Tattalin Arzikin Iyali



Lura na ilimi ga bin diddigin malamai game da wajibai, da kasa su zuwa wajibi na Aini (shi ne irin wajibin da ya hau kan kowane mutum, wani ba ya daukewa wani; kamar sallolin wajibi) da na Kifa'i (shi ne wajibin da ya hau kan mutane a matsayin su na jama'a, idan wasu suka yi shi ya fadi a kan sauran; kamar sallar gawa), za ta bayyana gare mu, ta hanyar nazarin wajibin Kifa'i, cewa tsarin Musulunci ya wajabta wa daidaiku, ba tare da iyakance jinsin mace ko namiji ba, ya wajabta musu samar da bukatun al'umma da duk kashe-kashensu; kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da wasunsu na daga ayyukan da al'umma ke bukata; kai! wajibin Kifa'i ma na sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutum ko wasu mutane da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su; ba kuwa tare da la'akari da jinsin namiji ko mace ba.

Daga wannan za mu fahimci cewa kasa ayyukan hidima cikin al'umma da aiwatar da su, ya ginu ne a bisa asasai biyu: na mutum shi kadai da na tarayya; kuma a cikin dukkan halayen biyu, Musulunci bai bambanta tsakanin namiji da mace ba, maimakon haka, a wasu fagagen wajibcin Kifa'i, kamar wajibcin aikin likita da ya kebanci mata da karantar da su, yana fuskantar da wajibcin ne zuwa ga jinsin mace.

MACE DA HARKOKIN SIYASA

Daga cikin al'amurra na asasi da aka sanya a teburin tattaunawa da muhawara ta tunani da wayewa a karni na ashirin, akwai al'amarin hakkokin mace, daga ciki kuwa har da shigar ta cikin rayuwar siyasa da harkokin siyasa.

Abin da ke ba da mamaki shi ne cewa wadannan masu kira ga hakkokin mace na siyasa, suna fuskantar da tuhumarsu ga tunanin Musulunci da akidunsa, suna siffanta su da cewa tunane-tunane da akidu ne da suka haramta wa mace shiga cikin rayuwar siyasa, kuma su ke hana ta aiwatar da ayyukan siyasa; suna dogara da abin da suke ikirari da yanayin zamantakewa da siyasa wadanda suke shaidawa a garuruwan Musulmi, ba tare da sun tantance Musulunci a matsayinsa na tsari, shari'a da dokoki; da masu bin Musulunci wadanda ke misalta shi a cikin halayyarsu ta siyasa da zamantakewa ba; da cewa abin da suke shaidawa a kasashen Musulmi ya sabawa yadda ya kamata ya kasance cikin al'ummar Musulmi ba; domin surar mace a wadannan kasashe na Musulmi da hanyar yin mu'amala da ita da kimarta a cikin al'umma, a yanayin da yake na sabawa Musulunci, ya samo asali ne daga wasu tunane-tunane da al'adu da ayyuka na zamantakewa da ba sa misalta Musulunci, masamman ma matsayin mace a fagagen aiki, al'adu, zamantakewa, siyasa da alakarta tare da namiji.

Siyasa a yanayin Musulunci na nufin lura da sha'anonin al'umma a dukkan fagagensu na rayuwa, da ja-gorancin tafiyar da suke yi a hanyar Musulunci; don haka ita (siyasa) wani nauyi ne na zamantakewa baki daya da aka kallafa wa musulmi baki daya. Wannan nauyi malamai sun kira shi da Wajibi na Kifa'i; wato game da shi ake horo da magana da dukkan Musulmi, ba tare da la'akari da kasancewarsu maza ko mata ba, in banda wanda aka toge (saboda wani dalili) daga cikinsu; misali fad'ar Allah Madaukaki:­

"..Cewa ku tsayar da addini kuma kada ku rarraba". Surar Shura, 42:13. Da irin fadarSa Madaukaki:­

"Allah kuma Ya yi wa wadanda suka ba da gaskiya daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alkawarin lalle ba Zai sanya su masu mayewa a bayan kasa kamar yadda Ya sanya wadanda suka gabace su masu mayewa..." Surar Nuri, 24:55. Da fadarSa Madaukaki:­

"..ku bi Allah kuma ku bi ManzonSa da kuma majibinta al'amurranku (wato Imamai Ma'asumai).." Surar Nisa'i, 3:59.

Cikin dukkan wadannan ayoyin ana fuskantar da magana ne ga dukkan Musulmi maza da mata; ashe ke nan tsayar da addini da akidunsa da dukkan tsare-tsarensa na siyasa, zamantakewa, ibada da sauransu, nauyi a kan dukkan Musulmi, haka nan horon yin biyayya ga Majibinta al'amurra da ya zo a cikin wannan aya ana fuskantar da shi ne zuwa ga dukkan baligai; haka nan alkawarin mayewa ana fuskantar da shi ne ga dukkan wadanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari maza da mata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next