Neman TabarrukiAllah madaukkakin sarki ya sanya wani bangare na kasa ya zama wurin ibada sakamakon kasantuwar wasu bayin Allah masu kira zuwa ga tauhidi a wurin, kamar idan Allah yake ba da umarni da a tsayar da salla inda annabo Ibrahim ya kasance (Makamu Ibrahim). Inda Allah yake cewa: “Yayin da muka sanya Ka’aba wurin da mutane zasu rika taruwa kuma wuri na aminci, to ku riki wurin da Ibrahim ya tsaya wurin sallaâ€[5]. Yin salla a wannan wurin kasantuwar ba shi da bambanci da sauran wuraren da suke a msallacin, ya samo asali ne daga tsayuwar da Ibrahim ya yi a wajen sakamakon haka ya samu albarka ta musamman, don haka ne masu salla suke so su yi salla a wajen, domin neman tabarruki. Haka nan zamu gani yadda Allah ya sanya tsakanin dutsen safa da marwa wurin ibada, wannan kuwa duk saboda al’barkacin kafafuwan wata baiwar Allah ta taka wajen har sau bakwai, don haka ne Allah yake ba da umarni cewa mahajjata su je su dawo a wannan wuri har sau bakwai, duk wannan ana yinsa ne don neman tabarruki da Hajara (a.s) kuma babu wani dalili wanda ya wuce wannan. 2-Rigar Annabi Yusuf Ta Warkar Da Annabi Yakub (a.s) Annabi Yakub sakamakon rashin Yusuf ya yi kuka tsawon shekaru da shekaru, ta yadda har ya rasa ganinsa, yanzu Allah yana so ya mayar masa da idanunsa, Annabi Yakub (a.s) sakamakon aza rigar Yufus da aka yi a kan fuskarsa ya samu lafiya, kamar yadda Allah yake fada a cikin littafinsa mai tsarki; “Ku tafi da wannan rigar tawa ku jefa a kan fuskar babana ganinsa zai dawoâ€. [6] Rigar annabi Yusuf ba ta kasance tana da saka ba ce ta musamman wacce ta fita sauran mutane, an yi wannan riga ne da audugar Misra kuma a nan a ka saka ta, amma Allah madaukaki ya so ya isar da ni’imarsa zuwa ga bawansa ta hanyar wannan riga. Sakamakon dora wannan riga a kan fuskar Yakub ya koma yana gani tangaram kamar yadda Allah yake cewa: “Yayin da dan aike ya zo sai ya jefa rigar a kan fuskarsa sai ganinsa ya dawoâ€. [7] 3-Akwatin Alkawari Ya Kasance Dalilin Natsuwa Da Cin Nasara Annabi Musa (a.s) a karshen rayuwarsa ya kasance ya sanya allunan attaura wadanda aka saukar masa da kuma wasu abubuwa da ya gada masu muhimmanci a cikin wani akwati ya kuma mika shi zuwa ga wanda ya gaje shi wato Yusha’u Bn Nun, sakamakon haka ne Bani Isra’il sun kasance suna bai wa wannan akwati muhimmanci kwarai da gaske, don haka duk lokacin da zasu yi yaki tsakaninsu da wasu al’umma sukan tafi da wannan akwati tare da su, ta wannan hanyar ne suke cin nasara a kan makiyansu, zuwa lokacin da wannan akwati mai matsayi da abin da yake a cikinsa ya kasance a hannunsu sunkasance suna rayuwa madaukakiya, amma abin bakin ciki sakamakon raunin addinin da suka samu ta hanyar makiyansu wannan akwati mai dinbin daraja ya kau daga hannunsu. Bayan wani lokaci sai Allah madaukaki ya zabi Dalut a matsayin kwamandan yaki ga Bani Isra’il, sannan annabinsu ya bayyana musu cewa alamar wannan kwamandanci da aka bai wa Dalut cewa daga Allah ne, akwatin nan wanda yake kuna natsuwa da shi. Idan kuka halarci wannan yaki za a mai do muku da shi. Ga abin da Allah yake cewa: Sai annabinsu ya ce musu lallai alamar mulkinsa shi ne za a zo muku da akwati wanda akwai natsuwa a cikinsa daga ubangijinku, sannan akwai sauran abin da iyalan Annabi Musa da Harun suka bari, mala’iku suna dauke da shi, a cikin wannan aya ce gareku idan har kun kasance masu imaniâ€. [8] A nan Allah madaukaki ta hanyar annabinsa yana ruwaito batun neman tabarrukin da Bani Isra’il suke da wannan akwati, abu mafi muhimmanci shi ne ta yadda mala’iku suke daukar wannan akwati, idan addinin Allah yana ganin yin haka wani aiki wanda ya saba wa kadaita Allah sam ba zai yiwu annabin Allah ya kawo shi ba a matsayin wani labari mai farantawa. 4-Neman Albarka Da Wurin Da As'habul Kahfi Suka Kasance Muminai masu kadaita Allah bayan sun gano inda aka rufe As’habul kahfi, dukkansu sun hadu a kan cewa zasu gina masallaci ne a kan kabarinsu ta yadda ta hanyar ibada kusa da kaburburansu zasu nemi tabarruki. Ga abin da Kur’ani yake cewa a kan haka: “Sai wadanda suka ci nasara a kan saura suka ce, zamu gina masallaci a kan kabarinsuâ€[9]. Masu tafsir suna cewa: Abin da ake nufi da gina masallaci a cikin wannan aya shi ne yin salla awurin da neman albarkaci daga jikunansu. Dangane da neman tabarruki zamu wadatu da wannan ayoyin guda uku ne. Kula da ma’anar wadannan ayoyi zasu koyar dam u ne wani asali na ilimi daga Kur’ani ai girama, wannan kuwa shi ne nufin Allah madaukaki ya tafi a kan cewa zai kwararo da ni’imominsa na fili da na boye zuwa ga dan Adam ta hanyar wasu daga cikin bayinsa, a nan kuwa tsakanin abubuwan da suka shafi rayuwar duniya da wanda ba su ba babu bambanci, misali Allah madaukaki a kan abin da ya shafi shiryarwa yakan dauki wani abu wanda aka saba da shi ya yi amfani da shi, wato ta yadda yake zabar wani daga cikin bayinsa a matsayin Manzo ya aiko shi zuwa ga mutane domin ya shiryar da su. Amma wani lokaci nufinsa yakan yi rigaye a kan ya tafiyar da ni’imominsa ta wata hanya wacce ba a saba da ita ba don ya isarda wannan ni’ima zuwa ga bayinsa. Neman tabarruki kuwa bai wuce wannan ba ta yadda mutum zai nemi wani abu daga ni’imar Ubangiji ta hanyar da ba ita ake bi ba wajen neman wannan abin a cikin rayuwar duniya. Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP) Facebook: Haidar Center - December, 2012
|