Kaddara Da Hukuncin Allah



hfazah@yahoo.com

Saudayawa mutane sukan yi magana su ce: Allah ya kaddara ko ya hukunta, ko kuma Allah ya so ko Allah ya yarda, ko kuma al’amarin Allah ne da sauran kalmomi da suke amfani da su wajen bayanin wani abu da ya wakana, wannan al'amarin yana iya kasancewa mummuna ko kyakkyawa, sannan kuma yana iya kasancewa na samuwa ne da yake wakana ko kuma abu ne wanda Allah ya hana yin sa ko kuma ya yi umarni da a aiwatar da shi kamar na shari’a.

Don haka muna iya binciken wadannan kalmomi tukuna kafin mu shiga cikin bayanin hakikanin abin da ake nufi da wannan al'amari, sannan kuma sai mu yi bayanin tasirinsa a al’amuran da suka shafi al'umma da rayuwarta a ayyukanta na yau da kullum kuma ya dabaibaye cigabanta da ma samuwarta a matsayinta na al'umma mai hakki da 'yanci. Da farko muna iya binciken wadannan kalmomi na hukuncin Allah ko kaddarawarsa domin mu san me ake nufi da wadannan kalmomi a yadda al'ummarmu suke amfani da su da kuma yadda masana Allah suke ganinsu.

Kalmar Allah ya kaddara ko ya hukunta kalmomi ne da ake amfani da su da nufin al'amarin da ya wakana ya faru ko kuma abin da ya faru kuma ya samu: idan aka samu riba ko faduwa a kasuwanci ko aka kulla aure sai a ce Allah ya kaddara, haka nan idan aka samu haihuwa kamar aka samu namiji ko mace sai a ce; haka Allah ya hukunta ko ya kadddara ko kuma ya so ko kuma ya yi nufi. Wato da son Allah da kaddarawarsa da hukuntawarsa da nufinsa kai da yardarsa duk sai a yi amfani da su a kan al'amari daya. Koda yake ba kasafai bahaushe yake amfani da Allah ya yarda ba sai ga abin da yake na alheri ko na farin ciki da jin dadi, amma duk da haka idan da zaka ce Allah ya yarda yayin da ka fadi a ciniki ne ko kuma a jarabawar makaranta, ko a hasara kamar tadukiya, ko rashin lafiya, ko hadari, to suna komawa zuwa ga ma’anar cewa shi ne ya kaddara ya hukunta.

Idan muka duba mahangar ilimin sanin Allah muna iya ganin sun kawo ma’anar da suke amfani da ita game da kaddarawa da hukuntawa. Idan muka dauki kalmar kaddarawa "kadar" a larabci sun ba ta ma'anar da ta saba da ta hukuntawa ko zartarwa "kadhaa" a larabci. Yayin da zamu ga sun yi amfani da kalamr farko "kadar" a kan abin da ake auna shi ake kuma daidaita shi kamar dai mai dinki da yake auna yadi yake daidaita shi ta hanyar yankawa da hadawa da dinkawa domin samar da wando ko riga, ko kuma mai gini da yake kwaba yashi da sumunti kuma ya daidaita bulallika sannan sai ya daidaita tsakaninsu ya hada su domin samar da gini cikakke wanda zai iya ba mu gida cikakke gamamme shiryayye. Amma idan aka ce ya hukunta “kadhaa” to ya riga ya gama aikin kenan, wato ya zartar da aikin ya yi sitampin ya  gama, kamar gida ne da aka gama gina shi, ko kuma riga da aka gama dinka ta, ko kuma wani rubutu da aka gama aka sanya sitampi a kan takarda, don haka sai a ce: ya zartar ko ya hukunta, ko ya gama.

A nan kenan muna iya ganin bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu duk da kuwa suna layi daya ne ba layuyyuka mabambanta ba. Abin da muke nufi a layi daya suke kamar mai yanka yadi da yake daidaita shi ai ba komai zai cimma ba kuma ba wata natija za a samu ba sakamakon yanka wannan yadin sai kaiwa ga samar da riga, don haka ne ma muna iya cewa; kaddarawa a nan wato yanka yadi da dinka shi, da kuma hukuntawa wato gama dinki abubuwa biyu ne da suke a layi daya. Amma da mun ce ba a layi daya suke ba, to sai mu ce kenan mai dinki yana kaiwa ne ga samar da gida da dinkin da yake yi, kamar yadda muna iya cewa kenan (idan da haka ne) mai gini yana dora bulo ya kwaba siminti da yashi domin daga karshe a samu riga da wando, don haka ne sai mu ce a layi daya suke kenan, amma ba haka ba ne, domin ba a layi dayan suke ba. Domin mai dinki kaddarawarsa da hukuntawarsa tana iya kaiwa ne kawai ga samar da riga da wando da hula d.s.s. kamar yadda mai gini kaddarawarsa da hukuntawarsa tana iya kai mu ne ga samar da gida. Don haka ne muna iya cewa: kaddarawa da hukuntawa a layi daya suke a ma'anarsu, sai dai kawai sai an wuce marhalar kaddarawa ne sai a kai ga hukuntawa (ko kuma gamawa ko zartarwa). Kuma bahaushe kana amfani da wadannan kalmomi sannan sai ka sanya musu ma'anar so da nufi da yarda, kuma hakan daidai ne idan muka lura da cewa sai an yi so da kauna da nufi sannan sai a kai ga kaddarawa da hukuntawa, don haka sai ka ambaci abu da sunan da ake kiran sababinsa a fadinka da cewa; haka Allah ya so, ko ya yarda. Sannan wannan kaddarawa da hukuntawa natijar so din ne, kuma suna iya kasancewa a ayyukan halittawa da samarwa ko shar'antawa, ko ayyukan bayi: to a nan ne fa aka samu badakala da cakudewa da yamutsewar tunani.

Sai dai akwai bahasin palsapa kan wannan al’amari da ya shafi kaddarawa da hukuntawar Allah a bahasin iliminsa amma ba zan tabo shi ba saboda kebantarsa da Allah amma yana amfani wajen kawo misalai a yanayin ma’anar wasu hadisai da ba su inganta ba, da kuma bayanin cewa; ilimin Allah da faruwar abu tun kafin faruwarsa ba ya sanya shi mai tilasta faruwar abun ta hanyar dankara shi kan bayi ba da zabinsu ba. Don haka ne zamu bayar da karfi kan mas’alar kamar yadda malaman sanin Allah suka yi bayani domin shi ne ya fi saukin fahimta sannan kuma ya fi amfani ga al’umma. Kodayake akwai dan bambanci a isdilahohi da suke amfani da su tsakanin imamiyya da mu’utazila da ash’ariyya abin da yake bahasi ne da ba zai amfane mu ba a irin wannan matsayin koda yake ba zai cutar ba.

Idan aka ce Allah ya halitta me ake nufi? Kuma me muke iya fahimta daga wannan magana? Tabbas na san masu amsa zasu bayar da jawabi kan cewa Allah ya samar da wani abu ne. A wannan fage muna da ma'anar halittawa da take nufin samarwa, wannan samarwa din ba ta hannun abin halittawa, kuma ba ta hannun abubuwan da suke a matsayin sabuba da aka yi amfani da su wajan wannan aiki na samarwa, sai dai wadannan abubuwan da suke sabuba suna iya yin tasiri cikin yanayin da aka yi halitta din.

Da wani bayani da ya fi sauki muna iya cewa; Ubangiji yana yin halitta, kuma saudayawa a wannan duniya da muke iya amfani da gani ko ji ko tabawa ko dandanawa ko shakawa domin rizkar abubuwa mabambanta a cikinsu da akwai abubuwan da Allah ya sanya su sabubba domin samar da halittun da suke cikinta wadanda suka hada da mutum da dabbobi da tsirrai d.s.s, sai dai cewa; wadannan sabuban duk da ba su suke yin halitta ba amma Allah ya sanya su masu tasiri cikin halitta din. Misalin zafi da muke iya ganin yana faruwa sakamakon kunna wuta, muna iya ganin wannan zafin da Allah ya samar da shi bai kawo shi haka nan ba batare da wani sababi ba, a nan muna iya ganin ya sanya sababin samar da zafi ita ce wuta, ko rana ko gas da sauransu, kamar kuma yadda yake samar da ‘ya’ya ta hanyar iyaye ne. Kuma mazhabin Ahlul Baiti (A.S) ya saba da ash’arawa da suka cire tasirin wadannan sabuban suna masu ganin cewa Allah ne yake halittar zafi, kuma babu wata rawa da wadannan sabuban kamar wuta da rana suke iya takawa wajan samar da zafi.

Amma wannan magana ta ash’arawa tana da rauni idan muka duba zuwa ga samuwar tasirin wadannan abubuwan a zahiri ta yadda: furiji ko wata da yake sama ba zasu iya bayar da zafi ba, kuma wuta da rana ba zasu iya bayar da sanyi ba, kamar yadda maniyyin mutum ba ba zai iya bayar da kare ba, kuma kwan kaza ba zai iya bayar da shaho ba! Haka nan dai muke iya ganin tasiri tsakanin aububuwa mabambanta don haka ne ma ash’arawa suka kirkiro ra’ayinsu na “kasb” al’amarin da yake bai gushe ba cikin duhu, kuma wannan ne ma ya sanya Imamul Haramain ya yi kokarin gujewa daga wannan ra’ayi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next