Kaddara Da Hukuncin Allah



Sannan muna iya ganin cewa a wannan mahallin na halittawa babu wani abu da zai iya zabar yadda zai kasance, don haka Allah ya yi nufin su kasance kamar yadda yake so kuma haka nan ya kaddara ya hukunta. Da wannan ne muke sanin cewa idan aka haifi mutum to don Allah ya yarda ya yi shi ne, kuma ya hukunta ya lizimta ya tilasta ya kasance kamar yadda ya yi shi, babu wata rawa ta zabinsa da zai iya takawa kan wannan ko kadan, sai dai akwai rawar da sabubba suke iya takawa, kamar ana iya halittarsa nakasasshe ko tauyayye sakamakon buguwar cikin uwa ko nau’in yadda take kwanciya, ko kuma nau’in abincin da take ci, ko kuma nau’in yadda ake saduwa kamar shin a lokacin cikin bakin ciki ne ta samu cikin ko lokacin farin ciki ko razani ko rashin nutsuwa da makamantansu.

Sannan muna iya ganin nau’in halittun sun sassaba a yanayinsu, mafi girman kima da Allah ya yi wa mutane da mala’iku da aljanu shi ne; su suna iya sabawa idan suka ga dama, a yau idan mala’iku da mutane da aljanu suka ga dama suna iya yi wa Allah tawaye, amma sauran halittu sai aka yi su da wata dabi’a tabbatacciya da ba ta karbar canji sai dai amfana daga gareta domin samun wata habaka zuwa wani mikdari daidai gwargwado kamar yadda ake yi wa kare tarbiyyar gadi ko aike.

Halittarmu tana iya nuna mana cewa ba mu da zabi kan yadda za a samar da mu kuma wannan samuwar tana da marhaloli daban-daban, sannan muna iya ganin hakan a fili cewa da an tambayi wani mutumin me kake so ka kasance da ya ce ina son in kasance kamar yanayi kaza ko kuma shakali kaza ko kuma kamar wane. Ba wasa ba ne kuma ba rashin hadafi ne ya sanya ka ga mutane musamman wasu lokuta wasu mata suna yin shafe-shafe domin su gurje fatarsu ta koma irin wata kala, musamman ko daga baka zuwa fara, ko daga fara zuwa yalo da sauransu.

Sai kowa ya kasance yana da wani yanayi daban da na waninsa, kuma da an nemi shawararsa da an yi shi dan kabila kaza, ko launi kaza, ko kuma da ma an haife shi dan kasa kaza, da ma shi ne wane kaza! daidai gwargwadon ma'aunan da suke su ne ma’aunin kamala gunsa.

Sannan kuma ya halicce su ne bisa mafi tsarin halitta ta yadda tawaya da take faruwa a halittarsu take komawa zuwa ga sabubban samuwarsu ne da suke karbar tawaya da kamala domin mustahili ne wannan tawayar ta zo daga Allah madaukaki mai tsantsar kamala da babu wani kwarzanen tawaya gareshi. Duk da haka wannan ba zai sanya mu mantawa da cewa dukkan komai asalinsa ya gangaro daga Ubangiji madaukaki ne.

 Sannan wannan sabubban suna da tasiri matuka, kuma wannan yana daga cikin abin da ya sanya ni tambayar malamina Allama Ayatullahi Sayyid Adil Alawi cewa; don me mutane suke ganin a halittar wasu mutane musamman mace a kan samu dalilin arzikinsu da kuma talaucinsu ta yadda za a ce tana da kashin tsiya ko kashin arziki. Sai ya ce: “Haka ne, kamar yadda mu ma a nan kasashenmu muna da irin wannan; akan ce wance tana da goshin tsiya ko goshin arziki sai dai wannan wani bangare ne na sababi da ana iya kawar da shi da addu'a da makamantan hakan”. Al’amarin tasirin bayi a cikin ayyukan Allah da halittawarsa abu ne sananne da shari’a ta zo da shi, kuma muna iya ganin wannan misalin a hadisan da suka yi bayanin ajalin da aka hukunta wa mutum amma sai a canja shi. Misali ya zo cewa: Allah yana kaddara wa wani mutum zai mutum nan da kwanaki 3 amma sai ya yi sadaka ko sadar da zumunci sai Allah ya mayar da shi shekaru 30. Don haka mu mun saba da yahudawa da suka ce an yi wa hannayen Allah kukumi; ya riga ya gama komai ba zai iya canja wani abu ba.

A takaice muna iya cewa; babu wani zabi da muke da shi a kan al'amarin halittawa, sai dai muna iya tasarrufi cikin sabuban halittawa, ko kuma mu yi wani abu da Allah zai canja mana wani abu da ya kaddara shi a kanmu. Kuma tasarrufi cikin sabuban samarwa wani abu ne wanda aka samu iliminsa a likitanci a wannan zamani kuma shari'a ba ta kore shi ba kamar yadda tun farko shari'a ba ta yi musun sa ba.

Ayyukan Mutane Da Kaddara

Haka nan matakan da dan Adam yake dauka ana kirga su cikin kaddarawar Allah ne: kamar dai shan magani ne ga marasa lafiya, ko yawaita istigfari ga mai son ya yi arziki, ko saukar ni’imar Allah ga al’umma idan ta yi imani ta yi takawa. Kuma muna iya ganin wannan a koyarwar musulunci a ruwayar Saduk a littafinsa “Attauhid” shafi na 369, yayin da imam Ali (A.S) yana tafiya ya kauce daga kusa da wani bango da ya karkace kamar zai fado, sai wani ya ce; masa: Ya Amirul muminin shin kana gudun kaddarar Allah ne? sai imam Ali (A.S) ya ce: “Ina gudu daga kaddarar Allah ne zuwa ga kaddarar Allah”!  Shi ya sa muka ga ruwayar da take magana game da mutane biyar wadanda ba a karbar addu’arsu ya hada da wanda ya ga garu ya karkata zai fado bai kauce ba har ya fado masa (wannan yana kama da mai addu’a ne a kan wani al’amari amma bai dauki matakin da ya dace da shi ba, ba yadda za a yi ya ga kyakkyawar natija).

Kuma a wata ruwayar muna iya ganin yadda imam Ali (A.S) ya ba wa wani mutum amsa game da cewa; yakin da suke yi da kaddarawar Allah ne ba tare da Allah ya tilasta su ba, sai dai wani abu ne wanda suke zuwa da zabinsu, kuma ba don wannan zabin da Allah ya ba su ba, to da babu ma’anar aiko manzanni da aikin lada ko na sabo ko kuma umarni da hani ko sakamakon aljanna da wuta. Don haka ne ma ya zo daga imam Ridha (A.S) cewa: Duk wanda bai yi imani da kaddara ba to ya kafirta.

Saudayawa wasu suna cakudawa tsakanin kaddarawar shar’antawa da kuma ta samarwa, sannan sai su tashi wata natija mai ban mamaki da zata kai su ga imani da tilascin ayyuka da rashin zabin kansu, don haka sai su jingina wa Allah ayyukansu da wani lokaci sukan iya kasancewa na sabo ko na zalunci da munana kai tsaye. Wani lokaci kuma suna cire tasirin kansu a matsayinsu na masu zabi suna masu kaddarawa cewa; kaddarar Allah tana cire musu zabin da ya ba su: muna iya ganin irin wannan al’amari kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next