Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S)



Tare da cewa abin da da ya gudana na tarihi da rayuwar da Ahlul Baiti (A.S) suka yi ya kasance yana nuna kutsawarsu mai zurfi ta siyasa da badini mai kyau, da gina al’umma da kishiyantar wannan magana da furuci da ita. Domin abin da Ahlul Baiti (A.S) suka hadu da shi na kisa, da kora, da takunkumi na zahiri da na badini, a yanayi na jejjere tsawon zamani a hannun umayyawa da abbasawa da usmaniyawa da tilatsa musu domin neman ganin bayan koyarwarsu a cikin al’ummar musulunci.

Sai dai muna iya ganin wannan matsayi da Ahlul Baiti (A.S) suke dauke da shi na badini mai yalwa a cikin musulmi, wannan kuma ba domin komai ba ne sai domin wadannan matsayi da Ahlul Baiti su ke dauke da shi a cikin musulmi, na asalin nazari a musulunci, sannan da karfafa hakan a cikin ayoyin kur’ani mai girma da sunnar Annabi, da riskar musulmi ga wannan al’amari, da kokari da hidima mai girma da suka yi ga musulmi da musulunci, ta yadda duk da samuwar abubuwan da suka kishiyanci koyarwar tasu amma wannan ya tilasata samuwar wannan gani ga matsayin nasu a tarihin musulunci.

Kamar yadda wannan mahangar ta musulmi ga Ahlul Baiti (A.S) ta zama ita ce take fassara mana dayawa daga wannan adadi mai girma na darasosi da litttattafai da bincike na musamman game da su, wannan ya shafi wannan maudu’i na musulunci daga malaman musulmi duk da sabawar mazhabobinsu, ko kuma samun furuci da wannan gaskiya daga cikin abin da yake kunshe cikin littattafan ilimin musulunci a fikihu da tafsiri da hadisi da tarihi da makamantansu, ta yadda babi wani littafi da ya zama togiya daga hakan.

Ba zai yiwu a fassara wannan al’amari na tarihi ba da yanayi da ya dace ya kuma yi daidadi a hankalce sai dai a bisa akidar imamiyya isna ashariyya, ta yadda ya zama ana ganinsu a matsayin rukuni da musulunci ya tsayu a kansa a sakon karshe da Allah ya yi alkawarin karewa da kuma wanzarwa, Ahlul Baiti (A.S) kuma su ne wadanda suke misalta cigaba da wanzuwar wannan sako da abin da ya kunsa da nauyin da yake dauke da shi, duk da cigaban isar da sakon da suke yi ba yana nufin annabta ba ne, kamar yadda manzo (S.A.W) ya gaya wa Ali (A.S) cewa: “Kai gareni kamar matsayin Haruna ne ga Musa sai dai ba Annabi bayana”.

Ahlul Baiti (A.S) su ne cigaban wannan sako domin su ne kunnen dokin alku’ani kuma masu fassara gareshi domin su ne masu dauke da sunnar Annabi da dukkan abin da ta kunsa, kuma su ne masu kunshe da wannan mas’uliyya domin su ne imaman shiriya kuma al’alamin tsoron Allah masu kuma isar wa daga manzo (S.A.W) kuma su ne majibinta al’amari bayansa.

Kamar yadda aka kaddara wa wannan sako ya zama na karshe ya wanzu ya ci gaba, haka nan ba makawa Ahlul Baiti (A.S) sun wanzu bisa hakika kuma da tasiri cikin al’ummar musulmi, wannan shi ne hakikanin da babi wani mai bincike da zai iya musun sa komai nisan girman kansa da kin gaskiya da kin gaskiya da hakika.

Gudummuwar Da Ahlul Baiti (A.S) Suka Bayar

Sai dai duk da wannan akwai tambaya muhimmiya da zata rage wacce take: menene hakikanin rawar da suka taka a rayuwar musulunci, tare da samun wannan matsayin na musamman a mahangar musulunci da kuma hakikanin ruhin zamantakewar al’umma gun musulmi?

Amsar wannan saudayawa yakan kasance cikin abu biyu masu muhimmanci:

Na farko halifanci da maye gurbin bayan manzo (S.A.W)

Na biyu: komawa gare su a tunani da addini da dukkan al’amura masu alaka da fahimtar sako da kuma rassansa.



back 1 2 3 4 5 6 next