Hadiye Fushi da JuriyaNa Biyu: Hadiye Fushi da Ababe Masu Motsa Rai
Muna iya samun cikakken bayani kan batun hadiye fushi da ababen da ke motsa rai cikin maudhu’in Jihad al-Nafs (fada da son zuciya) kamar yadda muka yi nuni da hakan a baya, kamar yadda kuma za mu iya samunsa cikin hukumce-hukumce zama da mutane. 1 – Hadiye Fushi da Siffofi Abin Yabo
A fili za mu ga a duk lokacin da Allah Madaukakin Sarki ko kuma ManzonSa da Imamai (a.s) suke magana kan kan siffofin kwarai (abin yabo) na dan’Adam ko kuma siffofin da ya kamata ya siffantu da su inda yana son zama mumini, za mu ga cewa suna jaddadawa kan siffofin da ke da alaka da wannan bangare na ruhin dan’Adam wato abubuwa masu motsa rai. Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Yana da kyau mumini ya kasance yana da siffofi takwas: dauriya yayin harzuka, hakuri yayin bala'i, godiya (ga Allah) yayin jin dadi, yarda (ta zuci) da abin da Allah Ya arzurta shi da shi, ba ya zaluntar makiya, ba ya cutar (rashin adalci) da abokai, jikinsa na cikin wahala daga gare shi, (sauran) mutane kuwa suna cikin jin dadi daga gare shi. Hakika ilmi masoyin mumini ne, hakuri kuwa mataimakinsa, hankali kuma kwamandan dakarunsa, tausayi (sassautawa) kuwa dan’uwansa, biyayya kuma mahaifinsa[1]â€. Daga Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Siffofi uku duk wanda ke da su siffofin imaninsa sun cika: Idan ya samu kwanciyar hankali (da wani abu) hakan ba ya sanya shi cikin barna, idan kuwa wani abu ya sosa masa rai (fushi), fushin ba ya fitar da shi daga gaskiya, idan ya samu karfi ba ya wuce (gona da iri) kan abin da ba nasa ba[2]â€. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ashe ba zan sanar da ku wanda ya fi kama da ni daga cikinku ba? Sai suka ce: Na’am Ya Manzon Allah! Sai ya ce: Mafi kyawawan dabi’un cikinku, mafi saukin taimakon cikinku, mafi kyautatawan cikinku ga makusantansa, mafi so da nuna kauna ga ‘yan’uwansa na addini, mafi hakurin cikinku kan gaskiya, mafi hadiye fushin cikinku, mafi kyautata yin afuwan cikinku, kuma mafi tsananin adalci da daidaitawa yayin farin ciki da kuma fushi[3]â€. a)– Hakuri Kan Biyayya da Kuma Hakuri daga (Aikata) Sabo
Daga nan za mu ga cewa hakuri wajen biyayya ga Allah, da kuma hakuri wajen aikata sabon Allah Madaukaki suna zuwa a matakin farko na ayyukan kwarai. A cikin wani ingantaccen hadisi, an ruwaito Abu Abdullah al-Sadik (a.s) yana cewa: “Idan Ranar Kiyama ta tsaya, wasu jama’a ta mutane za su mike su nufi kofar Aljanna, sai a ce musu: ku ne su wa? Sai su ce: mu ne ma’abuta hakuri, sai a ce musu: a kan me ku ka yi hakurin? Sai su ce: mun kasance masu hakuri kan biyayya ga Allah, da kuma hakuri wajen saba masa. Sai Allah Madaukakin Sarki Ya ce: lalle sun yi gaskiya, ku shigar da su Aljanna. Hakan kuwa shi ne fadinSa Madaukaki cewa: “Lalle za a cika wa masu hakuri ladansu ba tare da wani hisabi ba[4]â€. b)– Kunya da Kame Kai
Kamar yadda a wannan bangaren ma za mu wasu siffofi wadanda sukan kasance daga cikin mafi daukakan ibadu, kamar kunya da kame kai na ciki, farji da kuma idanuwa. Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Babu wani ibada da ya fi daukaka a wajen Allah kamar kunya da kame kai na ciki da farji[5]â€. Daga wajensa (a.s) yana cewa: “Dukkan idanuwa za su yi kuka Ranar Kiyama in banda guda uku: idon da ya zauna a farke tsawon dare saboda Allah, idon da ya zubar da hawaye don tsoron Allah, da kuma idon da ya gintse daga abubuwan da Allah Ya haramta ganinsu[6]â€.
|