Neman Tabarruki



Karamomi Biyu Da Suka Bayyana Ga Maryam (a.s)

Kur’ani yana ambatar karamomi guda biyu da suka bayyana daga maryam su ne kamar haka:

1-Ta kasance tana ganin abinci a wurin da ta kasance tana bautar Ubangiji, sakamakon haka ne duk lokacin Zakariya (a.s) ya shigo wajenta sai ya tarar da abinci a wajenta, sai ya tambaye ta daga ina take samun wannan abincin, sai ta ce masa: “Wannan yana zuwa ne daga Allah, Lallai Allah yana azirta wanda ya so ba tare da hisabi ba”. [3]

2-Maryam yayin da zata haihu ta kama wata itaciyar dabino sakamakon ciwon nakudar haihuwa, sai kwatsam ta ji wata murya tana cewa: Ki kama wannan reshen busasshe na dabino ki girgiza shi domin ‘ya’yan dabino su zubo miki”. [4]

A wadannan wurare guda biyu da muka ambata na karamomin sayyida maryam (a.s) na kawo mata abinci da ake yi da kuma yadda busasshyar itaciyar dabino ta yi ‘ya’ya, duk suna nuna mana tsarkin ruhin Maryam ne, ta yadda wadannan abubuwa suka faru sabanin yadda suka saba faruwa saboda girmanta. Zuwa yanzu mun fahimci ma’anar mu’ujiza, a nan ya dace mu yi bayani a kan neman tabarruki.

Menene Neman Tabarruki

Tabarruki ya samo asali ne daga kalmar ‘baraka’ wacce take bayar da ma’anar Karin ni’ma, a nan kuwa abin da ake nufi da haka shi ne mutum mai imani kuma mai kadaita Allah yanemi wani abu ta hanyar wani abu wanda ya zo daga annabawa ko manyan bayin Allah. Wannan kuwa ba yana nufin cewa ba mutum ya kulle kofar faruwar abubuwa kamar yadda suka saba faruwa, a lokaci guda mutum yana bin hanyar da aka saba da ita kuma ya nemi kari ta hanyar neman tabarruki daga bayin Allah ta yadda kofofin ni’ima zasu bude a gare shi.

Babu shakka babu wata alaka ta duniya tsakanin abubuwan da suka ragu daga bayin Allah da abin da mutum yake samu na daga ni’immomi ta hayar wadannan abubuwan. Amma kamar yadda muka yi bayani cewa wani lokaci lokaci ni’imar Ubangiji takan kwararo wa dan Adam ta wata hanyar da ta saba wa wacce aka saba. Haka nufin Allah ya rigaya a kan cewa ta hanyar neman tabarruki da manyan bayin Allah da abubuwan da suka ba ri mutum yana iya samun abin da yake nema, wannan kuwa wta hakika ce wacce ayoyin Kur’ani suke tabbatar da ita. Sannan ruwayoyi mutawatirai sun zo a kan hakan, sana babu wani dalilin hankali wanda yake kin yiwuwar tasirin abubuwan da ake jingina su zuwa ga bayin Allah.

A nan zamu kawo wasu daga cikin ayoyin da suke bayani a kan haka:

1-Neman Tabarruki Da Matsayin Annabi Ibrahim (a.s)



back 1 2 3 4 next