Hadiye Fushi da JuriyaHassada ba ta kumshi farin cikin da mutum ya kan ji ba dangane da wata falala da Ubangiji ya kan ba wa wasu daga cikin bayinSa. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Mumini ya kan yi farin ciki kuma ba ya yin hassada, shi kuwa munafuki ya kan yi hassada ne ba ya yin farin ciki[27]â€. d)– Himma da ‘Yan Garanci
Shari’a ta haramta tasirantuwa da ‘yan garanci cikin alaka ta zamantakewa. ‘Yan garanci dai kamar yadda Imam Ali bn Husain (a.s) ya fassara shi, shi ne: “mutum ya dauki ashararin mutum daga kabilarsa a matsayin mutumin kirki sama da na wata kabilar, ‘yan garanci ba shi ne mutum ya so kabilarsa ba face dai daga cikin ‘yan garanci shi ne mutum ya goyi bayin kabilarsa cikin zaluncin da suka yi[28]â€. Daga wannan hadisi da kuma ma’anar ‘yan garanci shi kansa, za a iya fahimtar cewa ‘yan garanci shi ne son kai, mika wuya da goyon bayan karya kan gaskiya[29]. Daya daga cikin bangarorinsa zai iya shiga cikin batun adalci da insafi da bayani kansa zai zo nan gaba. A daidai wannan lokaci kuma zai iya shiga cikin batun abubuwan da ke motsa rai da ake bukatuwa da hadiye su da samun iko a kansu. Akwai hadisai da dama da suka zo kan haramcinsa (‘yan garanci), kamar ingantaccen hadisin da Imam Sadik (a.s) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: “Wanda ya nuna ‘yan garanci, lalle ya kwance igiyar imani daga wuyansa[30]â€. e)– Girman Kai, Ji-Ji da Kai da Alfahari
Daga cikin wadannan shu’urai na zuciya da aka haramta har da girman kai da alfahari, da mu’amala da mutane da irin wannan hali. Cikin wani ingantaccen hadisi, an ruwaito daya daga cikin Bakirai biyu (a.s) cewa: “Duk wanda ke da komai kashin girman kai cikin zuciyarsa ba zai shiga Aljanna ba[31]â€. Kamar yadda aka ruwaito cewa abu na farkon da aka fara sabon Allah da shi shi ne girman kai, shi ne sabon Allah da Iblis ya yi lokacin da ya ki aikata abin da aka umarce shi, ya yi girman kai don ya kasance daga cikin kafirai[32].
|