Tattalin Arzikin Iyali



"Sai Aliyu ya fita yana dauke da Fadimatu 'yar Manzon Allah (s.a.w.a.) a kan dabba da daddare zuwa mazaunan Ansar, tana neman taimakonsu; su kuwa sun kasance suna cewa: Ya 'yar Manzon Allah, hafcika bai'armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba".21

Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadimatu (a.s.) da Khalifa Abubakar (r.a.) da Umar bin Khaddabi (r.a.). Ta hanyar lura da ayoyin nan biyu (ayar Shawara da ayar Wilayar Muminai), kamar yadda bayanin fassarar su ya bayyana daga Sayyid Sadar, za mu same su a matsayin asasi na tunani mai fadi kan hakkokin siyasa; kai! wajiban siyasa ga al'umma da dukkan mutanenta maza da mata daidai wa daida.

Wata aya kuma wadda ke wajabta aikin siyasa da wajibcin Kifa'i a kan maza da mata, kamar yin tawaye wa mahukunta masu dagawa, tsayar da daular Musulunci, wayar da kan mutane ta fuskar siyasa da wasun wadannan, ita ce fadar Allah Madaukaki:­

"A sami wasu mutane daga cikinku, suna kira zuwa aikata kyakkyawan aiki da hani da mummuna, wadannan su ne masu babban rabo."

AIKur'ani Mai girma a wannan aya, yana wajabta samun wasu jama'a daga Musulmi da suke kira da kyakkyawan aiki suke kuma hani da mummuna; wadannan jama'a sun hada maza da mata daidai wa daida, da dalilin fadar Allah Madaukaki:­

"Muminai maza da muminai mata kuwa, maji6inta al'amarin juna ne; suna umurni da aikata allied kuma suna hani daga mummunan aiki, wad'annan su ne masu babban rabo." Surar Taubati, 9:71.

Bayyanannen abu ne a tunanin Musulunci cewa fagen siyasa shi ne fage mai fadi da ya hada horo da aikin kirki da hani da mummunan aiki, wadanda suka kunshi kira zuwa tsayar da tsarin Musulunci, kalubalantar azzaluman shugabanni da karakatattun tsare-tsare na zalunci, kamar yadda suka kunshi shiga cikin gudanar da shugabanci, tsarin siyasar al'umma, wayar da kan mutane a fagen siyasa, shawara da mubaya'a kamar zaben shugaba da wakilin al'umma, shiga cikin wakilcin al'umma a majalisu da muke kira da 'majalisun wakilai', wadanda ke aikin horo da aikin kirki da hani da mummuna ta fuskar siyasa da sauran irin wadannan.

Ta hanyar nazarin yanayin zamantakewa da siyasa wadanda ya wajaba ayi aiki a tsaikonsu, za mu iya fitar da cewa wannan al'umma (ko mutane) da Alkur'ani ya yi kira da a same su da cewarsa: "A sami wasu mutane daga cikinku.." ba za su iya aiwatar da aikin su a matsayin su na mutane kamar yadda AIKur'ani ke so ba sai sun zama mutane tsararru, wadanda ke gudanar da ayyukansu ta wayayyun hanyoyi wadanda suka dace da yanayi da marhalar tarihi da Musulmi ke raye a ciki.

Wannan na nufin wajibcin shigar mace yadda ya kamata cikin jama'a da ayyukan siyasa, da cikin kungiyoyi, jam'iyyu da mu'assasosin tunani da kawo gyara dabam-dabam, matukar aiwatar da wannan wajibi kamar yadda ake bukata ya ta'azzara ba tare da haka ba.

Daga wadannan asasai na AIKur'ani za mu fahimci cewa rayuwar siyasa a Musulunci a bude take ga mace kamar yadda take bude ga namiji a dukkan matsayinsu -na wajibi Aini da Kifa'i- ko halaccin shiga cikin rayuwar siyasa da dukkan fagagenta.

KALMA TA KARSHE

KARIN BAYAN I

A karshe: mace ba ta da hakki ko karimci sai a Musulunci, wanda ya tabbatar da ka'idojin hakkoki da karama ga daidaikun nau'in dan Adam baki daya da fadarsa:­

"Hakika Mun karrama bani Adama, Muka kuma dauke su a tudu da ruwa, Muka kuma fifita su a kan da yawa daga abubuwan da muka halitta da fifita wa mai yawa."

"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.."

Da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.):­

"Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata".22 don haka ba abin da ya rage ga mace sai ta nemi hakkokinta kamar yadda AIKur'ani ya tanadar mata, ta kuma lizimci abin da ya wajaba a kanta kamar yadda AIkur'ani ya iyakance mata; a matsayinta na uwa, 'ya, kuma mata; kuma a matsayin ta na mutum da ke da hakkin wilaya da kauna a cikin al'umma; da ke amfani da iyawarsa na tunani, rai da jiki a wuraren alheri, tsarki da kawo gyara. Bayan ta jarabci dacin rayuwa a rudun rayuwar sha'awe-sha'awe munana a duniyar wayewar duniyanci watsattsiya.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8