Kaddara Da Hukuncin Allah



Saudayawa a hukuncin Allah ko kaddarawarsa a halittawarsa a harshen hausa a kan yi amfani da kowanne a mahallin kowanne musamman da yake mutane sun fi bayanin abin aka riga aka kammala shi, tayiwu a wasu wurare su yi amfani da wadannan kalmomi kan a bin da ba a kammala shi ba, kamar yadda wani zai ga mai babur yana gudu sabanin ka'ida kuma a can gaba ga wata mota ta gindaya zata tsallaka, sannan sai ya ji karar jan burkin mashin din nan da sauti mai karfi, sai ya ce; Allah ya kaddara! ko ya hukunta!: Yana mai nufin cewa; a bisa abin da ya auna kuma ya kiyasta akwai sharuddan yin hatsari da suka kammala da suka hada da gudun da ya wuce misali da gindayawar mota da jan burki, wannan kuwa shi ne ma'anar kaddarawa. Amma kuma bayan an riga an yi hatsari to wannan aukuwar da faruwan tasa ta kasance an hukunta kenan.

Komadai wane irin abu ne muke nufi a kaddarawa da hukuntawa -kamar yadda muka ce bahaushe yana amfani da su da ma'ana daya- ba komai ba ne sai samarwa da halittawa da Allah yake yi, kuma muna iya karawa da cewa; wannan yana kama da fadinmu ne cewa; Allah ya kaddara wa rana ta rika juyawa tana motsawa a wurinta, kuma ya kaddarawa duniya ta rika motsawa tana juyawa a wurinta a lokaci guda kuma tana tafiya tana kewaye rana a shekara sau daya, wannan al'amarin yana kaddara samuwar dare da rana. Amma kuma bayan samun dare ko rana to wannan yana nufin an riga an hukunta hakan an riga an gama kamar yadda aka yi wa takarda da aka rubuta sitampin[iv].

A cikin wadannan mas’alolin da suka shafi ayyukan bayi ne kafafu suka zame, don haka sai wasu jama'a suka tafi a kan tilasci kamar yadda ya gabata. Sai ka ga wani ya yi sata sai wasu su ce; an kaddara masa hakan ne, ko kuma ya ki daukar mataki da ya dace kan abu har ya faru sai a ce: an kaddara, ko kuma a ki canza wani abu da yana iya canzuwa kamar wani mutum ya zo ya take hakkin mutane sai ka ji an ce Allah ne ya kaddara hakan, kana iya ganin an yi magudi a zame sai kawai ka ji wani ya ce: Allah ya kaddara hakan ya ba wane mulki don haka sai saura su yi hakuri da hakan!

Idan muka ce Allah ne ya yi hakan kamar yadda mujabbira suke nufi cewa; shi ne ya yi hakan kai tsaye kamar yadda wuka take a hannun mai yanka to wannan yana iya komawa zuwa ga jingina wa Allah madaukaki tawaya da zalunci da aikata fasikanci da dukkan wasu ayyuka munana kamar kashe annabawa da salihan bayi -Allah ya nisanta daga haka-.

Don haka masu cewa; Allah ya kaddara mana wane ya kasance shugaba da ma’anar da mujabbira suke nufi, to sun jingina dukkan munana da zalunci ga Allah ne, kuma Allah ya barranta daga muradinsu da manufarsu da suke nufi suke jingina masa ita. Amma idan suna nufin Allah ya kaddara da ma'anar cewa ya tabar da ayyukan bayi da suka ki daukar mataki don haka sai ya ki kawo musu canji suka fada cikin bala’i yana gani ya kyale duk da zai iya canjawa amma ya sanya sharadin canjin shi ne su tashi tukuna, kuma ba zai gyara su ba sakamakon sakacin da suka yi suka bar hakkokinsu har ma wani mutum ya haye karagar mulki yana dandana masu kuda da azaba to wannan gaskiya ne kuma daidai ne, kuma muna iya cewa Allah ya kaddara kuma ya batar da wannan al'ummar idan dai suna nufin ya jingina su ga kawukansu kuma ya ki sanya rahama a cikinsu. Wannan kuwa yana komawa ne ga dokar Allah ta cewa; sai wanda ya yi kokarin neman shiriyarsa da datarwarsa ne yake taimaka, domin ba ya kawo canji sai mutane sun nemi canjin sannan sai ya kawo dauki.

Ra'ayoyin mujbira da ash'arawa da sufaye (sufayen da ba bisa tafarkin Ahlul Baiti (A.S) suke ba) suka samu ya taso ne daga musun sabuban da suke tsakatsaki wajen samar da halitta ko aiwatar da ayyukan halitta, domin idan muka duba zamu ga wanda ya yi kisa da wuka shi ne ake jingina wa kisa kuma shi ne ake hukuntawa, amma kwamandan da ya bayar da umarni aka yi kisa to ana iya jingina masa kisa kuma a jingina wa sojojinsa kisan domin suna da zabi kuma shi ma yana zabi. A wannan misalin da wani zai ce ayyukan nan na sojoji aiki ne na kwamanda kai tsaye kamar yadda wuka take a hannun mai kisa to ya yi kuskure, kuma a nan ne kafafun wadannan mutane da muka ambata suka zame, a nan ne suka sha kasa suka fadi warwas.

Don haka magana ta gaskiya muna iya cewa: kwamanda ya yi kisa kuma a hukunta shi kuma a ce sojoji sun yi kisa su ma a hukunta su, wannan kuma shi ne sahihin ra'ayi domin ba duk iri daya sabuba suke ba, sabuba suna da bambanci tsakaninsu domin akwai masu zabi kuma akwai marasa zabi, a nan muna iya ganin bayi suna da zabi kuma suna iya yi ko kuma su ki yi.

Kamar mai fadi ne (a wata waka ta Farisawa) da yake cewa: Dole ne ya sha giya, domin idan bai sha giya ba to ilimin Allah zai zama jahilci: yana nufin Allah ya kaddara masa dole sai ya sha giya, kuma sai ya dauki giya ya sha kuma ya kira wannan da cewa Allah ne ya kaddara. A nan muna iya cewa Allah ya halicci giya ta hanyar halittar tsabar da ake hadawa a yi giya kuma ya halicci tasiri tsakanin abubuwa da sinadirai kuma ya sanya tasiri cikin abubuwan da ake sarrafawa, don haka ne ma idan wani ya hada giya aka sha to za a iya buguwa sakamakon tasirin da Allah ya kaddara ya sanya a cikin wannan hade, wannan a batun halittawa kenan. Amma a game da shan wannan giya da hada ta da wannan ma’ana ba zai karbu ba domin shanta bisa zabi ne, kuma a fili yake cewa ba Allah ne ya yi shan bayi ba don haka ne ma bai yarda da shi ba kuma ya yi gargadin ukuba a kai, don haka ne ma idan wani ya sha giya sai aka ce Allah ya kaddara ya sha wannan giyar sai mu ce: idan ana nufin ya halitta giya sakamakon shi ne ya samar da wadannan sinadirai da tsirrai to haka ne amma idan kana nufin shi ya hada ta da kansa ya sha sai dai kawai ya yi amfani da wannan bawa ne wajen hada ta da shanta a nan sai mu ce; ka zo da wani abu mai muni kuma Allah ya barranta daga hakan. Haka nan idan ana nufin ya kaddara da ma'anar ya yi umarni da a sha a shar’ance sai mu ce wannan ma ya yi muni kwarai domin kage ne ga Allah kuma ba mu samu wani daga musulmi ya yi da’awar hakan ba, kamar yadda idan aka ce ai shi ya dauka ya sanya ta bakin mai sha kuma shi ya hadiyar masa da ita kamar yadda yake gun mujabbira, sai mu ce tir da wannan kauli da ya jingina dukkan nakasu da tawaya ga Allah madaukaki. Amma idan ana nufi ya kaddara da ma'anar ya tabar da wanda ya sha wannan giya ya kyale shi da halinsa kuma ya saka masa da mummunan aikinsa ta yadda ya yi tambele ko ya fada rami ko ya bige kansa ya ji ciwo to wannan haka ne. Haka nan idan aka ce: Allah ya kaddara wa wane ko su wane bata ko ya batar da al’umma kaza ko kuma ya shiryar da ita da cewa ba don Allah ya kaddara musu shiriya ba, da ba su shiriya ba, ko kuma ba don Allah ya kaddara musu bata ba, da ba su bata ba, wannan duka daidai ne idan aka cire tilasci a ciki.

Kuma muna iya ganin yadda Allah madaukaki ya ce; ya shiryar da Samudawa, a fadinsa madaukaki: "amma Samudawa sai muka shiryar da su, amma sai suka zabi makanta a kan shiriya" (fusilat: 17) a nan kalmar makanta tana nufin bata. Sannan kuma a fadin Allah madaukaki "mun shiryar da su" da zaka tambaya shin Samudawa sun shiryu sai a ce maka ba su shiryu ba, amma kenan shin Allah ya fadi sabanin gaskiya ne, sai mu ce; Allah ya barranta daga fadin sabanin gaskiya, to don me ya ce: ya shiryar da su!.

Idan aka ce: Allah ya kaddarawa Samudawa bata: ana nufin ya tabar da ayyukansu bai karba daga garesu ba kuma ya jingina su da kawukansu domin ba ya batar da mutane sai ya yi musun bayanin abin da zai tseratar da su (tauba: 115), wato Allah yana shiryar da mutane ne sannan kuma idan suka ki shiryuwa sakamakon zabinsu sai kuma ya batar da su, wato; idan ba su karba ba sai ya batar da su ya bar su da zabinsu, don haka muna iya cewa; ya batar da Samudawa. Saboda Allah yana cewa: “ba yadda za a yi Allah ya batar da mutane har sai ya yi musu bayanin abin da zasu ji tsoronsa”[2]. Kuma a fili yake a zahiri sai da Allah ya yi wa Samudawa gargadi ya shiryar da su sannan kuma sai ya batar da su sakamakon hanyar da suka zaba. A nan muna iya ganin shiriya kala uku ce; shiriya takwiniyya, da tashri’iyya kuma Allah ya yi wa Samudawa da dukkan al’ummar duniya wadannan. Sai kuma shiriya taufikiyya wacce Allah bai bayar da ita ba sai ga wanda ya karbi wadannan na farko ya yi amfani da su kamar yadda Allah ya so, amma bayaninsu zai iya kawar da mu daga abin da muke magana yanzu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next