Neman Ceto 2



Suna cewa: Dole ne muce ya Allah ka sanya mu cikin wadanda zasu samu ceton Muhammad (s.a.w).

Saboda haka sam ba mu da hakkin da zamu ce: Ya Muhammad ka cece mua wajen Allah. Tabbas Allah ya bai wa Manzo damar yin ceto, amma ba mu da ikon da zamu ce ya Allah ka cece mu, don haka dole ne mu nemi ceto a wajen Allah wanda ya ba shi damar ceto.

Amsa: Ayoyin Kur’ani sun yi bayani a kan cewa masu bayar da sheda da gaskiya zasu yi ceto a ranar kiyama, wato zasu kasance masu ceto a ranar kiyama (amma tare da izinin Allah) a inda yake cewa;

“Wadanda suke kiran wanin Allah sam ba zasu samu ceto ba, sai kawai wadanda suka bayar da sheda da gaskiya suna sane”[7]

Kalmar “Illa” da ta zo a cikin wannan aya tana kebance kawai wadanda suka mallaki yin ceto.

Abin da kuwa ake nufi da mallakar ceto kuwa shi ne wadanda suke da izinin yin hakan daga Allah madaukaki. Tambaya a nan shi ne tun da Allah madaukaki zai bayar da wannan izini ga wasu daga cikin bayinsa, menene matsala don mai laifi ko zunubi ya nemi wannan ceton daga wadanda aka ba dama.

Duk da yake neman ceto ba yana wajabta karba ba ne, amma wannan wanda yake da izinin yin ceto karkashin wasu sharudda zai cece wanda ya nemi ceton. ABin lura a nan shi ne maganar da shugaban wahabiyawa yake yi inda yake cewa: Allah ya bai wa waliyyansa damar ceto, amma ya hana mu da mu nemi ceton daga gare su. [8]

Na farko; cikin wace aya ce Allah ya hane mu da mu nemi ceto daga masu ceto na gaskiya? Idan wannan hani saboda cewa neman ceto shirka ne, kamar yadda muka yi Bahasi a baya dangane da shirka, zamu iya fahimtar cewa sam wannan ba shirka ba ne, domin kuwa wanda yake neman ceto ba ya ganin wanda zai cece shi amatsayin Allah ko wani mai tafiyar da ayyukan Allah, kawai mutum yana ganinsa ne a matsayin wani bawan Allah mai matsayi a wajen Allah, domin kuwa yana ganin cewa duk wani abu yana gangarowa ne daga Allah, ballantana wannan ya zama shirka, domin kuwa ba bauta ba ne ga mai ceton.

Na biyu: Wannan magana ta shugaban wahabiyawa tana warware kanta, domin kuwa idan har Allah ya bai wa waliyyansa wannan hakki da dama na ceto me zai sanya kuwa ya hana su amfani da wannan damar da ya ba su, wato ya hana al’umma su nemi wannan ceton daga gare su.

2-Shirkar mushrikai da neman ceto daga gumaka



back 1 2 3 4 5 next