Tattalin Arzikin Iyali



"Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka, kuma kar ka manta da rabonka na duniya..". Surar Kasasi, 28:77.

Kamar yadda shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki da neman kudi, haka ta yi bayani a kan bambamce-bambamcen karfi da iyawar dan Adam, da wajibcin samun kamala ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaikun nau'in dan Adam; Allah Madaukaki Ya ce:­

"...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hldima." Surar Zukhrufi, 43:32. Kamar yadda AIkur'ani ya kwadaitar a kan yin aiki,neman abinci da musayar amfanoni; Manzon Allah (s.a.w.a.) na daukar yin aiki da neman arziki a matsayin jihadi da ibada; hakika haka ya zo cikin abin da aka ruwaito daga gare shi (s.a.w.a.) cewa:­

"Mai wahalar neman kudi don iyali kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah".18

"Ibada kashi bakwai ce, mafificiyarsu neman halaliya". 19

 Hakika malaman furu'a (fikihu) sun yi kokari mai yawa wajen karance-karance da bin diddigin game da yin aiki da neman abinci, inda suka fitar da hukunce-hukuncen shari'a da matsayinta game da aikin sana'a da hidima, kuma suka kasa su kashi biyar ta fuskar shari'a kamar haka:­

1-Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kan shi, a matsayin wajibi; kai! ta ma wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da ke kansa.

2-Haka nan Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa da ayyukan alheri; a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin haka.

3-Shari'ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana'anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina da wasun wadannan; kamar yadda ta haramta duk wani aiki da ke ja-gora zuwa aikata haram, ko da kuwa shi a kashin kanshi halal ne.

4-Shari'ar na daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu dabam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next