MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).



MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).

Bayan waki’ar Ashura Imam Zainul Abidin Ali bin Hussain (a.s) yana da zabi biyu,su ne:- Imma dai ya sa sahabbansa shiga wata harka sakamakon motsawar rai da tausayi ya jefa su cikin wani garaje wanda wutarsa ba badewa ruruwarta zai yi sanyi, ya bice (saboda ba su da sifofin masu jihadi), sannan daga bisani a bar wa Banu Umayya filin ci gaba da danniya da babakere kan makomar al’umma wajen tunani da siyasa, ko kuma ya rinjayi tausayi da biri---bokon fushi da tunzura, kana ya tanadi share fage wa wani babban aiki wanda zai kai ga dawo da rayuwa irin ta musulunci. Bukatun share fagen su ne tunani mai jagorantan aiki da samar da wata salihar jama’a domin ta zama iri ga juyi da sauyi nan gaba, ya kuma nisanci idanun Banu Umayya, ya ci gaba da aiki haikan wanda manufarsa ita ce gina tunani da kuma dai-daikun matane. Da haka ne zai yi tafiya mai yawa kan manufar kira, Imamin da zai gaje shi kuwa zai zama ya kara kusanto cimma manufar.

To wani zabi ko hanya zai fifita? Ko shaka babu, hanyar farko ita ce ta sadaukarwa da daukar fansa, sai dai jagoran da yake shiri saboda harakar tarihi da kuma zamanin da tsawonsa ya zarce tsawon rayuwar Imam nesa ba kusa ba, sadaukar da rayuwarsa kawai ba ta isa. Dole ne ya zama mai zurfin 14tunani, mai yalwar zuciya, mai hangen nesa mai dabara da hikima cikin al’amuransa. Wadannan sharrudda sun wajabtawa Imam zabar hanya ta biyun.

14  Imam Ali bin Hussain (a.s) ya zabi ta biyun duk da dauriya da wahal-halu da juriya da kuncin da ke tattare da wannan hanya.Ya ba da rayuwarsa kan wannan tafarki (a shekara ta 95 bayan hijira).

Imam Sadik (a.s) ya sifanta mana yanayin da imami na hudu ya rayu a kai da kuma rawar da ya taka ta jagaba, ya ce:-“Bayan Imam Hussain (a.s) mutane sun juya baya banda mutum uku, Khalid Alkabuli da Yahya ibn Ummi Dawil da Jubair bin Mud’im. Daga bisani sai mutane suka dawo suka yawaita. Yahaya Ibn Ummi Dawil ya kan shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:- “Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu …..”(Mumtahina aya 4.)

Wannan riwaya tana nuna halin da al’ummar musulmi take ciki bayanan kashe Imam Hussaini (a.s). yanayi ne mai ban tsoro, na fatattaka da raunin zuciya wanda ya game al’ummar musulunci a lokacin da waccan waki’ar ta faru, abin takaicinda ya auku a Karbala al’ummar har ma shi’ar Ahlulbaiti, ya fadi warwas. Wadannan  ‘yan shi’an da suka gamsu da alaka da Imamai a zuci kawai amma a aikace sun karkata wa duniya da jin dadinta da kelkelinta. Irin wadannan suna nantsawon tarihi hatta a zamanin nan namu, ba kuma kadan suke ba.

Daga cikin dubban masu da’awar shi’a a zamanin Imam Sajjad (a.s) mutum uku kadai suka rage bisa tafarki, mutum uku ne razanarwar Ummayawa da kamun da hukuma ke yiwa mutane bai sa su firgita ba, kuma son kubuta daga neman zaman lafiya bai girgiza azamarsu ba. Sun ci gaba da amsa kira da fama bisa wannan tafarki da  cikakkiyar azama da tabbata. Guguwar da ta kwashi al’umma tamkar wasu zauna gari-banza suka kuma bi manufar azzalumar hukuma, ba ta kwashi wadannan mutanen ba. Dayansu watau Yahya ibn Ummi Dawil ya kan mike a masallacin Madina ya yi huduba wa masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti yana mai baiyana bara’a gare su, kamar yanda ya gabata, yana kafa hujja da abin da Annabi Ibrahim (a.s) da mabiyansa suka fada wa masu bijirewan zamaninsa “ Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu.” Ibn Ummi Dawil ya karanta wannan aya mai girma gaba ga masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti ne domin ya baiyana cikakken rabewa tsakanin sassan guda biyu:sashen ma’abota sako masu lizimta da kuma sashen masu zaman dirshan da sassautowa zuwa burace-buracen da basu taka kara sun karya ba da kuma rudi da abin duniya mara kima. Wannan rabewa tana tare da dukkanin kiraye-kirayen addini. Imam Sadik ya sifanta wannan rabewa na sassan biyu da cewa:- (Wanda ba ya tare da mu, to yana adawa da mu). Watau wanda duk ba ya sashen tauhidi to yana bangaren dagutu, babu wata ma’ana ga zama dan ba ruwanmu domin kuwa ba wani yankin tsaka-tsaki.

Wannan musulmi mai wilayar gaskiya ga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) watau Yahaya bn Ummi Dawil, da wannan kiran nasa ya baiyana rabewa tsakanin masu gamsuwa da wilayar da ta takaita ga motsin rai alhali suna kwanto cikin abubuwan amfanin kansu, suna nitse cikin dattin kuntataccen zatinsu,da masu lizimtar Imam a tunani da kuma aiki. Bisa dabi’a wannan rabewa tana nufin wuce gaban cewa batattun masu rinjaye su janye mutum, amma ba tana nufin watsi da batattun ba. Da wannan fikira ne wannan salihar jama’a ta fuskanci aikin tsamar da duk wani mai iya ‘yantuwa daga wahala da kangi. Sannu a hankali, sai wannan jama’a mai jihadi da dauriya ta yawaita, kuma da wannan ne Imam Sadik (a.s) yake ishara yayin da ya  ce: “…… daga bisani sai mutane suka dawo suka yi yawa” Ta haka ne Imam Sajjad  ya ci gaba da ba da   himma kan  aikinsa. Wannan  aikin  da

  wadansu matsayin da Imam ya dauka, wadanda za mu ambato nan gaba yana daga cikin abubuwan da suka janyo shahadarsa da ta wasu daga mukarrabansa.

Ban ga wani bayyanannen sa-in-sa da hukuma a rayuwar Imam Sajjad (a.s) ba. Kamar yanda muka ambata, hakan shi ne abin da ya dace da hikima.  Domin da ya dauki irin matsayin da muke gani a rayuwar Imam Musa ibn Ja’afar (a.s) da imaman da suka biyo bayansa dangane da mahukuntan zamaninsa da bai iya ciyar da aikin sauyi gaba har ya samar wa Imam Baqir (a.s) damar mayalwacin aiki ba. Da yayi haka da an hallaka shi da salihar jama’ar da take tare da shi.

Ba mu iya tsinkayar ra’ayin Imam na hakika dangane da masu iko illa nadiran, ko a nan ma bai kai matsayin fito-na fito ba. Iyaka dai yana tabbatar da wani matsayi wa tahiri yana kuma fadakar da jama’ar da take kusa da shi kan abin da ya shafi aikinsa da harakarsa gwargwado. Irin wadancan matsayi sun hada da takardar suka mai tsanani da Imam da aikewa wani malami mai alakar kut-da-kut  da Banu Umayya watau Muhammad bin Shihab Azzuhri. Muna iya fahimta a takardar cewa Imam yana magana ne da tsararraki masu zuwa tsawon zamani, ba da Azzuhri ba saboda Azzuhri ba mutumin da zai iya yantuwa daga kangin liyafar Banu Umayya da wasanninsu da mukamansu da al’farmarsu ba ne.Tahiri ya tabbatar da hakan, domin kuwa Azzuhri ya gama rayuwarsa ne cikinsa hidimarsu tare da rubuta littafi da kuma kirkirar hadisai saboda neman kusanci da su [1]



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next