Hadiye Fushi da JuriyaKamar yadda aka ce, girman kai shi ne “mutum ya wulakanta sauran mutane da kaskantar da gaskiyaâ€, ya zo cikin wasu ruwayoyi cewa wannan nau'i na girman kai shi ne mafi muninsa. Daga Abdul’A’ala bn A’ayan yana cewa: Abu Abdullah (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: mafi girman girman kai shi ne wulakanta halittu da kaskantar da gaskiyaâ€, sai ya ce: na ce: mene ne wulakanta mutane da kaskantar da gaskiya? Sai ya ce: “Jahiltan gaskiya da cutar da ma’abutanta, duk wanda ya aikata haka, to yana gasa da Allah cikin rigarsaâ€. A cikin wani hadisin kuma na daban daga Muhammad bn Umar bn Yazid, daga babansa yana cewa: “Na fadi wa Abi Abdillah (a.s) cewa: ni na kasance mai cin abinci mai kyau, da kuma jin kamshi mai dadi, da kuma hawar abin hawa mai kyau, yana suna bi na, shin akwai girman kai cikin hakan don kada in aikata? Sai Abu Abdillah (a.s) yayi shiru na wani lokaci ya ce: “Lalle mai girman kan da aka la’ana shi ne wanda ya wulakanta mutane da rufe ido kan gaskiyaâ€, Umar ya ce, sai na ce: Gaskiya dai ba na rufe ido kanta, wulakanta mutane kuwa ban sanshi ba: sai Imam ya ce: “wanda ya kaskantar da mutane da yi musu ji-ji da kai, wannan shi ne mai girman kai[33]â€. Ahlulbaiti (a.s) sun bayyana dalilin girman kai da alfahari, kamar yadda ya zo cikin wani hadisinsu – da cewa shi ne shu’urin gazawa da kaskanci cikin zuciyar mai shi. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Babu wani mutum da zai yi alfahari face sai saboda gazawa da kaskancin da yake ji a tattare da shi[34]â€. A wani hadisin kuma na daban an ruwaito shi (a.s) yana cewa: “Babu wani mutum da zai yi girman kai face sai saboda wani kaskanci da gazawar da yake ji cikin zuciyarsa[35]â€. Daga cikin alamun da suke nuni ga girman kai – kamar yadda ya zo cikin ruwayoyi – har da wuce gona da iri da rashin girmama sauran mutane. Cikin wani hadisi daga Husain bn Abil Ala, daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: na ji shi (a.s) yana cewa: “Mai yiyuwa ne girman kai ya kasance cikin ashararan mutane daga kowani jinsi, girman kai kuwa mayafin Ubangiji ne, duk wanda ya yi gasa da Allah kan mayafinSa babu wani abin da zai same shi face kaskanci. Wata rana Manzon Allah (s.a.w.a) ya wuce ta wasu hanyoyi na garin Madina…………, sai aka ce mata: kauce daga hanyar Ma’aikin Allah (s.a.w.a), sai ta ce: ai hanya ta kowa ce, sai jama’a suka taso mata, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ku barta ita ma’abuciya girman kai ce[36]â€. f)– Handama, Kasala da Wauta
Har ila yau akwai kuma wasu dabi’u da shu’uri na zamantakewa da shari’a ke kyamansu sakamakon irin mummunan tasirin da suke da shi cikin rayuwar dan’Adam na shi kansa ko kuma tare da sauran al’umma, ta yadda mutum zai kasance bawan waninsa ko kuma mai take hakkokin sauran mutane ko kuma wanda ya kange kansa daga gare su da kuma al’ummarsu. Daga cikin irin wadannan shu’uri da ke da mummunan tasiri a rayuwar dan’Adam har da handama.
|