Matasa Da Rayuwa



Kamar yadda ilimi kuma ya ba da gagarumar gudummawa wajen daga martabar fahimtar dan'-Adam ga rayuwa, ci gabantar da hanyoyin kerekere da kuma tsara rayuwar al'umma. Ya taimaka wajen biyan bukatun dan'Adam da kuma samo sabbin hanyoyi magance matsalolin rayuwa.

Babu makawa, kirkiro wutan lantarki, man fetur, radiyo da talabijin, hanyoyi rubutu da buge-buge da kuma na safara da dai sauransu, sun bude wa dan'-Adam sabuwar fahimta ta rayuwa. Kuma sanannen abu ne cewa a duk lokacin da fahimta da masani-yarmu da rayuwa ta karu, fahimtarmu ga addini da ma'anar imani ma za ta karu. Don haka ilimi abu ne da yake kira zuwa ga imani kana kuma abokin zaman rayuwa.

3.  Hankali da kwarewa: Hankali shi ne fitilar dan'Adam a rayuwarsa, don haka a duk lokacin da mutum ya yi amfani da hankali kamar yadda ya dace, to ba makawa zai kai shi ga alheri da kuma tsamar da shi daga halaka, bata da kuma nadama.

Dan'Adam ya kasance mai aikata abubuwa da daman gaske a rayuwarsa, don haka ya mallaki kwarewa daban-daban a rayuwartasa. A saboda haka, ya za ma dole ya yi amfani da wannan kwarewa da ya samu wajen kyautata rayuwarsa, kamar yadda kuma yake wajibi ya yi amfani da kwarewar sauran mutane a dukkan bangarori na rayuwarsa shi kadai, da na aure, tattalin arziki, siyasa, wayewa da dai sauransu.

A saboda haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya yi mana umurni da amfani da hankali da kuma kwarewar al'umman da suka wuce. Don kuwa kwarewar mutane da kuma abubuwan da suka faru a baya na tarihi, bugu da kari kan abubuwan da hankali mutum ya kirkiro na ilimi, hikima da dai sauransu, abubuwa ne da suke taimakawa, nesa ba kusa ba, wajen tabbatar da kyakkyawar rayuwa da kuma bube sabbin kofofin fahimtarta.

Don haka ne Alkur'ani mai girma yake shiryar da mu zuwa ga amfani da kwarewar al'ummomi da kuma daidaikun mutane bugu da kari kan tunani da kuma amfani da hankali. Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa:

"Kuma Shi ne Wanda Ya shimfida kasa, kuma Ya sanya duwatsu da koguna a cikinta, kuma daga dukkan 'ya'yan itace Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yana sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, hakika akwai ayoyi ga mutane wakanda suke yin tunani". (Surar Ra'ad, 13: 3)

"Kuma ba Mu aika ba a gabanninka face mazaje, Muna wahayi zuwa gare su, daga mutanen kauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin kasa ba, domin su duba yadda karshen wadanda suka kasance daga gabanninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lahira shi ne mafi alheri ga wadanda suka yi takawa, shin fa, ba ku hankalta? Har a lokacin da Manzanni suka yanke tsammani, kuma suka yi zaton cewa an jingina su ga karya, sai taimakonMu ya je musu, sa'an nan Mu tserar da wanda Muke so, kuma ba a mayar da azabarMu daga mutane masu laifi. Lalle ne, hakika, abin kula ya kasance a cikin kissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani kirkiran labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukkan abubuwa, da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani". (Surar Yusuf, 12: 109-111)

An ruwaito Imam Ali (a.s.) yayin da yake huduba ga dansa Imam Hasan (a.s.), yana shawartarsa da yin amfani da kwarewar sauran mutane, inda yake ce masa:

".....don ka shirya wa karbar kwarewar wasunka ta hanyar tunaninka, don ka tsira daga fadawa cikin abubuwan da suka fada. Ta haka sai ka tsere wa wahalar nemansa da kuma wahalar gwaji. Don haka, sai ka ga ka san abin da muka gani kana muka shaida da ma abubuwan da suka
bayyana maka wadanda watakila mu ba mu riske su ba....." ([6]).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next