Ajali KoWa'adi



Kamar yadda hikayar Abut Tufail take nuna mana yadda imam Ali (a.s) ya sayi wani tufafi da ya kayatar da shi, amma sai ya yi sadaka da shi yana mai kafa hujja da fadin Manzon Allah (s.a.w) cewa;  â€œDuk wanda ya fifita wasu a kansa, to Allah zai fifita aljanna gareshi ranar kiyama[13], al'amarin da yake nuna mana cewa; mafificiyar aljanna ta wadanda suke fifita wasu a kansu ne.

Haka nan idan mun koma zamu ga fadin Imam sadik (a.s) jikan Sayyida Zahara (a.s) yana mai nakalto labarun sadaukarwar da ta yi ta hanyar fifita wasu a kanta yana mai cewa: “Ya kasance akwai wani sha’ir gun Fadima (a.s) sai ta yi tuwo da shi, yayin da ya dahu sai suka sanya shi a gabansu, sai wani miskini ya zo, sai miskinin ya ce: Allah ya yi muku rahama, sai Ali (a.s) ya tashi ya ba shi sulusi –wato; kaso daya cikin uku- ba a dade ba sai ga wani maraya, sai marayan ya ce: Allah ya yi muku rahama, sai Ali (a.s) ya tashi ya ba shi sulusi. Sannan sai wani ribatacce ya zo, sai ribataccen ya ce: Allah ya yi muku rahama, sai Ali (a.s) ya tashi ya ba shi ragowar sulusin, ba su dandani wannan abincin ba. Sai Allah madaukaki ya saukar da ayar nan a kansu, kuma wannan aya tana aiki kan kowane mumini da ya yi hakan[14]. Wannan lamarin mai nuna kololuwar sadaukarwa da fifita wasu a kan kawukanmu yana nuna mana girman wannan gida da yake karkashin tarbiyyar Annabi (s.a.w) kuma har ila-yau yana nuna mana cewa; wannan al'amari bai kebanta da wannan gida ba, wato; lamari ne wanda mu ma aka umarce mu da kamanta shi kamar yadda muke iya ganin karshen wannan ruwaya yana nuni da hakan.

Muna iya cewa; da za a ba wasu mutane wani abu don su raba a tsakaninsu, sai ya kasance dole ne daya ya fi yawa ko yaya ne, idan kana son ka nuna fifita zabin wasu a kanka to sai ka bari su fara zaba, idan kuwa kai ne mai rabawa sai ka bari su fara dauka, idan kuwa kai ne zaka ba su sai ka mika musu mafifici kuma mafi yawa a ganinka. Hafiz Muhammad Sa'id Kano, Cibiyar Al'adun Musulunci 2/13/2009

 


[1] Gurarul Hikam: 986.

[2] Gurarul Hikam: 606.

[3] Hashari: 9.

[4] Gurarul Hikam: 1705.

[5] Gurarul Hikam: 1148.

[6] Gurarul Hikam: 2888.

[7] Gurarul Hikam: 6342.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next