Ajali KoWa'adi



Ya zo cewa imam Ali (a.s) ya aika da wani gwamna Afrika, bayan wani lokaci sai ya aiko masa da wasika yana cewa dukiya ta yi yawa gun mu me zamu yi da ita? Sai imam Ali (a.s) ya ce masa ka ba wa talakawa ita domin su wadata, sai ya sake aiko da wata wasika wani lokaci zuwa ga imam (a.s) cewa talakawa sun wadatu kuma har yanzu akwai dukiya mai yawa me zamu yi da ita? Sai imam Ali (a.s) ya aiko masa da cewa ka aurar da gwagwarensu da wannan dukiya, sai ya aurar da gwagwarensu sannan sai ya aika da ragowar dukiya zuwa ga imam (a.s).

Haka ne yayin da tunanin Ali da aikin Ali ya yi hukunci da koyarwar Ali to al'umma zata rayu rayuwa mai dadi, domin aikinsa aikin Manzon Allah ne da ilimin da Allah da Manzonsa suka ba shi, kuma shi imam Ali shi tafarki ne madaidaici kuma hujjar Allah a kan mutane gaba daya da koyarwar da Annabi (s.a.w) ya yi wa al'ummarsa.

Kuma kamar yadda hukuma take daukar nauyin gina mutane su samu tsayuwa da kafafunsu haka nan ne su ma mutane aka karfafe su da idan ta samu matsalar tattalin arziki sai su agaza mata domin kada ta yi rauni ta rushe alhalin da ita ne tsarin al'umma yake kafuwa ya tasyu. Wani lokacin mukan ji maganar rage ma'aikata daga wata kasa ko gwamnti ko kampani ba tare da an maye musu da wata sana'a ko wani aiki ko kuma kasuwanci ba, wannan wani abu ne mai matukar muni matuka, musulunci bai yarda da hakan ba, domin wannan tozarta dan Adam ne, sannan kuma a bisa tsrin da Obama yake yi wa Amurka a kwanan nan sai na gani jiya ta intanet cewa; zasu kirkiro aiki na dan lokaci -part time- domin tallabar rashin aikin yi da ya fara yawa a kasar, da sauran matakai da kasashe sukan dauka.

A bisa hakika tsarin karfafa dogaro da kai wani abu ne daga sirrin tattalin arzikin al'umma da walwalarsu, sannan kuma jikan Imam Ali (a.s) wato Imam sadik (a.s) ya yi nuni da hakan a yayin da Ammarus Sabadi ya tambaye shi cewa; "Mutumin da yake kasuwanci amma idan ya yi aikin kwadago sai a ba shi abin da yake samu a kasuwanci, sai ya ce: kada ya yi aikin kwadago, sai dai ya nemi Allah madaukaki ya arzuta shi ya yi kasuwanci, domin idan ya yi kwadago sai ya hana kansa arzikin"[4].

Sannan kuma an hana mutum ya karbi aiki bai yi komai ba sai ya ba wa wani kuma ya ci riba a kai, don haka idan yana son ya samu riba a kai dole ne shi ma ya kasance ya yi wani abu ko yaya ne a cikin aikin kamar yadda zamu iya ganin hakan a koyarwar alayen Annabi (s.a.w) yayin da aka tambayi dayansu (a.s) game da mutumin da yake karbar aiki kuma sai ya ba wa wani ya yi shin zai iya cin riba a cikinsa, sai ya ce: a'a, sai dai idan ya yi wani aiki a cikinsa shi ma[5].

Kuma an tsananta matuka kan wanda yake zaluntar dan aiki kuma ya hana shi ladan aikinsa kamar yadda wata ruwaya daga fiyayyan halitta take cewa; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya zalunci dan kwadago to Allah zai shafe aikinsa kuma ya haramta masa kanshin aljanna, kuma hakika kanshinta ana jin sa tun daga nisan tafiyar shekaru dari biyar"[6]. Da fadinsa cewa; "Zaluntar dan aiki hakkinsa yana daga manyan zunubai[7].

Haka nan an hana jinkirta ba wa dan aiki ladansa kamar yadda fiyayyen manzanni yake cewa: "Ku ba wa dan aiki ladansa kafin guminsa ya bushe, kuma ku sanar da shi ladansa yana cikin aikinsa"[8]. Amma game da yarjejeniya kuwa to dalibinsa Imam Ali (a.s) yana cewa ne: "Manzon Allah ya hana daukar mutum aiki har sai an sanar da shi ladan aikinsa"[9].

Amma tsarin albashi musulunci yana zuwa ga cewa; a ba wa kowane mutum abin da zai ishe shi rayuwa daidai gwargwadon halin da yake ciki da kuma nauyin da yake kansa, wannan kuma tsari ne da duk fadin duniya tun bayan Manzon Allah da hukumar Imam Ali ba a sake samun wanda ya yi aiki da wannan tsarin ba a hukumance. Hafiz Muhammad Sa'id Kano, Cibiyar Al'adun Musulunci 2/13/2009

 


[1] Zukhrufi: 32.

[2] Kasas: 26.

[3] Wasa'ilus shi'a: 13/244/3.

[4] Alkafi: 5/90/3.

[5] Alkafi: 5/273/3.

[6] Amalis saduk: 347/1.

[7]  Albihar: 103/170/27.

[8] Kanzul ummal: 9126.

[9] Alfakih: 4/10/4968.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10