Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S)Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su tabbata ga shugaban annabawa Muhammad da alayensa tsarkaka. Magana Game Da Ahlul Baiti Da Muhimmancinta
Bayan haka hakika magana game da Ahlul Baiti (A.S) a musulunci yana daga mafi girman magana da take da sasanni daban-daban na akida da tunani da wayewa da tarihi da zamantakewar al’umma. Wannan kuwa saboda cewa cigaban sakon Annabi da bayaninsa yana ciki imamanci da shugabani da Allah ya wajabta binsu da sonsu. Kamar yadda su ne tsaran kur’ani mai girma da yake shi ne nauyi mafi girma, Ahlul Baiti (A.S) su ne daya nauyin wanda ba zai rabu da Kur’ani ba, kai su ne malaman al’umma da suke fassara shi da bayyana shi da kuma gano hikimominsa da fitar da taskokinsa. A lokaci guda su ne suke rike da sunnar Annabi (S.A.W) da bayaninta da samuwarta da ainihinta, suna sane da abin da take komawa zuwa gareshi a lokacinta da kuma nan gaba dinta. Kamar yadda su ne abin koyi kyakkyawa da jagorancin al’umma na gari wajan daidaito, da hakuri, da yalwar kirji, da kyawawan dabi’u, da tafarki na gari wajan kira zuwa ga Allah (S.W.T) da hikima, da wa’azi kyakkyawa, da jihadi a tafarkin Allah da rayuka da dukiya, da kuma shiryarwa domin sadaukarwa da dukkan abin da suka mallaka mai kima domin kare addini da gaskiya da adalci da kuma taimakon abin zalunta. “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya kuma tsarkake ku tsarkakewa[1]†Saboda haka Ahlul Baiti sun jure wa daukar nauyin wannan sako mai girma kuma a kan wannan tafarki zargin mai zargi ba ya cutar da su, sai suka bar tarihi mai girma na jagorancin al’ummar musulmi jagoranci mai tasiri, suka kuma tsayar da ayyuka masu girma a tsawon zaman rayuwarsa a dukkan fagage: na ruhi da siyasa da ilimi da akhlak, suna masu kare addinin musulunci da musulmi daga dukkan makiya na ciki da na waje da ga kuma: karkatattun shugabanni, da munafukai, da yan neman dama na siyasa, da zindikai mulhidai, da ma’abota bidi’a da bata, da miyagun malamai da yahudawa, da nasara, da mabarnata. Ahlul Baiti Su Ne Rukuni Mafi Muhimmanci
Wadannan al’amuran da wasu suke damre da wasu suna karfafa muhimmancin wannan bayani na musulunci, a lokaci guda suna bayyana abin da ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) da wasunsu na daga ruwayoyi, kuma Kur’ani ya yi nuni zuwa gareshi, wanda ya nuna su ne suke misalta daya daga rukunoni na asasi wacce aka gina musulunci a kanta, kai su ne rukuni mafi muhimmanci a ciki. Wannanan hususiyya da matsayi na musamman na Ahlul Baiti (A.S) hakika yana kusan zama wani abu ne da dukkan musulmi suka yi ittifaki a kansa, koda kuwa sun saba a mafi yawan abubuwa, shin a zurfi ne ko yalwa ko bayani. Hada da haka akwai nassosi na ayoyi da ruwayoyi ingantattu mutawatirai masu yawa da suka sanya girmamawa da mika wuya da so da biyayya da dukkan musulmi suke nuna wa ga Ahlul Baiti (A.S).
|