Tattalin Arzikin Iyali



5-Koma bayan abubuwan da muka ambata a sama,

asalin da shari'ar Musulunci ke tabbatarwa game da aiki shi ne halalci; da haka yin aiki don tara dukiya ko kara yin kudi wani al'amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari'a ta halalta.

Yayin nazari da bin diddigin ma'anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba za mu sami abin da ya hana mace yin aiki ba, ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji da magana da shi sun zo cikin wasu nassosii.

Ayyukan Matar Aure: Shari'ar Musulunci ta iyakance wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure da abubuwa kamar haka:­

1-Yana daga hakkin mace ta shardanta wa miji cewa ba zai hana ta yin aiki ba a lokacin daura aure.

2-Miji ya amince a kan aikin matarsa ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu; wannan idan ta so yin aiki ba tare da wani sharadi da ya gabata ba ke nan. Idan kuwa miji ya ki amincewa da matarsa ta yi aiki a irin wannan hali, wannan ba ya nufin cewa shari'ar Musulunci ta hana mace aiki. maimakon haka wannan na komawa ne ga alakar miji da matarsa.

3-Idan mace ta yi aure alhali ta riga ta yi yarjejeniyar aiki na wani ayyanannen lokaci da wasu. to yarjejeniyar aikin ba ta baci ba, ko da kuwa ya sabawa hakkin miji.

4-Idan matar aure ta kulla yarjejeniyar aiki ba tare da izinin mijinta ba. to ingancin wannan yarjejeniya ya tsayu ne a kan yardar mijin idan aikin na sabawa hakkokin miji. idan kuwa ba ya sabawa hakkokinsa, yana aiwatuwa.

5-Hukuncin macen da ta kulla duk wata yarjejeniyar aiki

da mace ta kulla yana gudana.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next