Neman TabarrukiKur’ani a cikin surar bakara aya ta 22 yana bayyanar da wannan tasiri wanda yake karkashin ikon Allah (s.w.t) (Ta bakin masu falsafa tasiri zilli) inda yake cewa: “Shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide, sannan ya sanya muku sama a gine, kuma ya saukar muku ruwa daga sama, sannan ya fitar da tsirrai daga gare shi wadanda suke arziki ne gare kuâ€.[2] Wannan aya tana bayyanar da yadda tasirin da ruwa yake da shi wajen fitowar tsirrai da yadda itatuwa suke yin ‘ya’ya sakamakon saukar ruwan sama. Sannan kuma aikin ilimin kimiyya baki daya shi ne gano yadda tasirin da yake akwai tsakanin halittu ne, ta yadda ta wannan hanyar za a san yadda alakar da take tsakanin abubuwan halitta domin yin amfani da su kamar yadda ya dace. Kuskuren wannan duniyar da muke ciki shi ne, ta yadda take bayyanar da fuskarta ta zahiri wanda sakamakon haka ne saia dauka cewa ai abubuwan da suke da tasiri ga sauran halittu kamar ma su ne sanadi na asali babu wani abu bayan hakan, alhali kuwa bayan wannan duniya akwai wanda shi ne mai tasiri na hakika kuma shi ne ma yake tafiyar da komai da komai, sannan tasirin sauran halittu abin da ya kama daga kasa har zuwa sauran taurari suna tafiya karkashin iko da nufinsa kuma kamar yadda ya tsara ne suke tafiya. Allah Shi Yake Bayar Da Iko Ya Kuma Amshe Idan Ya So Kamar yadda ya kasance Allah shi yake bai wa wasu daga cikin halittu ta yadda zasu iya yin tasiri a sauran halittu, haka nan idan ya ga dama yakan amshe wannan ikon ta yadda ba zasu iya yin tasirin ba a cikin wasu. Misali Allah yana bai wa wuta umarni da cewa kada ta kona Ibarahim (a.s) kamar yadda shi ne ya sanya wuta tana iya kone wani abu, haka nan kuma shi ne ya amshe wannan tasiri da take da shi kuna. Haka nan yake bai wa teku umarni da kada ta nutsar da annabi Musa da mutanensa, saboda da haka kamar yadda Allah yake bai wa wasu daga cikin bayi ikon yin wani abu haka nan idan ya so sai ya amshe wannan karfi da ikon da suke da shi. Wata Fuskar Daban Da Allah Yake Bayyanar Da Ikonsa Iko da kudirar Ubangiji ta ginu a kan cewa kowane abu zai faru ta hanyar wani na musamman, amma sakamakon wasu dalilai sai Allah madaukaki ya sanya wasu abubuwa su auku ba bisa yadda suka saba faruwa a al’ada ba. Wannan kuwa yakan faru ne yayin da annabawa suke so su tabbatarwa mutane cewa suna da alaka da Allah (s.w.t) Irin wannan aiki shi ne ake kira da “Mu’ujizaâ€. Mu’ujizar annabawa baki daya tana faruwa ne ta wannan hanyar, babu shakka kasantuwar sanda busasshiya ta koma macijiya, ko kuma janyewar ruwan kogi ta hanyar sandar Musa (a.s) ko kuma sanya makaho wanda ba ya gani ya koma yana gani, da warkar da sauran cututtuka masu wuyar magani, dukkan wadannan abubuwan suna faruwa ta hanyar da ba su saba faruwa ba (amma ana ba muna Bahasi ne a kan hakikanin mu’ujiza ba ne). Da wannan ne zamu fahimci cewa, mafi yawa, baiwar Ubangiji tana isowa zuwa garemu ne ta hanyar da aka saba da ita, amma wani lokaci takan iso wajenmu ne ta wata hanyar daban wacce ba a saba da ita ba, wannan kuwa ita ake kira da mu’ujiza, wannan kuwa tana faruwa ne yayin da mutumin da ya zo da ita yana ikirarin annabta ne kuma ya zo da ita ne domin ya tabbatar da alakarsa da Ubangiji. Amma duk lokacin da irin wannan ya faru, amma wanda ya zo da shi bai yi da’awar annabta ba, ana ce ma shi da karama.
|