Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S)



Saboda haka zamu samu mafi yawan bahasi da karatu da aka yi a kan wannan maudu’i ya karfafa ne a kan wannan al’amura biyu manya.

Sai dai taskace gudummuwar da Ahlul Baiti (A.S) suka bayar da wadannan al’amura biyu manya da muhimmancinsu yake mai girma ta nahiyar nazari da tunani na gaba daya game da sakon musulunci yana iya kawo shubuha mai girma ta nahiyar aiki na zahiri. Wato wannan rukuni na zahiri wadanda su ne Ahlul Baiti (A.S) da an a jiye su gefe guda gaba daya har zuwa yau da ya kai ga wata iyaka da wani geji mai girma a rayuwar musulunci, ta yadda aka nesantar da su daga fagen jagoranci da halifanci in banda ‘yan shekaru kalilan da imam Ali da dansa Hasan (A.S) suka yi, hakan nan ma aka nisanci daukar tunani daga garesu ta bangaren musulmi sai dai a wasu abubuwa ‘yan kadan kwarai.

abin da ya dada kawo matsala shi ne, wannan bincike da ya shafi wadananan al’amura guda biyu masu muhimmanci da girmamawar mafi yawanci ya takaita ne da bahasin tabbtatar da wilaya da mrja’anci ba tare da ya jibanci muhimmancin tafsirin wannan nazari ba ko bayanin rawa muhimmiya da zata iya yiwuwa wannan imamanci da marja’anci sun taka a rayuwar msusulunci, da kuma alakarsu da nazarin wannan sako na karshe da sauran sakonnin ubangiji da hadafinsu mai tsarki, tare da cewa su Ahlul Baiti (A.S) da kansu a hadisansu yayin da suka jibanci wannan al’amri sun karfafa wannan rawa da suka taka muhimmiya da abin da ya shafi wannan nazari karfafawa mai fadi.

Cigaban Bincike Game Da Ahlul Baiti (A.S)

Saboda haka ne muna da bukatar yin bincike game da Ahlul Baiti (A.S) saboda bayanin hakikanin matsayinsu a wannan mahanga da kuma a wajan musulmi gaba daya, da kuma bayar da muhimmanci kan wannan bincike da zai yi bayanin dukkan abin da ya shafi rawar da suka taka a rayuwar musulunci ta wata nahiya, da kuma karfafawa a kan janibin alakar wannan al’amura ta nahiyar nazarin musulunci ta wani bangare. A nan yana da kyau mu nuna wasu bangarori na wannan bincike;

Na farko: Tafsiri da kuma bayanin wannan hadafofin musulunci ta hanyar karfafar tunanin Ahlul Baiti (A.S) a sakon musulunci, ta yadda ta hakan zaka karfafa bayanin cikon sakon musulunci a matsayin shi ne na karshe da kuma tabbatar da wannan sako da hadafofinsa na aiki koda kuwa a takaice ne.

Na biyu: Bayanin bangaren alaka tsakanin wannana rukuni mafi muhimmanci na musulunci da sauran rukunoni, ta yadda cigaba yake bayyana a cikin wannan nazari na musulunci, da kuma dacewa wajan gini da hadafi da kuma sakamako.

Na uku: Bayanin alaka a tsakanin wadanan siffofi na musamman, da kuma abin da ya shafi akida da fikirar da ta kebanta da mazhAbun Ahlul Baiti (A.S) banda sauran mazhabobi na musulunci da kuma wannan fahimta ta nazarin musulunci da ta tsayu bisa tunanin imamancin Ahlul Baiti (A.S) da kuma rawar da suka taka a rayuwar msusulunci.

Misali, menene alaka tsakanin wadannan al’amura: isma, takiyya, ceto, tawili, bada, humusi da ribar kasuwanci, da auren mutu’a, da makamancisu na daga tunani a shari’ar musulunci wacce ta kebanta da mazhabar Ahlul Baiti (A.S) da kuma imamanci wanda yake rukuni na asasi a nazarin musulunci?.

Shin sabanin shi mujarradin sabani ne a ra’ayin akida ko fikihu, sannan ya juya zuwa ga sabani da sa-in-sa na siyasa da akida, ko kuwa wadannan al’amura da tunani suna da alaka mai karfi a asalin nazari sai suka juya suka koma dauki-ba-dadi a tsakanin al’ummar musulmi?.

Na hudu: Binciken alaka ta aiki da nazari a bisa asasin maslahohin musulunci da hadafofi madaukaka tsakanin matakai da aikace-aikace daban-daban da kuma aikin da su imaman Ahlul Baiti (A.S) suka gabatar da su a lokuta daban-daban ga al’ummar musulmi.



back 1 2 3 4 5 6 next