MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).



ZARCEWAR IRIN RAYUWAR  IMAM SAJJAD.

An wayi gari mabiya Ahlulbaiti sun zama wata jama’a fitacciya mai dogaro da kai, kirar Ahlulbhaiti kuwa wacce ta dan tsaya ta kuma boye bayan shamaki mai kauri a dalilin waki’ar Karbala da waki’o’in da aka zubar da jini da suka biyo bayanta kamar waki’ar  Harra da tawayen Tawwabun  wadanda fir’aunancin Umayyawa ya haifar ta zama samamma ce mai yaduwa ta kuma bayyana cikin da yawa daga yankunan daular musulunci, musamman a Iraki da Hijaz da Kurasan. Tare da wannan samuwa, ta haifar da tsari na tunani da kuma aiki.   Kwanakin da Imam Sajjad (a.s) ya sifanta da cewa :  “ mabiyansa ba su wuce ashirin ba” sun kau sai ga Imam Bakir (a.s) yana shigo masallacin Ma’aiki (s.a.w.) a Madina jama’a mai yawa daga mutanen Kurasan da sauran lardunan duniyar musulmi suna kewaye shi, suna tambayarsa hukuncin musulunci kan al’amuran rayuwa dabam-dabam. Mutane kamarsu Dawus Yamani da Katada ibn Da’ama da Abu Hanifa da wadansu daga shugabannin mazhabobin fikihu suna tahowa domin su sha daga ilmin Imam ko kuma su yi jayayya da shi kan al’amura dabam-dabam.

 A wannan zamanin an sami mawaka masu kare mazhabin Ahlulbaiti da bayyana manufofinsa. Daga cikinsu akwai Kumait wanda ya sauwara mafi kyan surar da kwararru ke zaiyanawa a kan wilaya ta tunani da kauna ga mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kasidarsa mai suna hashimiyya. Hakika harsuna basu gushe ba suna nakaltar wadannan gwalagwalan wake yayin da zukata suke kiyaye su.

Ta wata fuska kuwa halifofin Banu Marwana cikin wannan dan lokacin, sun sami wata natsuwa da tabbatar mulki bayan Abdulimalik ibn Marwan (m.86H) cikin shekara ashirin da ya yi mulki, ya murkushe dukkan masu ja da mulkinsu, kuma yiwuwa  cewa sansancewar aminci da natsuwa da halifofin Marwaniyawa na wannan lokacin ya samo asali ne daga kasancewar sun sami mulki tamkar wata ganima, sabanin magabatansu wadanda suka yi jan aiki kafin su kai ga mulki. Wannan natsuwa ta sa halifofin baya shagaltuwa da wasanni da jin dadin duniya, tadodin da galibi suke tare da mai jin iko da alfarma da kuma girma. Ko mene ne ma dai, damuwar halifofin Banu Marwan da lamarin mazhabin Ahlulbaiti ta ragu a wancan lokacin, sai ga Imam da mabiyansa suna rayuwa kusan a ce cikin aminci daga farautar hukuma. Bisa dabi’a, Imam zai ci tafiya mai yawa kan tafarkin tabbatar da manufofin mazhabin Ahlulbaiti a irin wannan yanayi ya kuma kai shi’anci wani sabon zango. Wannan kuwa shi ne ya bambanta rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta saura. Ana iya takaita abin da rayuwar Imam, cikin shekaru goma sha tara na imamancinsa (95-144H) ta kunsa kamar haka:-

Yayin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya zo cikawa ya yi wasici da cewa dansa Muhammadu ya zama Imami bayansa, gaba ga sauran ‘ya’yansa da danginsa, ya kuma ba shi wani akwati. Riwayoyi sun ce akwatin cike yake da ilmi, sun kuma ce akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a) a ciki. Imam Sajjad (a.s) ya ce:- “Ya kai Muhammadu wannana akwati ka tafi da shi gidanka” Sannan ya ce:- “Hakika babu dinari ko dirhami a ciki, sai dai cike yake da ilmi”[4]

La’alla wannan akwati wata alama ce mai muna cewa Imam Sajjad ya mikawa dansa  jagorancin tunani da ilmi (tunda yana cike da ilmi) ya kuma  mika masa nauyin jagorancin juyi (tun da yana kunshe da makamin Annabi (s.a.w.a)).

Gami da farawar Imam da mabiyansa faffadan aikinsu na yada koyarwar Ahlubaiti (a.s) farfajiyar yaduwar kiran ta kara fadi, ta sami sababbin fuskoki wadanda suka zarce fagenta daya gabata a Madina da Kufa. Sai ga ta tana yaduwa cikin  larduna manisanta daga cibiyar mulkin Umayyawa. Lardin Kurasan na daga cikin wadancan wurare kamar yanda riwayoyin tahiri suka nuna.[5]

Yanayin tunani da zamantakewa mai kaskanta mutane ya zaburar da Imam da mabiyansa wajen haraka mai dorewa ba tare da gajiya ko kosawa ba domin sauya wannan mummunan yanayi da tabbatar da  abinda Ubangiji ya wajabta na kawar da wannan baudiyar.

Suna ganin mafiya yawan mutane sun rusna wa gurbatanccen yanayin da Banu Umayya  suka yada, suka nitse cikin kazantar abin duniya iya wuya har suka wayi gari tamkar mahukuntan nasu,basu fahimtar zance, kunnensu bai jin nasiha. “Idan mum kira su ba sa amsa mana”.[6]

Ta wata fuska kuwa, Imam da jama’arsa suna ganin bincike-binciken fikihu da ilmul kalam da hadisi da tafsiri na karkata ne wajen dadada wa fir’aunancin Umayyawa da bin sonransu. Saboda haka duk hanyoyin dawowar jama’a kan katari da sun toshe, ba don zaburar mazhabin Ahlulbaiti wajen bayar da wajibinsa ba  idan kuwa muka kyale su ba za su shiriya ta hanyar waninmu ba[7]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next