MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).



Irin wannan fayyacewa tana karfafa ruhin buri a zukatan da suke rayuwa cikin yanayin zalunci da danniya, ta kan wanzar da tunkudawa zuwa ga manufar da ake bida wacce ita ce kafa adalin tsari na musulunci.

 Shekara goma sha tara na imamanci Imam Bakir (a.s) aka yi aiki na gudana bisa wannan mikakken layi mabayyani. Shekara goma sha tara na koyarwa kan manufar gini da dabarun kare kai da tsare-tsare da kare haraka da takiyya da karfafa ruhin sa-rai da sauransu.

Shekara goma sha tara ana gudanar da wannan tafiya mai tattare da kaya da munin hanya wanda yake bukatar kokari da ijtihadi mai yawa. Lokacin da wadannan shekaru suka kawo karshe, ranar rayuwarsa mai albarka ta zo faduwa, sai abokan gabansa suka yi ajiyar zuciya domin a zatonsu idan wannan jagora mai shiryarwa ya tafi za su huta da tushen farkarwa da izawa wanda ya dade yana hana su hutu da barci.

Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kuma sa wannan dama ta kubuce  musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan sa Sadik(a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri  ne mai gwanin ban  sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su  a zangon zamani  wanda ya kebance shi . A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s)  ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki  na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minan”.[17]  ..Ita wannan ruwaya , wadanda suka yi bincike kan rayuwar Imam Bakir basu dube ta da kyau ba kuma sun gafala ga barin ma`anoni masu girma wadanda ta kunsa.  Imam ya rasu ya bar dirhami dari takwas, yayi umarni da aware wani abu daga ciki a baiwa masu kukan mutuwarsa a Mina. Yin kukan rasuwar Imam a Mina ya kunshi ma`ana mai girma .Lallai shi aiki ne na raya tushen nan da ya kasance a ko yaushe yana  watsa hasken wayar da kai da farkarwa da kuma sanya ruhin kamuji da gwagwarmaya.

Zaben Mina kuwa yana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda  haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kuma sami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za su ce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da ya sa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shi ko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Da dai sauran su. Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin.

 Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye.

Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya,  a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’an nan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanya wa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria.


[1] Dubi  Ajwibatu masa’il jarullah / Sayyid  Sharafuddin / sh 59-60.

[2] Tuhaful Ukulana ali rasul /sh  272-277.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next