuna masa cewa to me yake mamaki idan Allah (S.W.T) ya bayar da shi ga Annabi (s.a.w) da Alayensa (a.s).

Ka sani al’ummar musulmi sun ruwaito cewa; malaman al’ummata sun fi (ko kuma kamar) annabawan Banu Isra’il suke. Har ma wani malami a wani tafsiri nasa na ji ya fadi hakan sai ya yi murmushi wato; shi ne ya fi Annabi Isa da Musa da Yahaya da sauran annabawan Banu Isra’il (a.s). Idan kun fassara da malamanku to ina ganin matsayin kuma wasiyyan Annabi (s.a.w) da Allah ya ba su ilimi, ina kuma ga matsayin wasiyyinsa Imam Ali (a.s) wanda yake kofar iliminsa gaba daya!.

Ka sani ana magana ne kan abin da Allah ya bayar, ba haka nan ne dakansu suka sani ba.



1 2 3 4 next