Kaddara Da Hukuncin Allah



Kamar yadda muna iya ganin munin hakan ya sanya mu'utazila gudu daga wannan ra'ayi, amma sai suka fada cikin mummuna irinsa ko kuma sama da hakan ma muni, suka ce babu hannun Allah sam a ayyukan bayi, sun yi tsammanin wannan zai iya warware matsalar da suka yi gudu, amma sai suka gujewa tarkon farko suka fada wa na biyu, sai suka gujewa tarkon butulcewa Allah suka fada na gwama shi da waninsa; yayin da suka sanya mutum a matsayin mai tasiri kan ayyukansa mai zaman kansa ba tare da wani hannu da Allah mahaliccinsa yake da shi a kai ba.

A nan ne imamai (A.S) suka karfafa da cewa duk wanda ya yi furuci da tilascin Allah ga bayi to ya butulce masa, wanda kuwa ya tafi a kan ganin damar mutum (cire hannun Allah daga ikon ayyukan dan Adam) to ya gwama shi da waninsa. Kuma muna iya ganin yadda Allah yakan canja mana wani mataki ko ya ba mu wata kariya, ko kuma ya hana mu wata tafiya ko ya shiga tsakaninmu da wani abu da muke so a wasu lokuta, kuma wannan yana nuni da cewa; ashe bai cire hannayensa daga ayyukanmu ba.

A kan haka ne muke iya cewa; akwai hannun Allah a ayyukanmu duk da kuwa bai tilasta mu ba, wato da Ubangiji bai ba mu ilimi da hankali da karfi da iko da nufi da lafiya ba, da ba mu iya yin wadannan ayyukan ba, don haka akwai hannunsa a cikin ayyukanmu, amma kuma bai tilasta mu ba saboda ya halicce mu tare da zabi, domin ba ma'ana ya ce mu yi sannan sai ya tilasta mu kan yi ko kan kin yi, ko kuma ya ce mu bari sannan sai ya tilasta mu kan bari ko rashin bari, domin idan ya yi hakan sannan sai ya azabtar da masu yi ko masu bari sabanin umarninsa ko haninsa kuma ya ni'imtar da masu yi ko masu bari bisa dacewa da umarninsa ko haninsa, to wannan ya saba da hikimarsa kuma tambaya ta hankali ba zata gushe ba tana ganin zaluncinsa (Allah ya daukaka daga aikata haka, tsarki ya tabbata gareshi).

Don haka ne muke cewa; akwai hannun Allah a cikin ayyukanmu amma kuma bai tilasta mu ba, kuma Allah ya shiryar da kowane mutum da ma'anar aiko sako, sannan kuma ya shiryar da wasu da ma'anar sun yi riko da ni'imar da ya yi musu ta hankali sai suka bi shi, kuma ya batar da wasu mutanen da ma'anar sun ki riko da ni'imar da ya yi musu ta hankali sai suka saba masa.

A nan muke cewa; idan mutum ya ga dama yana iya  shiryuwa, kuma da ya ga dama yana iya bacewa, sai shari'a ta dangana bata gareshi domin ya ki amfani da hankalinsa ya ki biyayya ga umarnin Allah, kuma shari'a ta dangana shiryarwa ga Allah saboda shi madaukaki shi ya ba shi hankali da karfi da nufi da gabobin da ya yi amfani da su da duk wani abu da ya yi riko da shi kai har ma da sakon wahayi da aka yi da aiko annabi da shiriya da ya amfana da su wajen samun shiriya, karshe ma hatta da shi samuwar kansa.

Don haka a nan idan mutum ya ga dama ta hanyar riko da sabuban hakan yana iya dacewa ga shiriya, kuma wannan shi ne ma'anar kaddarawa da Allah ya yi a wannan al'amarin. Kuma muna iya ganin wadannan al'amuran matsayai da darajoji ba sun takaita da lahira ba ne, ko abin da ya shafe ta, har ma da duniyar mutum suna shafa: don haka idan mutum ya ga dama ta hanyar rikon sabubai yana iya cewa; ni ina son zama likita ko injiniya ko malamin addini ko shugaban garinmu ko kuma mai labarai ko makamancin wannan kuma idan ya samu yin riko da sabuban hakan yana iya kaiwa ga hakan da taimakon Allah da ya shirya masa kuma ya yalwata masa wadannan sabubai masu yawa a wannan duniya tasa.

Don haka ne kakan ga wani ya tashi tsaye yana son ya kasance daga waliyyan Allah ko kuma masu kawo gyara ko kuma masu shiryar da mutane zuwa ga Allah ko masu bauta wa Allah, da makamanta hakan, kuma matukar ya yi riko da hanyar yin hakan to sai a samu dacewa da wannan yalwatawar da Allah ya yi masa.

Kamar yadda idan ya dauki hanya sahihiya ta yin hakan ya kan iya kaiwa ga kololuwar hadafinsa, haka nan idan ya yi riko da sabuban hakan kan al'amuransa na wannan duniya -wadanda a bisa hakika su ma suna komawa ne zuwa ga al'amuran lahirarsa-  a wannan duniyar yakan iya kaiwa ga kololuwar hadafinsa, kuma haka nan kuskure wajen rikon hanya sahihiya a duka biyun yakan iya kaiwa ga rashin dacewa.

A kan wannan al'amari ne muzaffar mai littafin akidojin imamiyya yake cewa: "Mujabbira[i] sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi a kan cewa ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi’a tsakanin abubuwa[ii], suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika.

Sun yi musun wannan sababi ne saboda tsammanin cewa hakan shi ne ma’anar kasancewar Ubangiji mahalicci, Wanda ba Shi da abokin tarayya, amma duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next