Matasa Da Rayuwa



Rayuwar dan'Adam ita ce ayyukan jiki, tunani da na ruhi da mutum yake aikatawa tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Kuma ta hakan ne yake tabbatar da samuwarsa da kuma cika zati, ruhi da kuma yanayinsa....

Yakan cika hakan ne kuwa ta hanyar abubuwan da ya mallaka, na daga rayuwa, hankali, karfin yanayin abubuwan da suke kewaye da shi, jin dadi da kuma ciwo, gano abubuwan halitta da hankalinsa yake yi....da dai sauransu.

Hakika mun kasance muna ci da sha, muna sa tufafi, muna wasa da jin dadin kyawawan abubuwa, muna yin jima'i, muna jin soyayya da kiyayya, farin ciki da bakin ciki, jin dadi da kuma jin zafi, muna dariya da kuka, mukan yanke kauna kan al'amurra da kuma burace-burace....

Sannan kuma mukan yi tunani da kuma kirkiro abubuwa, mukan gano sabbin abubuwa sannan kuma mu sanya wasu, kuma mukan yi bayanin abubuwan da suke damunmu ta hanyar magana, rubutu, wake, farin ciki da kuma bakin ciki.

Kana kuma mukan gano abubuwan da suka fita daga wannan duniya tamu ta hanyar hankali da kuma tunaninmu, muna masu tunanin girmansu da kuma yadda aka samar da su. Kuma mukan gano ka'idojin samuwa da kuma Wanda Ya samar da ita....

Hakika mun kasance muna tunani, muna ji, muna aiki, kuma mukan tsara rayuwarmu da tunani da kuma shu'urinmu, da kuma ayyukan da suke fitowa daga gare mu.....

Mu mun kasance jiki, ruhi da kuma hankali ne wadanda aka arzurta mu da su. Mu muke sana'anta rayuwarmu kamar yadda mai zane yake zana hoto.... rayuwar kowanne daga cikinmu hotonsa ne na zati, to a cikinmu wane ne yake so hotonsa (zatinsa) ya kasance abin kyama....

Hakika rayuwa ba wai jin dadi da annashuwa ba ce kawai, face dai tana hade da abubuwan bakin ciki da dacin rai kuma. Ita ba wai kawai sakaka take ba.... face dai ita nauyi ce....nauyi ce a gaban Allah Ta'ala, nauyi ce a gaban al'umma da kuma mutanen da muke rayuwa da su. Sannan kuma nauyi ce a gaban dokoki, mutumci da kuma samuwa.

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

"Sa'an nan lalle ne Muna tambayar wadanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Muna tambayar Manzannin".(Surar A'araf,7: 6)

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:"Dukkanku makiwata ne, kuma dukkanku abin tambaya ne kan abubuwan da aka ba ku kiwonsu".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next