MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).



Mazhabin Ahlulbaiti ya yi Allah wadai da malamai da mawaka da suka sayarda kansu. An yi wannan sukan ne saboda kokarin farkarda zukatan wadancan malaman ko kuma zukatan mabiyansu. Imam yana fadawa Kumait, sha’irin Ahlulbaiti, da lafazin suka:- yabon Abdulmalik kayi?

Ya ce:- Ban ce da shi ‘ya shugaban shiriya’ ba, abin da na ce shi ne ‘ya zaki’ zaki kuma kare ne, ‘ya rana’ rana kuwa jamadatu ce, ‘ya kogi’ kogi kuwa mataccen abu ne, ‘ya maciji’ maciji kuwa kwaro ne mai wari, ‘ya tsauni’ tsauni kuwa kurman dutse ne. Sai Imam ya yi murmushi. Kumait sai ya rera wannan baitin gaban Imam:-

 Zuciyar da so ya tsare ya aure?

     Ban da yaranta tasa har da guri,

Wannan mimiyar ta kafa mararraba tsakanin alkiblar Alawiyya  da ta Umawiyya a daraja da kuma halaye ta hanyar dawwamammar zaiyanawa mai kyan gaske.

Wata rana Ikrima almajirin ibn Abbas wanda yake sananne ne, mai matsayin ilmi a cikin al’ummar wancan zamanin ya je yin mukabala da Imam sai haibarsa da natsuwarsa da ruhinsa da tunaninsa suka kama Ikrima. Abin da kadai ya iya fada shi ne:- “Ya dan Manzon Allah hakika na zauna gaban Ibn Abbas da waninsa sau da yawa amma irin abin da ya same ni yanzu bai taba samu na ba”. Sai Imam ya amsa masa da cewa:- “(Kai kana gaba ga gidaje wadanda Allah ya yi wa daukaka kuma ake ambaton sunansa a cikinsu)[8]

Ta wandansu fuskoki daban na ayyukan mazhabin Ahlulbaiti a wannan zangon kuwa, akwai jerin zalunci da fir’aunanci da kisa da azabtarwa da kora, da suka kewaye Ahlulbaitin Manzon Allah da mabiyansu ba don komai ba sai domin kokarin da suke yi na iza matacciyar zuciyar mutane da girgiza rayukansu wadanda suka yi sanyi da zaburar da kwantacciyar azamarsu da shiryar  da su zuwa harakar juyi.

Alminhal bin Umar ya ruwaito cewa:-  “Na kasance ina zaune tare da Muhammad bn Ali Albakir  (a.s) sai wani mutum ya taho ya ce da shi: Yaya kuke?  Sai Imam Bakir(a.s) ya ce:- “Lokaci bai yi  ba da za ku  san yanda muke?  Misalinmu a wannan al’umma tamkar Bani Isr’a’ila ne a da,ana yanka ‘ya‘ya maza ana barin (raya )mata.  Ka saurara!  Lallai wadannan suna yanka ‘ya‘yanmu maza suna barin  ‘ya ‘yanmu mata. Larabawa sun yi da’awar  fifiko bisa baibayi. Sai baibayin suka ce: ‘Mene ne dalilin haka?’  Sai suka ce:  “Muhammadu balarare ne daga gare mu” Sai suka ce da su:  “Kun yi gaskiya.” Kuraishawa kuwa suka yi da’awar cewa suna da wani fifiko bisa sauran larabawa. Sai sauran larabawa  suka ce “Mene ne dalili?” Sai suka amsa da cewa:  ‘Muhammadu bakuraishe ne’. Suka ce da su: ‘Kun yi gaskiya’. Idan mutanen nan sun yi gaskiya, to muna da fifiko bisa mutane domin mu zuriyar Muhammadu ne, mutanen gidansa kuma makusantansa masu kebanta da shi, waninmu ba ya tarayya da mu a wannan” Sai mutumin ya ce da Imam;  “Wallahi ni ina son ku, ku Ahlulbait”. Sai ya ce da shi: “To ka dauki bala’i a matsayin riga, domin kuwa wallahi shi (bala’i) ya fi kusa da mu da kuma shi’armu bisa ga gudanar igiyar ruwa a cikin kwari. Da mu bala’i zai fara sanan  ku”[9]

Da ganin alamar cewa mutumin ya girgiza saboda zaburarwar da ya ji sai Imam ya yi maza ya zana  masa tafarkin kiran, ya fayyace.Shi dai tafarki ne wanda  aka shimfida shi da jini da kwalla, Imam kuwa shi ne madugun tafiyar, bala’i yana samunsa da farko  kafin ya kai ga shia’rsa.

A tsakanin shi’arsa alakar Imam tana da wadansu sifofi kebantattu. Za ka gan shi cikin mabiyansa tamkar yanda kwakwalwa take a tsakanin gabban jiki yana ciyar da ruhinsu yana karfafa masu haraka  da himma ba tare da yankewa ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next