Matasa Da Rayuwa



Haka kuma manomin da ya mallaki wata gona, ba ya hada kai da sauran manoma wajen samar da ruwan da za su yi amfani da shi a gonakin nasu matukar dai gonarsa ta samu ruwan.

Irin wadannan mutane ba sa dubin lamurra da kuma matsaloli face in suna da manufa da maslaha a cikinsu.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi bayani kan wannan matsala ta zamantakewa mai matukar muhimmanci, da kuma kan wannan son kai wanda yake matukar cutar da maslahohin al'umma. Inda yake ce wa:

"Babu wanda zai yi imani daga cikinku (musulmai) har sai ya so wa dan'uwansa abin da yake so wa kansa na alheri([3])".

Ta haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya hada tsakanin tunani kan maslahohin al'umma da kuma fita daga son kai na mutum guda. Don mutum ma'abucin son kai wanda ba ya tunanin maslahohin al'umma, ba mumini ne na gaskiya ba. Kana kuma duk wanda ba ya tunanin maslahar sauran mutane, to babu wanda zai yi tunanin maslaharsa....to hakan kuwa zai kasance babbar kafar ungulu ga hadin kan al'umma da kuma ci gabanta.

Matukar dai ingantaccen shu'urin taimakekke-niya bai tabbata ga mutum da al'umma ba, kana kuma matukar babu wasu dokokin da za su kiyaye maslahohin mutum da na al'umma.... to ba makawa al'umma za su zamanto cikin rashin tsari da son zuciya, kana kuma da yawa daga cikin mutane za su kasance cikin wahalhalu. Daga nan kuma sai masu karfi su samu daman cutar da marasa karfi da kuma takura masu rayuwa....

Hakika shu'urin taimakekkeniya da kuma na kyawawan dabi'u da suke tare da mu, bugu da kari kan ka'idoji na Ubangiji madaukaka, suna kiranmu zuwa ga kiyaye maslahohin al'umma, kamar yadda kuma suke kiranmu zuwa ga kula da maslahohin da suka kebanta gare mu. Kuma a lokuta da dama maslahohin mutum guda sukan cutar da maslahohin al'umma, don haka ya zama wajibi mu nesance su.

A matsayin misali, lalatawa da kuma kara kudi a kan takardun kudi (rasidin kudi) yakan samar da makudan kudade ga masu wannan mummunan aiki, sai dai kuma hakan yakan haifar da mummunan gibi ga tattalin arzikin al'umma. To don haka ne ma dokokin Musulunci suka haramta wannan aiki da kuma hukumta masu yin sa.

To amma cikin ayyukan tsarkakakkun mutane muna iya ganin daidaituwa kan maslahar mutum shi kadai da kuma ta al'umma....

Daga cikin irin wadannan kyawawan ayyuka shi ne abin da aka ruwaito daga Shugaban musulmi, Abu Abdullah, Ja'afar bin Muhammad al-Sadik (a.s.). An ruwaito daya daga cikin sahabbansa (sunansa Mu'attab) wanda shi ne mai kula da harkokin cikin gidansa yana cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next